Sashe 38
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To zan ɗan taƙaice training ɗin nan ne ba dan komai ba sai dan labarin yana gaba, manyan abubuwan da yakamata ku sani suna gaba ne, kada mu ja lokaci a horar da su! Dan tafiyar bama a fara ba! Shiyasa zan taƙaice maku shi amun afuwa!.
A ɓangaren Ummie, cikin ikon ALLAH ta kama sana'a da kuɗin da Zaysh ya bata, ALLAH ya zubawa abin albarka, tana samu sosai, dan haka bata damu da auren da mijinta ya ƙara ba, an yi auren an luma kawo yarinyar gidan an haɗasu, ba kalar rashin mutuncin da yarinyar bata yi mata, amma ko kaɗan bata damuwa da ita, ta mai da hankali kan kasuwancinta, tana kuma yin waya da ɗan uwanta yana kwantar mata da hankali, har yanzu dai ciki shiru babu shi babu labarinsa, bata nuna damuwarta, tana dai cigaba da addu'ar ALLAH ya bata mai albarka!.
Zaysh dik in ya samu wani kuɗi sai ya ƙara mata, yanzu tana da babban shagon sai da abayoyi, kishiyar tata bata da burin da ya wuce ta ga shagon ya durkushe, ta yi balal'in duniyar nan kan lallai mijin ya buɗe mata nata shagon, ya ce shi bashi da kuɗi, ita ma Ummie ba shi ya buɗe mata ba, ɗan uwanta ne, to shi ne take ta ƙulla makircin yadda zata yi shagon ya durkushe komai ya kare dan mugunta da bakin hali, kuma wlh Ummie bata rageta da komai ba fa! Har kyauta tana yi mata, kawai dai mugun hali ne.
--------------------🔥
Yau ta kama ranar Friday, sai shirye-shirye Ummie take yi, ranar Monday zata je kasar Avaris passing out na Zaysh, dan zasu fita, tin da ya tafi bata sake sanya shi a idanunta ba sai waya kawai, kunga kuwa sai murna ai yanzu.
Kaya akwati guda ta shirya, kuma ita kaɗai zata tafi, dan mijinta bashi da halin biyan kuɗin jirgi, ita ɗin ma Zaysh na zai biya mata, ya ce kada ta taɓa kuɗin shagonta, shi ma kuma Vash ne ya bashi kyautar kuɗi ya ce ya yi shirin passing out ɗinsu, shi ne ya tura mata ta zo. Danginsa sai zaginta suke yi, wai yawo zata je, dama sun ƙala mata sharrin bin maza, wai idan ba bin maza take yi ba a ina ta samo kuɗin buɗe shagon nan nata?. Ita dai bata ce masu komai ba, suka ce ai sun san basu da komai, marayu ne, waye ya bata kuɗi?.
Bayan mijinta bata faÉ—awa kowa ga wanda ya bata ba, ta koma gefe ta yi shiru tana kallonsu.
Bayan ta kammala shirya akwatinta, ta rufesa kenan sai ta ji ana sallama a parlo. A natse ta amsa tare da miƙewa ta fito dan ganin wanene?. Cike da mamaki ta zaro idanunta a lokacin da ta ga mai daka mata sallamar. Muryarta har yana ɗan rawa wajen cewa.......
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥ï¸
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
STEP 1________🔥
10-11-2025.🔥
FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥ï¸ðŸ”¥
E_____________9
Bayan ta kammala shirya akwatinta, ta rufesa kenan sai ta ji ana sallama a parlo. A natse ta amsa tare da miƙewa ta fito dan ganin wanene?. Cike da mamaki ta zaro idanunta a lokacin da ta ga mai daka mata sallamar. Muryarta har yana ɗan rawa wajen cewa. "Lafiya kika shigo mun parlo yau kuma?".
"Lafiyar ce ta kawo haka"........ Ɗan zare ido Ummie ta yi, sai kuma ta basar da cewa. "Okey me yake tafe dake?"..... Shiru yarinyar ta ɗan yi, can kuma sai ta ce. "Albishir na zo yi maki, abin da kika kasa bawa mijinmu yau ALLAH ya bashi a jikina". Ta faɗa tana shafa shafaffen cikin nata. Wata figaggiya da ita kamar kazar mayu, wannan idan babban mota ya zo da gudu iskansa tsab zai kaita ƙasa, ba welcome bare goodbye, tana nan kamar namiji ya ɗaura zani!.
Ajiyar zuciya Ummie ta sauke, take murmushi ya bayyana a kan face É—inta, a sanyayye ta ce. "Kai Alhamdllh, ALLAH mai kyauta mai kari, UBANGIJI ya saukeki lafiya, amma na tayaki murna, banda abinki da rigima ai nima bani na hana kaina ba, ALLAHN da kika ce ya baki shi É—in ne dai mai bayarwa, kuma shi ne bai bani ba, a haka kuma ina gode mashi ina karawa, amma wlh na yi murna da ALLAH ya bamu ta wajenki, ai dik É—aya ne!". Da iya gaskiyarta ta yi maganar, dan ALLAH ya É—aura mata jaraban son yara, yara makota dik a wajenta suke wuni, dan haka bata bakinciki da wannan ciki, wlh idan aka haifa zata rike tamkar nata In Sha ALLAH baiwar ALLAH.
Wani irin ɗaure fuska amaryar ta yi, dan ita ba ta kawo mata labarin dan ta yi murna bane, burinta ta kuntata ma, amma sai ga shi tana murmushi. Cike da takaici ta ce. "To ai ba ɗanki bane, nice uwarsa, kada ki taɓa sa ran zai zo ko da kusa dake ne"......... Sosai Ummie ta ji kirjinta ya buga, sam bata ji daɗin hakan ba, ta zaci ai zasu haɗa kai su reni yaran ne!
Ganin fuskanta ya canza yasa amarya jin daɗi, burinta ya cika ta kuntata mata, dan ta kara mata takaici ma sai ta ce. "Idan fitsari banza ne kaza ta yi, ki haifi naki, nawa basu da alaƙa dake juya kawai, almost shekaru 5 kenan yanzu da aurenku ko ɓari baki taɓa yi ba, wai har mazan da kike bi ma babu wanda ya iya yi maki cikin ne? Sai kuɗi kawai suke baki? Ko da yake kece juya, ko zasu dinga kwana a kanki ba samun cikin zaki yi ba". Ta kai karshen maganar tare da juyawa tana wani hura hanci, ta nufi waje.
Tsaye Ummie ta yi, take wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska, da gudun gaske ta shige cikin ɗaki, babu abin da ya fi bata takaici irin ƙazafin zina da suke mata, a dik san da suka ce maza take bi suke bata kuɗi sai ta sha kuka, ga shi yau tsawon wattanni 8 bata samun damar hira da Zaysh, dan tin da suka shiga horo na karshe-karshen nan ba'a basu waya ba, an karɓi wayoyinsu, sai ranar Sunday yake kiranta da wayan securitys officers, kuma mintina biyar ake basu su gaisa da gida su ji idan kowa yana lafiya, baya ga haka basu da wani lokaci ɓatawa, dan a watannin karshen nan horo wuta-wuta ake basu babu kama hannun yaro.
Kuka ta ci mai isarta, sannan ta miƙe ta ƙarisa shirinta, wunin ranar haka ta wuni cikin ƙunci, sai can yamma ta nufi shagonta dan su yi lissafi gobe zata yi sammakon tafiya Abuja, daga nan zata hau jirgi zuwa Avaris, ta so zuwa Niger wajen ƴan uwanta na kauye ta kai masu abin arziki tin da ta ɗan samu rufin asiri, amma ba dama, sai ta ce bari ta bari sai ta dawo daga Avaris ta sauƙa ta can!.
Ko da ta zo fita sai da amarya ta yaɓa mata magana, wai dan ta ji tana da ciki ne dik ta shiga damuwa har da kuka ido ya kumbura, ita dai bata ce komai ba ta fice abinta. Sai habaice-habaice amarya take yi.......... Ita dai bata dawo gidan ba sai dare, a shagonta ta yi sallar mangrib da ishai suka yi lissafi da yaron shagon, sannan ta sayi abinci a restaurant ta dawo da shi. Tin da ta shiga ɗaki ta rufe kofa bata sake fitowa ba, dama mijin ba'a ɗakinta yake ba.
A ciki ta ci abincinta ta ƙoshi, daga nan ta kwanta abinta, da assusuba ta tashi ta ja akwatinta, mijin nata kuma yana nuna mata tsantsar so da kulawa, dan kuwa har tasha ya rakata da sanyin asuba, sai faɗi yake yana nanatawa kan ta kula da kanta. Da motarsu ya zo tashi ma, ya ƙanƙame hannunta yana faɗin zai yi kewanta sosai, ita ma har kwallah ta yi tana faɗin zata yi kewansa, dan tana mugun son shi, kuma tasan yana kula da ita, yana gwada mata kauna, kome yake faruwa ba yin kansa bane, ta sani kuma ta yi mashi uzuri, bata hukunta shi da laifin danginsa ba!. Ko kaɗai bai taɓa yi mata ƙazafin zina ba, masu yi ma idan ya ji ba karamin faɗa suke yi da shi ba, shi ya aminta da ita, danginsa ne dai sai shiru!.
A haka suka rabu cike da kaunar juna, ya koma gida ita kuma motarsu ya tashi sai Abuja, daga nan ta hau jirgin Mexico wanda already mijin nata ya wuce gaba wajen shirya mata komai, zata sauƙa a can, gobe ta hau jirgin Avaris kai tsaye, already an shirya jirgin da zasu tafi Avaris ɗin a Mexico, jirgi direct daga nan Naija zuwa Avaris ne babu, sai an yi masu juye a Mexico, shiyasa!.
TO UMMIE SAI DAI MU CE SAFE TRAVELS!.
----------------------🔥
AZURE.
BIKIN KARRAMA MATASAN SOJOJI KO ACE PASSING OUT.
Barrack É—in gabaÉ—aya ya canza, an sake mashi fenti, dik wasu sojojin dake waje sun dawo barrack, hakan yasa barikin ta cika da dubban zaratan sojoji, ta ko'ina su ne ke ta faman shawagi.
Ranar passing out, wannan rana ce da za su saka kakin soja da cikakken kima and ƴanci, su tsaya a bainar jama'a a matsayin sabbin sojojin ƙasa, kada ku manta su ba kamar sauran sojoji bane, sun shiga horo na musamman a babi na biyu, kunga dole bikin karramasu ya zama gagarumin biki sosai!.
Tin sati biyu da suka wuce aka fara preparation for the ceremony. Yau takama Monday kuma ranar da za su fito daga É—akin horon da aka shigar dasu bayan shekaru biyu suna gwabzawa da fama. Da safiyar wannan rana, sojojin sun tsananta kai komo a cikin barikin, kowa ka É—aga ido ka gani sai ka firgita, suna wani muzurai tamkar zasu cinye mutum É—anye!.