Sashe 20
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin zaro ido waje tai tamkar kwayarta zasu faɗo ƙasa a lokacin da ta ga jajayen idanunsa tamkar wuta, dik da bata kalli face ɗinsa gabaɗaya ba ta wani irin mahaukacin razana, take ta kame waje guda kamar ta sume, dan numfashinta ya ɗauke, idanunsa sun yi wani irin ja tamkar jini ne a ciki, dik wanda ALLAH ya bashi ikon haɗa ido da wannan guy a wannan lokaci ko bai suma ba kaɗan ne zata rage mashi saboda firgici.
Ganin ta ɗauke wuta ne yasa ya mayar da hulansa, slowly ya kwantar da kanta a gefen chest ɗinsa, ya ɗan rintse idanunsa saboda tsananin zafin da hannunsa yake yi mashi, alluran kashe zafin ta fara sauƙa, kun san dole akwai zafi. Yana jin motsin yaran Eagle suka shigo room na yarinyar.
In takaice maku labari har suka kashe Dr yana wajen da yarinyar, ba zai iya zuwa ya ceci Dr ba, saboda shi kansa taimako yake nema a yanzu. Jin shiru alamar sun bar ɗakin yarinyar yasa ya kokarta ya miƙe da ita, daga alama shahararren ɗan ta'adda ne, yadda yake da dauriya da karfi kamar wani doki, dik yadda aka yi ya sha gwagwarmaya ba kaɗan ba.
Da kyar ya lallaɓa ya kama room view suka komo cikin ɗakin, ya so dira ƙasa ya bar gidan, amma ha zai iya dira da ita ba, kunga ga ciwo a hannu, ga kuma nauyinta, jikinsa ba karfi, idan suka dira a tare zata iya jin ciwo koma ta bugu a in da ba zata rayu ba, shi ma kuma haka. So dole ya mayar da ita cikin ɗakin, bata ko motsi.
Cikin toile ya kaita, a cikin jaccuzi ya kwantar da ita tare da fitowa, dispenser dake room ɗin nata ya ja zuwa toilet ɗin, da kyar ya ɗaukesa ya ɗaura a saman Jacuzzin, ya rufeta, sannan ya fito, ya koma ta view, ya dinga lallaɓawa a hankali ya sauƙo, a lokacin sun kunnawa gidan wuta sun fita. Shi ma fita ya yi.
Yasan da wuya wutar ta kamata, dan a cikin Jaccuzi ya kwantar da ita, ga disperser É—in da ya É—aura mata, shiyasa washegari ya tura yaransa su É—aukota da dik sauran abin da ya rayu a gidan dan ya rama alkhairin mahaifiyarta a garesa, ta sadaukar da ranta a cetansa, yana kwance a gadon asibiti ya turosu.
Shi ne suka zo suka É—auketa, sun sameta sume a cikin Jacuzzin, amma hayakin wutar tai mata illah, ga kuma wutar ta kakkama dik wasu robobi a cikin toilet É—in ta cinye, ko jami'an da suka zo basu san tana ciki ba saboda wannan rufeta da ya yi...... To kun ji abin da ya faru! Yanzu mu koma kan labarinmu!.
Ta jima zaune a wajen tana shan kukanta, tana ganinsa ya sauko ƙasa, ya wuce kitchen ya sauke ruwan da ya ɗaura a pot, ya sanya rariyar tea ya tace ruwan a cup, sannan ya ɗauka ya koma sama ba tare da ya kalli in da take ba. Ganin ba zai kulata bane yasa ta miƙe ta koma cikin room ɗinta cike da kunci, tana son sanin ina mammy ɗinta, meyasa aka kawota wannan irin dream house da take mafarki kullum! Suna da arziki sosai, amma CRYSTAL PALACE ba dik kai ba, sai ta zama ƴar kauye a nan.
Saman bed ɗinta ta koma ta kwanta tana cigaba da kukanta babu mai rarrashinta, ga shi bauɗaɗɗen nata ya yi sama abinsa, yana zaune a balcony yana shan tea ɗin da ya dafa cikin kwanciyar hankali da natsuwa abinsa. Bayan ya kammala ya umarci robot dake aiki a gidan da su haɗawa yarinyar abinci, su tabbatar ta ci, sannan su bata magani kamar yadda yake a tsare, kuma su yi mata wanka, yana gama basu bayani ya ɗauki wani tail coat ya sanya a jikinsa bayan ya yi wanka ya cire waɗan can, ya fita ya bar gidan, ita kaɗai a dik wannan girman gidan kamar wata mayya, ba uwa, ba uba, ba kawa, ba aboki, babu kowa sai robot, wannan ma kawai ai tashin hankali, ga shi baƙon waje.
Haka robot É—in nan suka hau aikinsu, tamkar mutane, suka shirya komai suka kai mata, maza ne su biyu. Tana kuka suka iskota. A saman table suka ajiye kayan abinci, É—aya ya taka zuwa in da take, da hannu É—aya ya É—agota, bai direta a ko'ina ba sai a saman sofar dake kusa table É—in.
Tana ta faman faɗin. "I don't want, please let me go"..... Ina babu wanda ya kulata, dan su ance su tabbatar sun bata abinci, dan haka a baki suka fara tura mata dole, abin da umarni suke karɓa, in kuma suka karɓa sai sun cika ko mutuwa ake yi.
Da taga babu sarki sai ALLAH sai ta hakura ta dinga karɓar abinci a natse kawai, ba sai an mata ɗure ba. Sosai ta ci kafin ta ce ta ƙoshi. Sai da suka tabbatar, sannan suka ɗauko magungunar, shi ma a baki suka bata ta sha, sannan ɗaya ya ɗauketa zuwa toilet, dan har da wanka aka ce su yi mata, tana cewa bata so, amma ina, ko a jikinsu, suka haɗa ruwan wanka. Dik tinaninta mutane ne shiyasa take ce masu bata so.
Tana ji tana gani yai mata zindir, ya jefata cikin ruwan katafaren glass Jacuzzi tamkar wata kayan wanki. Hannu yasa ya wanketa tas. Ai yau taga ikon ALLAH, kuka ta dinga yi tana kiran sunan Mammy É—inta, amma ina bata jinta.
Dawo da ita É—akin suka yi bayan sun nannaÉ—eta cikin towel, a kan gado suka jefata kafin su kwashi kayan abinci su fice, sun gama aikinsu kenan. Fashewa da sabon kuka ta yi, ta kifa kanta da gwiwowinta tare da jawo bargo ta rufe tsiraicinta. Kyakkyawan ash hair É—inta sai É—igar ruwa yake yi.
Tin sautin kukanta na fita, har ya daina fita, daga karshe barci mai nauyi ne ya ɗauketa a wajen, bata san lokacin da ta kwanta kudundune a cikin bargon ba, ta hau barci, ta ci kuka ta ƙoshi ja'ira. To kun ji halin da Seraph ƴar Dr take a ciki, mu haɗa kayanmu mu koma Barrack.
Note, Seraph shekarunta 10 a duniya yanzu, yarinya ce sosai.
-------------------------🔥
GIDA SOJA!. AFTER ONE MONTH.
A wannan wara É—ayan dik horon da aka yi masu a farko-farko ne ake ta maimaita masu dan ya bi jikinsu da kyau, ba'a É—aura sabon horo ba, tin suna iya mantawa har wannan horo na farko ya ratsa jikinsu sosai. Shiyasa na tsallake tin da ba zan yi ta rubuta maimaicin horo ba!.
A yau Monday watansu guda kenan a GIDAN SOJA, a yau zasu fara shiga horo sabo kashi na biyu.
Kamar kullum karfe 5:30 na asuba, bayan sun yi sallar asuba, dik sun hallara a wannan fili, a yau dai Noor ya fito, dan za su shiga sabon horo, a wata guda da suka wucen nan dik kullum sai Captain ya tashesa da duka, amma yau da yake za'a shiga sabon babi ya daure ya taso.
Sun kasance a cikin layi kamar kullum. Cikin zafin nama Captain ya tako, ya iskosu a wajen. Saman stage ya haye tare da É—an yin gyaran murya. Da sauri suka haÉ—e natsuwatsu tare da buga kafa, suka sara mashi. Jinnina kai ya yi kafin ya ce. "1, 2, 3 start!" Cikin É—aga murya.
Yana cewa start suka buÉ—i baki game da É—aga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA...... "We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, united as one, well never fall. Oh we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, a thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, our oath is strong, we'll see it through. Oh we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!".
Suna kai karshe ya ce. "Kamar yadda kuka sani ne, a yau zamu sabonta maku horo, zamu matsar dashi izuwa matakin gaba, ina fatan kun shirya?". Ya kai karshe da alamar tambaya. Wani irin kamewa suka yi alamar sun shirya ba tare da magana ba.
Rarraba idanunsa a kansu ya É—an yi kafin ya ce. "A yau zaku fara ne da endurance run for 10km". Babbar magana, gudu fa ba tafiya ba, na 10Km da matsala. Dayawa daga cikinsu sun É—an É—auke wuta, amma ganin babu fuskan wasa yasa suka daure.
Maryan Captain ne ya katsesu da cewa. "Lokacinku ya fara daga yanzu, kada ku manta lokacinku yana kirgawa ne! So attention".
Wani irin tsaki Noor ya ja tare da rike kai, har ga ALLAH ya gaji, ba zai iya jura ba fa. Ganin matasan sun fara gudu sun bar shi a wajen ne yasa yai gaggawar bin bayansu da É—an gudunsa, kada a barsa a baya.
Gudu na tsawon kilomita goma ba tare da tsayawa ba. Dik wanda ya yi baya, sai ya sake farawa daga farko. Babbar magana, kuma kun san dik wanda ya yi baya sai ya faro É—in nan ne, babu tausayi.
Haba haka suka zage dantse suka fara gudu babu wasa. Sai dai bayan kamar minti 30, gwiwowinsu sun fara raunata, amma ba wanda ke da damar tsayawa, dan ma wai a wata É—ayan can sun ta maimaita horo sun É—an samu karfi da kwari ne, da sai yaya kenan?.
Noor da ya tabbatar da gaske idan ya yi baya zai sake komawa daga farko, kuma ko mutuwa yake yi ba zasu yafe mashi ba, kilomita goma ba biyu kamar ta baya ba, yaushe zai koma baya ya sake dawowa, ai sai ya zage, yasa dikkan karfinsa wajen gudu. Da yaga kamar ba zai iya bama sai ya kwarara zuciyansa tare da yin shahada ya kama hannun Leo.