← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 227

Sashe 206

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kada ku manta team 1 dik suna da laptop a halin yanzu...... Daga nan ya zaƙulo bayanan Angelina ya turawa Zaynish da nashi bayanin shi ma. Fito da bayanan Manassa ya yi, ya san ba jami'a bace, surgeon division general ce, amma dik da takasance likitar sojoji a jikinsa yana jin tana da sani kan aiki irin nasu Arya, kuma ya san dik da take surgeon general to fa anbata horon kare kai, dan wannan dokar AZURE ce, harta likitocin sojoji suna karɓar hoto dan kare kansu.

Dan haka sai ya ce. "Arvash kira mun Manassa yanzu"....... Miƙewa Vash ya yi, ya fito. Zaune ya iskota suna hira da Juraiz, ta ɗan saki jiki tana biye mashi, a tinanin Juraiz V ce ba Manassa ba, dan shi baya iya rabesu fa, shiyasa ya tsaya sai tsarata yake yi.

Take kishin larabawan ta motsa, tamke fuska ya yi sosai game da cewa. "Ke! Sir Nirash na kiranki". Yana faɗa ya juya ba tare da ya kalli in da Juraiz yake ba. A hanzarce ta miƙe, bata lura da yanayin face ɗinsa ba, da sauri ta rufa mashi baya suka shiga tantin Leo.

Kamewa ta yi ta sara mashi kafin ta ce gatan nan......... A dake ya tambayeta game da aiki irin nasu Arya shin tana da kwarewa a kai?..... Kai ta gyaɗa game da sanar dashi cewa dik abin da su Arya suka sani ita ma ta sani kamar yadda dik abinda ta sani a ɓangaren nata aikin suma sun sani. Ya ji daɗin jin hakan, sai ya ce. "You can go". Ya faɗa game da dawo da kallonsa a kan laptop ɗinsa.

Take ya kwashi bayananta ya turawa Vash da bayanin yadda zasu yi aiki a tare........ Ita kuwa ta zo dab zata fita Vash ya ce. "Daga nan ki wuce cikin tantinku! Dare ya yi". Yana tamke fuska ya faÉ—a, babu wasa a tattare da shi. Cikin girmamawa ta ce. "Okey sir". Ta faÉ—a tare da ficewa.

Duka Noor ya kai mashi a damtsen hannunsa yana faÉ—in. "Ya da tamke fuska mutumin, ko dai ko dai?"..... Kara tamke fuskan ya yi. "Ko dai ko dai me?". Ya tambaya irin ban gane komai É—in nan ba.

Noor ya ce. "Ko dai kana ciki da sister ɗin tamu ce?"....…... Kai ya girgiza game da cewa. "Kawai dare ya yi ne, amma ni bana cikin komai"........ Zaynish ya ce. "In ta yi wari zamu ji"....... Murmushi Noor ya yi. "Kyalesa my Tiger, zai yi bayani ne". Cewar Noor ɗin.

Leo dai aikinsa ya cigaba da yi a laptop É—insa, ya fito da email na Arya, ta nan ya yi mata hello game da cewa it's Nirash, dik wani information ki saka mun shi tanan, zan duba...... Sosai Arya ta ji babu daÉ—in ganin ya ce ta tura mashi ta email, hakan na nufin ba zai dawo tantinsu ba, ta so ne ya dawo ko kallonsa ta sake yi kafin ta yi barci, to amma ya zata yi? Haka ta danne tana shafa kan Jehan da ta tada kai da cinyarta tana aiki da hannu É—aya, dik wani sabon abu da zata gani sai ta yi screen record ta tura mashi.

Shi ma ya tasa laptop gaba yana aiki ba kama hannun yaro, tin yana É—an jiyo hiransu Noor sama-sama na shakiyancin da suke yi wa juna har hankalinsa gabaÉ—aya ya bar kansu, bai ma san time É—in da suka fice daga tantin kowanne ya wuce nasa tantin ba....... Wajen wuta Noor ya nufa, yana zuwa yasa hannu ya É—auki V cak a yadda take zaune É—in, ta baya ya É—auketa.

Bai direta a ko'ina ba sai cikin tantinsa. A tsakiyar electric mattress ɗinsa ya direta game da sauƙowa, ya zare rigan jikinsa ya ajiye kafin ya haye. Kwanciya ya yi a miƙe, cike da shagwaɓa sosai a muryansa ya ce. "My Juliet, tausa nike so, jikina na mun zafi".

Miƙewa zaune V ta yi, ta haye kan flat tummy ɗinsa, damatsan hannunsa dake a murɗen nan ta fara matsa mashi da lausasan tafukanta tana faɗin. "Sorry my Romeo"........ Lumshe idanu ya yi laushin tafukanta na ratsa shi.

Ganin haka yasa ta dage ta kara yi mashi sosai tana ta faman yi mashi sannu, ya É—aura hannunsa É—aya a kan mazaunanta ta baya yana aikin shafe mata su.

Ta jima tana matsa mashi jikin kafin ya juya da ita, ta koma ƙasa shi ya dawo sama, kurawa juna ido suka yi, ya ɗan turo mata baki, a shagwaɓe sosai ya ce. "Julie, I'm in need of something very urgen".

Tana binsa da wani irin kallon ƙauna ta amsa da. "What's that?"...... Sumbatar ɗan bakinta ya yi kafin ya amsa da. "You"........... Lumshe ido ta ɗan yi game da sake buɗewa. "I'm yours already"..... "Sure?". Yana shagwaɓe fuska ya faɗa. Kai ta gyaɗa mashi alamar very sure ma kuwa. Sumbatar gefen kumatunta ya yi game da komawa gefe ya kwanta, sai ya kawota jikinsa ya rungume. Daga nan ya ce su yi barci.

Ba musu ta lafe luff a kirjinsa, ba jimawa barci yai awon gaba da su. A ɓangare Leo da Arya kuwa, tamkar yadda dare yake matsayin rana a wajen ƴan ta'addan nan, haka yakasance a wajensu. Aiki suka sha har karfe 3, tana tare da laptop ɗinta shima yana tare da na shi, sai da nasa ta ɗauke caji ya kare, sannan ya hakura, yai mata dropping messages through sms kan da safe zasu cigaba, da yake dik suna da number abokan aikin nasu, sai ya laluɓo nata ya turo mata saƙon.

Yana tura mata ya kashe wayar, yai addu'ar barci ya kwanta. Ba jimawa barci tai awon gaba da shi. Ita ma kashe nata laptop ɗin ta yi, dama ba caji sosai, batteryn solar takusa ɗaukewa, tana kashewa ta miƙe ta ɗauki Jehan da ta yi barci a jikinta ta kwantar da ita saman mattress, ta gyara ta kwanta a gefenta, already su Angelina sun jima da yin barci.

Saura sojojin dake sansanin suna bakin wuta suna ta hira tamkar rana ce ba dare ba, su Juraiz dik sun shiga tantunansu. ASUBA TA GARI.

MORNING D----O----L 🌅🔥

Asubarsu ta fara ne da farar asuba, shirin yin sallah suka yi, suka yi zaman karatun Alkur'ani mai girma kafin su yi askar ɗin safiya, Leo ya koyawa Noor karatun Alkur'ani na surori biyu daga ta ƙasa, ya fara ɗaukar haddarsu.

Around 7 daidai suka tashi daga wajen sallar, suka nufi cikin tantunansu, a nan ne kowanne ya buƙaci ganin macen da zai yi aiki da ita.

A can gefe kuwa, safiyar Arya ta fara ne da yi wa Jehan wanka, ta shafeta da mai, sai ta sanya mata kayanta tin da Jehan É—in bata da kaya, wandon jeans baki da top fari, kayan sun É—an yi mata yawa, amma haka ta sanya. Arya zata fita zuwa wajen koramarta Jehan ta ce zata bita. Hannunta takama suka nufi wajen koramar.

Da zuwansu Arya ta shiga ruwa, Jehan ta tsaya bakin ruwa tana ta faman kallonta, tana murnushin dake kara mata kyau sosai. Watso mata ruwa a fuska Arya ta yi tana faÉ—in. "Zaki shiga ne?". Ta faÉ—a game da yi mata nuni da hannu ta alama tana É—aga mata gera guda

Da sauri Jehan ga jinjina kai, dan mayyar son ruwa ce. Alama Arya tai mata da hannu kan ta shigo, da sauri ta cire wandon jeans É—inta, sai taki cire riga dan an fara kirgan dangi, girma ya fara zuwa, dik tana kunyar cire rigarta a gaba kowa, idan Arya zata yi mata wanka sosai take jin kunya, kawai daurewa takeyi.

Arya ta fahimci hakan shiyasa bata takura mata kan ta cire rigar ba. Da rigar ta faÉ—o cikin ruwa. Angelina dake tsaye a can nesa ne take mamakin yadda Arya take wasa da Jehan, sun dai san Arya macece miskisla mai mugun shariya ga mutane, ko su da suke Æ´an huÉ—unta ma bata sakewa da su har haka bare mutanen waje, makaranta wannan ba'a gani a waje sai dole, bata murmushi bata magana sai aiki, abin ya yi mugun basu mamaki, lallai sun yarda so gamon jini ne. ALLAH ne ya haÉ—a jinin Arya da Jehan.

Jawota kusa da ita Arya ta yi tana faɗin. "Kada ki je ta bakin nan ruwa ya tafi mun dake". Riko hannun Arya ɗin ita ma ta yi suka cigaba da juyi a cikin ruwan..... Unexpected suka ji hayaniya ya fara tashi daga cikin sansaninsu, Arya na ƙoƙarin saurarawa ta gano menene sai ga Manassa da gudu tana faɗin. "Bloody, waɗan nan masu kiwon shanun da kika ɗauko Jehan a wajensu har kika daki mutanensu ne suka yi gangami da sanduna suka shigo sansaninmu wai zasu kashemu".......... Toh fah, Fulani sun biyo sahu, sun zo ɗaukar fansa.

*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faÉ—akarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaÉ—antarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account É—ina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita É—in da zaku yi payment É—inku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faÉ—a maku komai.*

Likes comments and share fisabilillah.

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥

🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

For more information 08161390581 Whatsapp me only.

STEP 1🔥

2025-12-30.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________ 71 & 72

D-------O-------L🔥

"Bloody, waÉ—an nan masu kiwon shanun da kika É—auko Jehan a wajensu har kika daki mutanensu ne suka yi gangami da sanduna suka shigo sansaninmu wai zasu kashemu".
Chapter 206 · 0% Book details