← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 227

Sashe 81

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye wajen wani gaton shago na atamfofi Aryan ya shiga. Shi kuma guru ya wuce gaba. Manyan armed robbers biyu ne a cikin shagon, ɗaya na rike da bindiga yana wani zazzare idanunsa, ɗayan kuma na ta faman kwasan kaya, ga masu dukiya bayin ALLAH suka kwance luff a ƙasa, suna ji suna gani za'a kwashe masu halak ɗinsu, guminsu saboda tsoron wannan shegiyar kurmar abar da bata da sabo kuma bata jin yaren kowa face na kisa watau bindiga.

"Siiiiiiiiiitttttt". Aryab yai wa guy dake rike da bindigar. Da sauri ya juyo da jikinsa da bindigar, babu tausayi ya nufi harbin Aryan, bai san Champion namu na amana Champion É—in ne da gaske ba. Wata lace dage rataye a sama saitin kansu Aryan ya jawo tare da rufewa guy É—in idanu, sannan ya kama hannunsa ya huya bindigar, a lokacin ya É—ana kunamarta zai yi harbi, Aryan ya tayashi danna harbi kai tsaye ya fasa kan mutuminsu dake É—ebar kaya yana zubawa a bugu.

Sake hannunsa ɗaya daga jikin bindigar mutum ya yi yana ƙoƙarin buɗe lace na fuskansa, Aryan bai bashi wani dama ba ya kai mashi wata bahaguwar naushi a ciki, kafin ya gane me aka yi mashi ma Aryan ya kwaci bindigar tare da saitasa, take ya tarwatsa mashi ƙwaƙwalwa, a tsarin IRON FIST basa kama masu laifi, kawai idan suka isa waje kashesu dik suke yi, basa sa tsammanin ɓata gari zasu shiryu, kai bama sa basu dama, abin da suka sani kawai dik wanda ya kashe a kashesa kamar yadda addinin Musulunci ya koyar dasu, dan haka basu da lokacin ɓatawa wajen baiwa makasa damar ko zasu gyaru.

Ko da sauran Æ´an fashin suka ji karar harbin da Aryan yai basu wani damu ba, saboda suna harba bindiga sama ai dan firgita jama'ar kasuwar, so sun zaci sama mutanensu suka harba, sai suka cigaba da jidan kaya suna zubawa a buhu tamkar halaliyarsu.

Waje Aryan ya fito rike da bindigar, kowa ya gansa sai ya zaci armed robbers É—in ne, dan ya nannaÉ—e fuska da rawani, cikinsu kai tsaye ya shiga, kafin ma ya isa guru ya kashe mutum 4, kafin su farga an kashe masu bindigun 10 dikka saura masu kwasan kaya su zuba a buhu.

Nan suka farga da cewa su Aryan fa ba mutanen ba ne su bane, nan suka fara ƙoƙarin kokawa da su. Ganin haka yasa su Aryan suka jingine bindigun hannunsu, marasa bindigun ma sun kai su 10, dik sun fito tsakar kasuwan suka yi wa su Aryan zobe. Tini su Aryan suka ajiye bindigu suka hau gwada masu jami'an SSO suke, kuma IRON FIST renon AZURE suke. Dik wanda suka yi wa duka ɗaya sai ya baje a ƙasa, baya sake tashi, dama dik kayan maye ya cinye dik wani quality nasu.

A daidai wannan lokaci jiniyar motar ƴan'sanda ya fara karaɗe ko'ina a arear alamar suna zuwa. Cikin zafin nama su Aryan suka ɗauki bindigunsu, dik suka harbe armed robbers dake baje a ƙasar, basu bar ko mutum ɗaya da rai ba, sannan suka yasar da bindigun suka gudu ta tsakanin shaguna, suka haye katangar kasuwar suka dira ta baya. Ba zasu yarda a gansu ba ai, kada ku manta jami'an SSO suke, suka kuskura suka haɗu da ƴan'sandar nan to za'a samu matsala, dan ƴan'sansa zasu ce su buɗe fuskokinsu, su kuma ba zasu yarda ba, idan aka matsa zasu haɗa da ƴan'sandan dik su kashe ne, so gara su gudu kawai.

Basu zame ko'ina ba sai hotel ɗinsu, suna shiga suka hau haɗa kayansu, barin AVARIS a yau ya kamasu, idan ba haka ba sai an san SSO suna ƙasar AVARIS, dan dik waɗan dake kasuwar sun ga kalar fatarsu ai, zasu faɗa, kuma ma dole za'a nemesu tin da sun kashe almost 20 armed robbers, kunga kuwa nemansu wajibi ne.

Sun yi sa'a time da suka koma hotel ɗin Lion ya farka, yana zaune tsakiyar bed rike da waya yana ƙoƙarin kiransu kenan sai gasu nan. Ba tare da ɓata lokaci ba suka sanar mashi ga abin da suka aikata, harara ya dallawa Champion ba tare da ya yi magana ba. Guru ne ya ce. "Bro no time".

Shi ma hararar ya samu babu alamar Lion ɗin zai yi magana, har suka gama shiryawa bai kulasu ba, sai da guru ya haye saman bed ɗin ya jawo hannunsa yana faɗin su je, sannan ne ya ce. "I can't go anywhere"....... Aryan dake ƙoƙarin jan luggage box ɗinsu ne ya dallawa Lion harara kafin ya ce. "Do you heard what you said kuwa?".

Shiru babu alamar zai sake tanka masu, sai ma gyarawa da ya yi ya kwanta abinsa. Cikin fushi Aryan ya yi tsalle ya dira a tsakiyar gadon, dan in sun biyewa Lion wlh tsab zai ja masu aiki, dan wani lokaci Lion iskancinsa yawa ne da ita, sai ka kai zuciya nesa zama da shi.

Hannun rigar jikinsa Aryan ya naɗe tare da sunkuyawa ya cicciɓi Lion sama sai saman shoulder ɗinsa yana faɗin. "Ba zan iya juran iskancinka na wannan lokacin ba"...... Guru da iskanci shi kuma ya yi saurin damke hannayen Lion dukka biyu ya dawo da su ta bayan wuyan Aryan ya rike gam wai dan ma kada ya ce zai kwaci kansa, da hannu ɗaya Aryan ya rike Lion, ɗayan hannunsa kuma ya ja luggage box ɗinsu suka fito parlo.

A tsakiyar parlo Aryan ya sauke Lion tare da cewa. "Lets go"...... Wani irin kallo ya dallah masu da waɗan nan shaggun sharp eyes ɗin nasa masu rikitarwa kafin ya juya zai koma ciki, watau idan kana neman ɗan duniya ka samu Lion ka gama, tin da sun nuna a ƙage suke su bar hotel ɗin shi ne sai ya kuntata masu, ga shi ba zasu iya matsawa ko nan da can su barshi ba, iskanci kala-kala cike da cikinsa guy ɗin nan.

Ai cikin zafa Champion ya damko wannan tuntun jekar kitson nasa yana faÉ—in. "Baka isa ba"...... Da sauri guru ya tare gabansa yana faÉ—in. "Bro please".

Wani irin kallo Lion ya dallah mashi kafin can ƙasan maƙoshinsa ya ce. "Give me a way to pass"...... Jan tuntun gashin nasa da karfi Aryan ya yi har sai da Lion yai baya, dawowa ta gabansa Aryan ɗin ya yi, ya zamana su ukun suna fuskantar juna. Aryan ne ya ce. "

Likes comments and share fisabilillah.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

STEP 1🔥

2025-11-25🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________24 & 25

Wani irin kallo Lion ya dallah mashi kafin can ƙasan maƙoshinsa ya ce. "Give me a way to pass"...... Jan tuntun gashin nasa da karfi Aryan ya yi har sai da Lion yai baya, dawowa ta gabansa Aryan ɗin ya yi, ya zamana su ukun suna fuskantar juna. Aryan ne ya ce. "Lion please don't play with us here, kaga kai ka iya ɗaukar kasada na wuce misali, to wannan zai yi affecting namu sosai ne, zai ɓata mana mission ɗinmu".

Hararansa Lion yai kafin ya ce. "I think zaka cigaba da nuna ka isa dani ne". Yana É—aure fuska ya faÉ—a. Aryan zai amsa guru yai saurin rigasa da cewa. "Ina babu wannan magana, yanzu dai let's go". Ya yi saurin faÉ—ar hakan ne saboda yasan Aryan in ya buÉ—e baki zai lalata komai ne.
Kun san me ne? Lion ya tsani a nuna mashi iko, shi ma Aryan baya yarda a nuna mashi kamar bai isa ba. Yanzu da Aryan ya ce Lion ya tashi su tafi sai Lion ɗin ya ga kamar Aryan ya nuna mashi iko shi ne yaki tashi, shi kuma Aryan ya lallaɓashi yana ganin kamar ai ya bashi girma ne, idan suna gida yadda kuka san maguna haka suke da faɗa, amma idan suka je office girmama juna suke yi, dan rank ɗinsu daban-daban.

Da kyar suka shawo kansa, sannan ya yarda suka bar hotel É—in. Amma basu bar Avaris a lokacin ba, sai can yamma jirgin da suka yi booking ya tashi, sun dai bar hotel É—in ne suka yi nisa suka kama wani. By 4 na yamma jirginsu ya É—aga zuwa US. To safe journey our IRON FIST KUMA SSO.

--------------------------🔥

DEATH OR LIFE TEAM.🔥

A bakin wani katafaren dajin dake kudu maso yamma na AVARIS jirginsu ya tsaya, dikkansu using parachute suka yi wajen sauƙa, dan jirgin bata sauƙa ba, mazan ne suka fara sauƙa domin daji ne. A natse one by one suka diro ƙasa. Dikkansu idan ka kallin fuskokinsu aikin ne kawai a ransu, babu wasa a tattare da su, musamman Leo, Noor, Zaynish, Arya, Unays, Juraiz and V, waɗan nan su daban ne, burinsu su kafa tarihin da ba'a taɓa kafa irinsa ba a AZURE, a tarihin manyan da suka gabata a AZURE kafin su zo, sun karanta akwai wasu team masu suna F-L-F da su ne suka kafa tarihin da ba'a taɓa kafa irinta ba, amma sun bar AZURE yanzu, kai AZURE da kanta ta basu sunan F-L-F, su biyar ne a team ɗin, labarinsu sai da ya karaɗe duniya, tin daga kansu kuma ba'a sake wasu jami'an da suka yi rabinsu ba, to kudirin su Leo su bugesu, ya zamana sunan team ɗinsu DEATH OR LIFE ya zamana shi ne a sama da kowani suna.

Bayan sun kammala dirowa dikkansu, jirginsu ya tashi sama ya barsu a wannan ƙungurmin dajin. Gyara rucksack na bayansu suka yi, Leo ne ya fara wucewa gaba, ko tsoro babu ya kutsa cikin dajin nan. Bayan su 12 nan kada ku manta an haɗasu da ƙananan sojoji dake bar 1, an ƙara masu 12 soldiers.

Zaynish ne ya rufawa Leo baya cikin takun jarumta, while sauran sojijin zuƙatansu ya matuƙar kaɗawa da wannan ƙungurmin daji, amma ganin Leo ya yi gaba yasa suka ɗan samu kwarin gwiwa. Arya ce ta rufawa Zaynish baya tana riko igiyar rucksack ɗinta da kyau, ga wannan sheggun tauraran takalmar nasu da ko maciji suka taka ya taku kenan.
Chapter 81 · 0% Book details