Sashe 103
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan kowa ya gama bayanan dake a bayyane kowa yasan da su, masu karya sun shararo nasu, sai His Excellency ya buƙaci jami'an sirri na musamman da su bada nasu bayanan, watau irinsu SSO CIA da sauransu, misali kamar a Nigeria ace NSA da DG DSS, kun gane ai?.
A wannan karon sai da kowa ya gama gabatar da nasa, sannan SSO sune na karshe, guru zai sake miƙewa ya wakilcesu Lion ya ɗan dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu, sannan ya miƙe tsaye shi da kansa.
Ƙara ɗaure fuskar nan tamau ya yi, babu alamar annuri a tattare da shi, gyara mic ɗin gabansa ya yi kafin ya kunnata, a natse ya fara magana kamar haka. "Bisa ga bincike na sirri ya nuna cewa akwai manya daga cikin manyan jami'anmu dake taimakawa ƴan ta'adda, akwai masu basu makamai kuma akwai masu gwada masu hanyar guduwa". Ya ɗan ɗakata ba tare da ya ɗago ya kalli kowa ba, dik a cikinsu babu wanda ya kawo batun cewa akwai masu baiwa ƴan ta'adda makamai da sauransu sai SSO, shiyasa ya miƙe da kansa dan su gansa da kyau, kowa yana jin labarin halinsa dama, sun san ko a cikin SSO ɗin ma su basa ɗaukar raini ko wargi.
"Akwai manya dake ɗaukar nauyin ta'addanci ba iya kasar nan kawai ba, harda ketare! Sannan akwai sabbin hare-hare da aka shirya dan ƙaratowar zaɓe saboda maguɗin da kuka shirya, an kuma bada damar shigo da muggan miyagun kwayoyi masu haɗari dan ƴan ta'addan su bugu a ranar zaɓe su yi aiki cikin fitar hayyaci yadda zasu yi kan mai uwa da wabi ga kowa ba tare da tausayi ko tunani ba"........ Kai tsaye ba tare da shakkar kowa ba ya ce. "Harin ma ya shafi harda His Excellency saboda sanin cewa kujerar mulki ba zata kwace daga hannunsa ba saboda adalcinsa! A bisa binciken sirri ya nuna an hayo sabbin ƴan ta'adda bakin haure daga kasashe da dama, kuma dik wannan abin yana faruwa ne a tsakanin manyan jami'ai zuwa ministoci".
Babban GAT na sojojin kasar. (Bafa GAT namu na AVARIS ba, kada ku manta to) GAT É—insu ne ya ce. "Shaida zaka bada a bayyane ba wai ka tsaya ce mana binciken sirri ba!"....... Yana rufe baki conol lieutenant na Navy É—insu ya ce. "Shaida muke son gani, ka bamu shaida.........". Dukkansu cike da shakkarsa suka yi magana, saboda IRON FIST akwai balain kwarjini da cika ido, ga sawa mutane zarra da tsoro, sai ma idan sun kalleka da waÉ—an nan shaggun idanun nasu masu rikitarwa.
Kasa ƙarisa magana Conol ya yi saboda ido da Lion ya wurga mashi, bai san time ɗin da ya haɗiye maganar ba..... "I am speaking, yet the soldiers and the navy officers keep interrupting me! I talk and they talk over me! What kind of disrespect is this?!". Lion ya faɗa yana sauke idanunsa ƙasa saboda ya ga gabaɗaya ya rikita conol yasa sai zufa yake ta faman haɗawa na tsaresa da kallo da ya yi, yasa bawan ALLAH shiga ruɗu da tashin hankali tamkar ba jami'i ba, kun san su fa SSO kowani kaki shakkansu suke ji, ai na faɗa maku matsayinsu da kuma horonsu, musamman su da suka matsayin admirals ai sama suke da sojoji da sauran kaki.
Cikin zafin nama GAT and CONOL suka miƙe, at the same time suka sara mashi game da cewa. "Sorry sir"......... Shiru bai yi magana ba, dan yana son zuciyarsa ta ɗan sauƙa ne kafin ya yi magana, watau Lion shi irin mutanen nan ne masu balain saurin fusata, dan dai baya son hargitsa taron nan ne, akwai wani saƙon da yake son isarwa, ba dan haka ba yadda yake da saurin fushin nan da ya jima da kai masu duka sai dai su ji hakwaransu a ƙasa lokacin da suka shiga maganarsa, amma ya daure yana dannar zuciyar kada ya sumar da mutum.
Hasbiyallahu waniimal wakil kafa 10 ya maimaita a cikin ransa, take zuciyar ta sanyayya, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa........ "Dik wasu jami'ai dake da sa hannu a kan ta'addanci, da waÉ—an da suke tallafawa masu tada zaune tsaye, harda masu sai da makamansu ga Æ´an ta'adda dik ku kwana da shirin cewa SSO idanunta na kanku, kuma aikinmu tamkar iska yake, babu wanda yake iya sanin lokacin da aikinmu zai biyo ta kansa, kamar yadda babu wanda yake da sanin lokacin zuwan iska ko guguwa waje!". Ya É—an dakata saboda baya iya juran dogon magana.
Zazzaro idanu sosai suka yi a kansa, Conol a cikin ransa ya ce kai kaga yadda yake magana yasa na ji tamkar naga mutuwa a gabana ne take mun magana!.
Sai da ya nisa kafin ya cigaba da cewa. "SSO bata magana biyu, kowa kuma ya shaida!". Yana kai karshe ya koma ya zauna tare da ɗan yin ƙasa da kai tamkar mai tinanin wani abin.
Ai kusan duk jami'an dake wajen sun yi mugun shan jinin jikinsu, dayawansu tsoro ya bayyana a kan fuskokinsu, dan kamar yadda ya faɗa ne SSO basu taɓa magana biyu ba, tarihi ma ta shaida.
Wani irin daɗi His Excellency ya ji na jin abin da Lion ya faɗa, watau shirin kifar da gwamnatinsa suke yi ta ƙarkashin ƙasa kenan? Lallai kuwa da matsala.
Karin wani haske, kunga da His Excellency da su Lion suna da kusanci sosai, Mr President yana mugun kaunarsu sosai da sosai.
Wannan tsakanina da ku ne masu karatu, zan faɗa maku abin da su Lion basu sani ba, sun ɗauka kawai Mr President yana sonsu ne saboda jajircewansu a kan aiki kuma suna taimakawa gwamnatinsa, amma a gaskiya ba haka bane, shi ɗin jininsu ne, amma daga su har shi basu san da hakan ba, sun ɗauka shakuwa ce kawai take a tsakaninsu, amma gaba zaku ji wani irin alaƙace a tsakaninsu, shin ɗan uwan waye daga cikinsu, guru ne? Ko Lion? Ko dai Aryan? Mu je dai zuwa.
Wani irin musulmin shiru ɗakin taron ya kara yi, sai da Mr President ya yi gyaran murya tare da cewa su cigaba da jawabinsu. COAS ya fara bada rahoton ayyukan sojojin ƙasa a yankunan da ake fama da ƴan ta'adda.
CNS ya bada bayanan ragin fashin teku, musamman dilolin kwaya, ya bada rahoton irin jajircewar da suka yi wajen ganin an daina shigo masu da kwaya. Sai dai yana magana yana kallon Lion da ya yi ƙasa da kansa, su Aryan dik sun yi ƙasa da kai, IRON FIST basa son ana kallonsu, saboda kada ma wasu su haddace wani daga cikin halittar fuskansu, kun san su ɗin ruwa biyu ne, sai da ɓoye kai, so sun tsani kallo matuƙa, shiyasa dik in da zasu je kansu a ƙasa.
Bayan sun kammala jawabinsu ne aka fito da sabon tsarin zone enforcement protocol dan ƙara inganta tsaron ƙasar. Mr president ya ce a tsananta tsaro sosai, sannan dik jami'an a sabonta masu kayan aiki na zamani da sabbin makamai, aka rubuta takarda, suka tsara komai. Sai da aka gama Mr President ya kalli SSO, a natse ya ce. "Baku bamu naku tsarin ba? Kuma muna buƙatar shawarinku amma baku ce komai ba".
Shiru wajen ya yi suna jiran jin ta bakinsu. Amma babu alamar Aryan da Lion zasu motsa, saboda karairayin da wasu daga cikin jami'an nan suka sake shirgawa ya matuƙar kona masu rai, shi ne suke cooling down na temper ɗinsu kada su sanya lahira tai baƙo.
Haka dik jami'an nan suka bada ra'ayoyinsu da shawarinsu game da dabarun da suke ganin ya dace abi, amma su dai SSO shiru babu wanda ya ce word. Dole aka kyalesu dan shi Mr President ya san su waye su, dan haka shirunsu shi ne mafi alkhairi ga kowa dake hall É—in.
Bayan gama jin shawarin kowa Mr President ya yanke shawarin da ta dace, sannan ya umarci sabbin matakai.
Karfe 4 na asuba daidai suka gama wannan zama, Mr President ya yi wa kowa godiya game da gargaɗi mai karfin gaske, musamman ga ministan tsaro, sannan daga karshe guru ya rufe masu taron da addu'a, dan su Lion kam har yanzu sunƙi ɗago kai bare su sake yin magana.
Mr president ne ya fara fita, then su Lion suka rufa mashi baya, kai tsaye cikin gidan suka shiga, dan sun saba, in sun shigo Washington a nan ma suke sauƙa, ba yadda His Excellency bai yi da su ba kan su dawo Washington da zama amma suka ƙi, a New York aka haifesu har suka girma ba zasu iya ƙaura ba.
Already suna da room É—insu a gidan, dan haka shiryar suka yi tsab bayan sun yi wanka, suka fito zuwa masallacin shigaban kasa dake cikin fadar. Bayan sun yi sallah suka hau hanyar komawa New York, basu sake zama da Mr President ba dik da cewa ya so hakan, ya so su yi zama kan bincken nasu amma ba dama sai kawai ya hakura suka wuce.
Tin da suka kama hanyar airport Lion ya kifa kansa da jikin kujerar mota yana wani irin sauke numfashi mai ɗumi. Da farko Aryan ya so sharesa, amma ya ji ba zai iya ba, sai ya matso ya dafa shi tare da tambayansa me yake faruwa?. Tamkar zai haɗiyi zuciya ya mutu, sai da ya yi shirun good 5 mins, har sun fidda ran zai yi magana, sannan in a harsh way ya ce. "Ta ya za'ayi duniya ta gyaru? Ta ko'ina gurɓatattu ne! Son kai, zalunci, cin amana, son duniya, son abin duniya, dik ya cika zuƙatan kowa! A haka ta ya za'ayi duniyar ta gyaru?".