← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 208 OF 227

Sashe 208

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Angelina ta tsorata, ta ɗauka ko Aunty Ummie ta faɗa mashi ta kirata ne, hankalinta ya tashi sosai, ita kanta Manassa da ba ita ta yi laifin bama ta tsorata. Jiki ba kwari Angelina ta miƙe ta nufi waje.

Jim kaÉ—an Angelina ta shigo É—akin fuskanta É—auke da fara'a, da sauri ta kariso ta rungumi Manassa tana faÉ—in. "Sir Zaynish ya ce a tare zamu dinga aiki daga yau, ya ce in É—auko laptop É—ina bari ya duba wani abin, kuma ya ce in zo da drone na sirri guda É—aya, ashe Aunty bata faÉ—a mashi na kirata ba, na É—auka ta faÉ—a mashi ne har na ji hankalins ya tashi". Ta faÉ—a cike da farinciki.

Rungumeta Manassa ta yi game da cewa. "Na tayaki murna beb, daga nan zaki sace zuciyansa, ki mayar da hankalinki sosai, ki dage da aiki, ki dinga yin abubuwan da zai sanya ki shiga zuciyansa sosai". A cewar Manassa. Saketa ta yi tana faÉ—in. "Nagode da shawara my love".

Kai kawai Manassa ta jinjina, ɗaukar laptop ɗinta ta yi ta nufi waje. Cikin tantinsa ta shiga, yana zaune yadda ta barshi, ya jawo nasa laptop ɗin ya kunna yana ƙoƙarin sanya password kenan ta shigo baki ɗauke da excuse. Ko kallon in da take bai yi ba. A kusa da shi ta zauna game da fara bin ɗakin da kallo, ko'ina tsab-tsab, an share an goge, yana da mugun tsabta.

Kunna nata laptop ɗin ta yi game da miƙa mashi drone na hannunta, ba tare da ya kalleta ba ya karɓa, da kansa ya duba charjin drone ɗin, ya kuma saita shi kafin su sake shi a tashi, a daidai lokacin Arya tana kokarin dawo da drone ɗinta sansani saboda cajinsa ya kare zai iya faɗuwa ƙasa.

A natse Zaynish ya ce. "Bana son wasa a aiki, bana son ɓata lokaci, ki mayar da hankali, dik wani motsi na drone ɗin nan ki sanar dani da gaggawa, dik abin da kika gani ki yi gaggawar sanar dani, bana son maimaita magana biyu kan abu ɗaya". Ya yi maganar ba tare da ya kalleta ba.

Da okey sir ta amsa mashi cikin girmamawa, sannan ta fara bin drone É—in zuwa wajen wannan hayaki, dan shi ne aikin dake a gabansu yanzu....... A can cikin tantin Leo kuma, ya kira barrack a wayarsu dake amfani da tauraron É—an adam wanda babu ruwansa da network, ba kamar sauran wayoyi ba, wayar ujila ce, kira É—aya zata shiga ba kwana-kwana.

Kira ya dannawa BRIGADIER GENERAL AMEEZAN (BGA) dan wannan Mission na arewacin team É—insu sun tafi ne a karkashin umarnin BGA da kuma MAJOR GENERAL RAHEEL (MGR) sune ke da alhakin basu umarni a kan komai, suke controlling É—insu. Bugu É—aya BGA ya É—aga tare da faÉ—in. "Hello".

Tattare natsuwansa waje guda sosai Leo ya yi, cikin girmamawa ya ce. "Good morning sir"........ Daga can BGA ta amsa da. "Morning how is your work?".

Da Alhandllh Leo ya amsa mashi kafin ya ce. "Akwai wani information sir". BGA dake dake kan office chair É—insa ne ya amsa da yana sauraronsa. Bayanai kan hayakin nan da suka gani gabaÉ—aya Leo ya sanar da shi, ya ce zasu je su duba menene a wannan waje dan drone É—insu yaki ketara cikin wajen, ya bashi bayanin komai, ya rufe da suna jiran umarni.

A dake BGA ya ce. "Wait for my feedback, zamu yi zaman gaggawa a kan hakan yau, dik hukuncin da muka zartar i will let you know"...... Jinjina kai Leo ya É—an yi game da cewa. "Okey sir".

Katse kiran BGA ya yi, nisawa Leo ya yi yana É—an tinani, yana jin kamar ya shigar da abin da suka gani kan Æ´an ta'addan nan ma a hukumance su jira umarnin manya, yana jin kuma kamar su yi aikin without waiting for they're permission, shiru ya yi yana tinani, can ya ce bari ya kira Captain Onbish ya faÉ—a mashi batun hayakin nan ya ji me zai ce.

Laluɓo number Captain ya yi, bugu ɗaya Captain ya ɗauka game da kara wayar a kunne, yana zaune a office ɗinsa yana haɗa takardun zaman da zasu yi this coming two days kan yanayin tsaron ƙasar.

Bayan sun gaisa Leo ya sanar da shi abin dake faruwa da kuma abin da BGA ya ce mashi. Miƙewa Captain ya yi, ya shiga cikin toilet saboda camerar dake office ɗin, da alama baya son aji hiransa da Leo. A natse Captain ya ce. "Tin da ka rigada ka sanar da shi, wait for his permission, and dik umarnin da ya baka let me know, sannan ka kiyaye, ka yi taƙa tsantsan, muna da zama in the next two days dama, and nasan yau za'ayi zaman gaggawa a kan wannan batu, ka ankare, dan a cikinmu akwai waɗan da basa tsoron ALLAH, ka sani idan wannan hayaki ya gifta ta kan aikinsu to zasu hareka ne ta bayan fage, a zaman meeting ba zasu yarda su fito da alaƙarsu da hayakin ba, sai dai su sayi sojojin dake kewaye da kai, su sanya a kashe bakinka a kan hayakin, kaga sojojin bar one ne a tare da kai, babu abin da suka sani face karɓar umarnin manya, dan haka idan aka basu umarni daga sama tsab zasu ci amanarka, domin haka ka ankare, ina fatan dai ALLAH yasa babu seniors ɗinmu dake da sa hannu kan wannan hayaki bare a cutar da kai".

Dik da a dunkule Captain yake mashi magana hakika yana gano komai, Leo mutum ne mai karanta kasan harshen mutum, ya gano Captain sarai, lallai Captain baya son fitowa fili ya ce gurɓatattu sun yawaita a hukumar sojan, kuma da alama Captain ɗin yasan wasu daga cikinsu, yasan daga ina matsalar take, amma ba zai iya faɗa ba, yana dai faɗa ma Leo ya yi taƙa tsantsan.

"In Sha ALLAH zan kula sir, Nagode da shawara". Leo ya faÉ—a cikin girmamawa, ya rasa meyasa yake tsananin kaunar Captain, yana jinsa tamkar É—an uwansa na jini haka, haka shi ma Captain É—in, yana mugun son Leo sosai, shiyasa ma yake fitar mashi da sirrin GIDAN SOJA dik da yake sabon soja bai jima da fara aiki ba, amma kunga yana sanar da shi sirrin AZURE amma a dunkule cikin sirri.

Sun jima suna hira tamkar abokai kafin daga bisani suka yi sallama, Leo ya yi shiru yana nazarin kalaman Captain, lallai kuwa akwai matsala, a cikin ransa ya ce. "Tabbas zan canza hukumar soja, lallai zan juya tsarin abin, In Sha ALLAH nine mutum na farko da zai fara rusa banzan tsarin nan in shigo da sabbi, daga wannan rana da na kawo sabon tsarina ba za'a sake samun gurɓataccen jami'i ba, zan kafa tarihin da ba'a taɓa kafawa ba, zan bar baya mai kyau".... Nisawa ya ɗan yi game da turawa Arya saƙon ta shirya akwai in da zasu je by 8 PM.

Daga nan ya miƙe ya fita, ta baya ya bi ba tare da ya sanar da kowa in da zai je ba.

A can gefe kuwa, V ce zaune a cikin tantin Noor rike da laptop É—inta tana kokarin kunnawa. Shigowa ciki ya yi tare da sake labulen da suke sanyawa kofar tantin. ÆŠago kai ta yi ta sauke kallonta a kansa. Bosy smilling ya É—an sakar mata yana kallon kirjinta dake mashi welcome, sleeping dress ne a jikinta bata cire ba, ko wanka bata yi ba, bama ta jima da tashi ba.

Shi kuma yana sanye cikin uniform ɗinsu, ya je bakin ruwa ne ya dawo, zai shigo ɗakin ya umarci da a saki fulanin nan su tafi. Ba musu sojojin AZURE suka rakasu da bulalu suna zanesu har suka isa wajen huts ɗinsu, sun ji a jikinsu, idanu dik ya rena fata. Wanda Arya tai wa kaciya kam ma ALLAH ya karɓi rayuwansa daren jiya, ɗayan matashin ma yau da asuba ya mutu, shi ne fulanin suka fusata suka zo ɗaukar fansa.

Zuba mata idanu ya yi, da sauri ta miƙe tsaye, tana sakin cool smiling ta ce. "Good morning my Romeo"...... Ciki ya ƙariso yana amsa mata gaisuwar, dik ya nemi natsuwansa ya rasa, yana jinsa a wata duniya na daban.

Zama ya yi gefen mattress ɗinsu yana kallon kyakkyawan surar jikinta dake ƙara ɗaukar hankalinsa, ya kai hannu ya ɗan mari mazaunanta kafin ya riko hannunta ɗaya. A saman laps ɗinsa ya zaunar da ita game da jawo laptop ɗin nata, a tare suka fara pressing, ya ɗaura hannunsa ɗaya a kan flat tummy ɗinta, ya ɗan kwanto da kansa gefen wuyanta kaɗan yana shakar kamshin shampoo na gashinta.

Pressing na laptop ɗin take yi cike da kwarewa tana controlling drone ɗinta da ta tura yanzu. Lokaci guda ta ɗan ɗauke wuta game da dakatawa daga pressing ɗin jin sauƙar hannunsa gabaɗaya a saman fatar cikinta, ya ɗage mata rigar sleeping dress ɗin.

Wani irin dogon numfashi ta ja game da saukewa a hankali. Yana ɗan turo baki ya ce. "My Julie, ina cikin wani yanayi". A shagwaɓe ya faɗa. Bata iya motsawa ba, ta dai cigaba da yin shiru tana jin yadda yake yawo da hannunsa a kan cikinta. Sai kuma ya haurar sama izuwa kan tula-tulanta.

Wani irin nisawa ta yi a lokacin da ya taɓa breast ɗin nata, ai narke mashi ta fara yi tana sakin jikinta. Kara matseta a jikinsa ya yi, slowly ya sauke laptop ɗin ƙasa game da juyawa da ita, suka koma saman mattress ɗim. Ya kwantar da ita kafin ya zare rigan jikinsa. Dawowa kanta ya yi, ta yi shiru tana binsa da kallo, ga wani irin shaukin soyayyansa dake ɗebanta.

Cikin wani irin salon kauna ya haɗe bakinsu waje guda, hot kiss ya fara bata. Bata yi ƙasa a gwiwa ba ta fara mayar mashi da martani, ai take suka narkewa juna, suka fara bawa flower ruwa, take ya rabata da kayan jikinta, ya mance in da yake da kuma cewa rana ne ba dare ba, dik da babu wanda zai shigo mashi ba da izininsa ba amma rana ai da kunya.
Chapter 208 · 0% Book details