← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 227

Sashe 133

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyowa Aryan ya yi, suna fuskantar juna, cikin fushi, zuciya game da zugan shaiɗan ya ce. "Abba ba zan aureta ba!! Dik gidan nan ma babu wanda zai yi aure! Na kafa wannan doka! Ko kaki ko ka so Abba, ba shawaranka nike nema ba, wannan umarni na ne!! Babu wanda zai shigo da mace cikin gidan nan, ka faɗa mun auren me ya tsinanawa zuri'armu in banda wahala? Ka ce ka hana soyayya saboda an cutar da kai ta dalilinta, ka aurawa su babban yaya abin da basa so, me ya haifar? Wancan banzar (Mom Rimsha) ta zo ya shiga jikin yayana, ta kashe mana shi, mahaifiyar Vash, yaya yana zaune a gidan nan, ta ce sai sun je yawon ƙasashe shaƙatawa, a nan ya je suka yi haɗarin jirgi suka mutu, ka faɗa mun me mata suke tsinana mana a rayuwarmu idan ba balain da suke jefamu a ciki ba? Dole ne sai mun rayu da mace? Ka faɗa mun dole ne? Kai da kake tare da Ammie.......". Bai iya karisa maganar ba Faryan ya yi tsalle ya rufe mashi baki, dan ya lura yayan nasa ya fita hayyacinsa, ɓacin rai da shaiɗan sunsa ya manta da waye ma yake magana, an kure zuciyansa ne.

Babban abin da yai mashi zafi yadda aka dinga gayawa Abban nasu magana dan kawai ya je neman auren da su sun ce basa so, a yau Abba ya sa Aryan ya ƙara tsanan mata, har ita Seraphina ya ji ta fita mashi a rai, ya ji ya tsaneta.

Cikin fushi ya kwace kansa daga Faryan, yana huci ya nufi waje, yana wani irin taku na jarumta, jikinsa har wani girgiza yake yi saboda ɓacin rai.

Yana fita ba'a fi 2 mins ba Abba ya yanke jiki ya faÉ—i tsabar balain zuciya, take numfashinsa ta É—auke. Ammie kam ta rasa bakin magana, abin ya fi karfinta.

Sai da ta ga Abba ya faɗi ne ta kurma ihu wanda ya jawo hankalin su Faryan a kansa. Da gudu suka yi kansa suna ambatan sunansa, sai dai ina, baya motsawa, cikin zafin jini suka ɗaukesa izuwa cikin mota, ba tare da ɓata lokaci ba suka yi CRYSTAL PALACE HOSPITAL da shi.

Ammi kuwa zarya ta fara yi a parlon tana addu'ar ALLAH ya yayyafawa wannan musifa ruwa, tasan halin zuciyan Abba sarai, addu'a take mashi ALLAH yasa kada zuciyar ta buga, dan hakan tsab zai iya faruwa a irin fushinsa!

Suna shiga CP-HOSPITAL suka nemo nurses suka zo da bed domin a ɗaukesa. Da yake asibitin gabaɗaya kewaye yake da Camera, suna fito da Abba suka ɗaura shi a saman bed ɗin gabaɗaya camerorin dake wajen suka fara ɗaukansa. Lokaci guda jiniyar agajin gaggawa na asibitin ta fara ƙara wanda hakan ya janyo hankalin dik wani likita a kan su duba laptop ɗinsu su ga menene.

Suna duba cameras É—in suka ga Abba a kwance a kan gado. Wani nurse ne ya ce da Harleen wanene wannan? Ya faÉ—a yana nuna Abba. Harleen ya amsa da. "Muhammad Khaiza'an by name, ya yanke jiki ne ya faÉ—i.........". Bai iya karisar da maganar ba sakamakon amsakuwar da ya ji a asibitin ya amsa da kiran sunan Muhammad Khaiza'an.

Ya ALLAH ai tin daga kan Chief medical directors, medical officers, specialist doctors, obstetricians da bama aikinsu bane sai da suka nufi wajen, su specialized doctors, senior nurse, nurse, laboratory technician, receptionist, cleaners ma baa barsu a baya ba, technicians, health assistants, kai harta manyan securitys dake wajen sai da suka yi gudun tseran cetan ran bin gadan! Tin daga kan hawa na goma consultants suke gangarowa da gudun gaske tamkar ba manyan mutane ba, ai wasunsu ma gani suke elevator bata gudu, dan haka suka biyo escalator wanda ita ma tattaka stair ɗinta bibbiyu uku-uku suke yi suna tsallake wasu, suna gudu suna cin karo da wasu ma na gudun nufar wajen, lamarin da yai mugun gigita dik wanda yake a cikin C-P-H a yau, basu taɓa gani irin wannan tashin hankali ba, sai da suka ga consultants dake hawa na goma dik sun diro ƙasa ne ma suka ƙara gigicewa, yau ba ji da kai, ba tsare ma jama'a hanya idan zasu shiga elevator, da kafafunsu yau dai suka sauƙo. Tambayar da kowa yake yi wa kansa shi ne wanene wannan dattijon da ake gudun cetan rai a kansa? Waye shi da har su Chief medical directors dik suka yo ƙasa a dalilinsa?...... Cikin ƙasa da mintuna goma harabar C-P-H ya cika tam da maikatar lafiya, ai jama'a basu tashi sanin C-P-H tana da balain tarin ma'aikata har haka ba sai yau, watau suna nan kenan?.

Sosai Harleen yai mamakin ganin yadda daga kiran sunan Abbansu C-P-H ta rikice har haka, duba yadda ma'aikata suka rikice daga jin cewa Muhammad Khaizaan ya É—auke wuta, to ko su da suke Æ´aÆ´ansa ai basu yi wannan birkicewa ba. "To waye Abbanmu?" Harleen ya jefi kansa da tambayar da babu mai amsa mashi. Intently ya maido da kallonsa a kan Faryan da gabaÉ—aya kansa ya kulle shi ma, tambayar kansa shi É—in ma yake yi waye Abbanmu? TASHIN SENSE shekarunsu almost 31 a duniya amma wai suke tambayar kansu wanenen ma mahaifinsu tukun nan!.

Slowly Faryan ya kallesa, kamar baya son motsa bakinsa ya ce. "Harleen, I am completely confused, don't you think Abba is the owner of this C-P-H? Coz bana jin ko mamallakin wajen ma zasu yi wannan rikicewa a kansa"...... "Faryan, I think more than that, kasan CRYSTAL PALACE HOSPITAL mamallakin CRYSTAL PALACE ne ai, ba yadda za'ayi Abba ya mallaki C-H-P kawai, dole sai in C-P mallakinsa ne".

"If that should be the case we have to think more than that". Cewar Faryan ........ Jinjina kai Harleen ya yi.

Silent for almost 2 mins ne ya biyo baya kafin Harleen ya ce. "Faryan your words have the scent of truth! Ban taɓa ganin Abba ya biya kuɗin hayan gidanmu ba, in short Abba bashi da C-P note-B, ban taɓa gani ba, dole akwai abin da ya saɓa, Abba has hidden many things from us, and If that's the case, we should start investigating now".

Suna nan suna zancen tuhume-tuhumensu an shigar da Muhammad Khaiza'an special É—akin, bama su san wani É—aki aka shiga da shi ba, saboda suna can suna tinani. Sai da suka farga babu kowa a wajen ne suka fara neman ina aka kai Abban kuma?.

Ni ma na ce ina aka kaisa? Zaku sani ne, ba kuna nan kuna surutan banzanku ba, ga shi an yi gaba da shi.

Likes comments and share fisabilillah.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only.

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

For more information 08161390581 Whatsapp me only.

STEP 1🔥

2025-12-10.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________ 46

Afkawa cikin hospital ɗin suka yi suka fara nemansa, Harleen ya ɗaga waya zai kira Aryan Faryan ya dakatar da shi, cike da tashin hankali ya ce. "Yah Aryan ba zai ɗauki kiran kowa ba, a yadda ya bar gida a fusace ba zai waiwayemu yanzu ba, ka kyalesa kawai, kuma Abba yana jin haushinsa, idan ya zo faɗa zasu sake yi, kasan halinsu ai, dik sai zuciyar balai, gara ka kyalesa, dan Abba zai ce sai Yah Aryan ya bashi hakuri, shi kuma kasan abin da ba za taɓa yi ba kenan".

Tarar numfashinsa Harleen yai da cewa. "Ban san me ainahin matsalar Abba da Yah Aryan ba, Abba fushi Yah Aryan zuciyar balai da kafiya, Abba ya ce sai Yah Aryan ya ce mashi sorry, shi kuma ya ce da ya ce sorry gwara a kashesa, kai wannan balai dayawa take, ni nama rasa me zan ce da Abba, ka dubi faÉ—ar da suka yi kwanaki, sai da Yah Aryan ya fi 1 year bai tako gida ba, dan kawai Abba ya ce sai ya bashi hakuri, sai da Ammie ta dinga rokon Abba, kai ni wlh wani lokaci suna jefani cikin tashin hankali da kaÉ—awar zuciya".

Faryan ya ce. "Babu ranar sassautuwar al'amurra, dan ni banga ranar ba, ka yi duba da yadda Yah Aryan yake mana, ai exactly yadda Abba yake ne a lokacin da yake matashi kamar yadda Ammie ta faÉ—a mana, kaga kuwa gyaruwan wannan al'amari sai wani ikon ALLAH".

Harleen ya ce. "ÆŠan nagada kuma ya fi É—an na koya ba, ai Yah Aryan ma ya fi Abba zafin zuciya, ALLAH dai ya shirya mana shi, amma ni ina ganin idan ya yi aure zai canza"...... ÆŠan zaro ido Faryan ya yi, sai kuma ya É—an saki one side smiling kafin ya ce. "Kuma kana da gaskiya, Abba da yai aure ai ya canza, auren ya É—an sassautasa, da a baya kafin ya yi aure ne ai Yah Aryan bai isa ya dinga mashi wasu abubuwan ba, amma yanzu Alhamllh Ammie ta sassauta mana zuciyar Abba".

Mood na Harleen ne ya ɗan canza, da kyar ya iya cewa. "Ammie ta canza Abba ko kuma Ummie?"........ Shiru Faryan yai bai sake yin magana ba, da alama an taɓo chapter ɗin da baya so ko kuma chapter da tafi karfinsa. Cigaba da zarya suka yi a kofar da suke tinanin nan aka sanya Abba duba da cikan gomannin nurses da manyan likitoci a wajen, sai kai komo ake yi.

Dik wani likita dake asibitin a yau yana wannan É—akin, sun bar duba kowa, sun tashi daga kan kowa, dik sun gudo izuwa wajen Abba........ Harleen yana tsaye a wajen sai ga wani babban Dr ya fito, cikin girmamawa ya ce. "Who's Faryan and Harleen?".
Chapter 133 · 0% Book details