Sashe 167
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba zan ɗauketa ba Abba! Lallai ba zan saketa ba kamar yadda ka faɗa, amma kuma ka sani ka jefa rayuwarta cikin ukuba da azaba ne, ba zan taɓa sonta ko in zauna da ita ba!".......... Ammie ce ta miƙe, jikinta na kerma ta ce. "Aryan please ka yi shiru, mahaifinka ne fa!".
A fusace ya kalleta, cikin zafin zuciya ya ce. "Ki mun shiru, ba dake nike magana ba, na tabbata da mahaifiyata ce take tsaye a nan ba zata ce in yi shiru ba, ba zata yi shiru tana gani a zalunceni ba, yau da Ummie tana nan babu wanda ya isa ya cutar da rayuwata, amma saboda bake kika haifemu ba shi ne kika zuba ido yai mana abin da yake so, meyasa baki sa anyi har da Faryan ba? Saboda shi ɗanki ne?".......... Shiru Ammie ta yi tana jin zafin kalamansa, amma ta daure saboda tasan yana cikin ɓacin rai ne, da zafi abin da Abba yai masu, sun san babu wanda Aryan ya tsana biyun Rimsha, amma Abba ya haɗa wannan aure, shi ma yasan bai nemi zaman lafiya ba ai.
Abba ne ya ce. "Ohk, ni ne na cuceka kenan? Ni Aryan kake faɗawa na cuceka?!". Cikin faɗa ya faɗa. Mimmiƙewa su Faryan suka yi, Rimsha dai tin lokacin da Abba ya ce da Aryan ga matarka Rimsha, tin daga wannan lokaci da ta ɗaga mayafi ta kwala ihu ɗaya bata sake motsawa, Abba ya jefata cikin balain da yasa numfashinta ɗaukewa ta sume.
A fusace Aryan ya ce. "Abba......". Ammie ce ta yi ƙoƙarin sake dakatar da shi, saboda tasan hali, kuma tasan kome zai ce Abba fa magana ɗaya yake, in dik duniya zasu haɗu babu wanda ya isa ya sanya shi canza magana, ko ana mutuwa, ko wannan magana zata zama silar jefa rayuwar wasu a haɗari to fa ya yi ta ne, babu canji! Dan haka tsayawa ja in ja babu wani abin da zai ƙara masu, gara ta daure ta danni Aryan ɗin kawai.
"When I'm talking to my father, I don't need anyone to interrupt me, just get out of this room now!". In a harsh way ya faÉ—a, ya faÉ—a kuma ba tare da ya kalli fuskar Ammie ba, dan dik da yana cikin fushi yana jin nauyin yi mata magana without respect, dan dik da mahaifiyansa Ummie bata gidan, Ammie ta yi iya kokarinta wajen kula da su.
Rass gabansu Harleen ya faɗi, tin da suke basu taɓa ganin irin wannan musifa ba, kai Abba baya son zaman lafiya ko kaɗan, in banda neman jafai irin na Abba, a wannan yanyi zaka ce umarni kake bashi bama ka lallaɓa shi ba tin da ka yi son ranka? Mutumin da in ya birkice kai kanka gudunsa kake yi, amma wai umarni yake bashi da ya kula da Rimsha.
Nuna Aryan da scepter É—in hannunsa Abba ya yi, a fusace ya ce. "Sai dai ka nemi wani uban ba dai ni Khaiza'an ba muddin ka tsallaka wannan umarni nawa! Babu saki tsakaninka da Rimsha, kuma ka É—auketa yanzu ku tafi!". In a harsh way shi ma ya faÉ—a. Babban magana!. Gidan Abba ya rikice fa.
Juyawa da sauri Aryan ya yi, tamkar zai kifa, kamar zai tashi sama ya fice, baya ganin gabansa, kansa na mashi tsananin ciwo, zuciyansa tamkar zai fasa kirjinsa ya fito waje, ga damuwar rashin sanin in da Lion ya tafi, ga wannan bakar labarin wai an aura mashi Rimsha, wai kuma shi ya biya sadaki, innallilahi, da yasan shi za'a aurawa ita wlh ba zai kawo sadakin ba, gaskiya Abba É—an duniya ne, Harleen kuma an aura mashi Aunty Luna É—insa.
Baya ganin gabansa sam, bai san time da ya isa benensu Seraphina ba, yana shiga room É—inta ya nufi bed. Tana zaune tsakiyar gado, tana rike da waya, hawaye ya gama wanke mata fuska, tana ta kiran mumbersa bata shiga, ta damu, ta yi kuka har ta gode ALLAH, burinta ya zo ya faÉ—a mata waye wanda ya É—auki wayansa jiya.
Tana ganinsa ta miƙe, ta nufosa tana faɗin. "Daddy.....". Bata iya ƙarisa maganar ba ta dakata sakamakon ganinsa yana tangaɗi tamkar zai faɗi, ga shi ya dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi. Kallon kafafunsa ta yi, ko takalma bai sanya ba, tin daga nan ta goge hawayenta, dan tasan ba lafiya, cikin zafa ta matsa mashi hanya ganin yana ƙoƙarin bugeta tamkar bai ganta ba.
Yana zuwa ya faɗa saman bed ɗinta, ya yi kwanciyar ruff da ciki yana ƙara dafe kansa. Ai da gudu ta hawo gadon, ta zo ta ɗago kan nasa, ta ɗaura saman cinyarta, muryanta na rawa ta fara faɗin. "Daddy baka da lafiya ne? Meyake damunka?"......... Shiru bai iya tanka mata ba. Ƙara ƙanƙamesa ta yi, tana ɗan shafa gashin kansa, cikin taushin murya ta sake cewa. "Daddy ka yi magana please, baka da lafiya ne?".
Wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauƙe, ya zura hannayensa ta bayanta ya yi tighting ɗinta, yana huci mai zafin gaske. Ganin haka yasa ta cigaba da shafa kansa izuwa bayansa, ta fara faɗa mashi kalamai masu daɗi tana son shawo kansa, ya kwanta shiru a jikin nata yana jin kamar zuciyansa na sauƙa a hankali-hankali, ya zo wajen masoyiya ba.
Watau Jama'a idan ina hango cakwakiyar dake gaba a littafin nan ba, Rimsha ta auri uncle Aryan! How? Ba uncle ɗinta bane? Tambayar dake ranku kenan, to kada ku damu, zan warware maku komai. Ya auren nan zata kasance, daddy na son Seraphina, while ita ma tana tsananin sonsa, Rimsha babbar aminiyarta ce, shin ya za'a kaya, daddy zai auri Seraphina a ranar birthday ɗinta, sun zama kishiyoyi da Rimsha, a gaskiya na tausayawa rayuwar Rimsha matuƙa. A yaushe zasu gane uncle ɗin Rimsha shi ne daddyn Seraphina? Ya zasu yi idan suka gane? Dama ba Ammie bace ta haifi Aryan? Wacece Ummie da Aryan ya kira matsayin uwa? Ina kuma take a halin yanzu? Uhm akwai rikici sosai, zamu ga yadda wasan zai kaya, ga dai Rimsha baiwar ALLAH a can ta suma, ALLAH sarki ai dole ki suma baiwar ALLAH, irin wannan tashin hankali, Aryan fa aka aura maki, tab, idan akwai abin da ya fi suma ma yi zaki yi!.
To mu leƙa DOL team mu dawo, dan cakwakiyar CRYSTAL PALACE yawa ce da ita, ga Lion ya tafi bamu san in da ya yi ba. Ku karanta littafin Queen Of Surprise taku ta amana babu cawakiya ai kun san ba zai yiwu ba! Yanzu cakwakiyar zata fara mutanen kirki!.
-------------------------🔥
DOL.
Tafiya suke tsakiyar dokar daji, babu tsoro bare shakka, sun kashe light na hannayensu ma, a cikin duhu suke tafiya....... Zaynish ne ya ce. "Ina da yaƙinin akwai abin da suke shigo da shi, lallai ba iya kaya bane kawai!".
Noor dake jiki dik a mace ne ya amsa da. "Sosaima, ko kaÉ—an ban yarda da bakin ruwan nan ba"......... Sarai Leo ya fahimci halin da Noor yake a ciki na tsananin feeling, dan ko magana da kyar yake yi, amma bai nuna mashi kamar ya gane ba.
Vash dake faman dannar waya suna tafiya ne ya amsa da. "Na fi zargin suna shigo da makamai". ....... A natse Leo ya ce. "A baya kafin su shahara ne suka shigo da makamai, yanzu ina da tabbacin sun wuce wannan level ɗin, akwai dai abin da suke yi wanda ya saɓawa doka".
Tsalle Noor ya yi, ya haye saman bayan Leo tare da langwaɓar da kansa, yana saƙalo wuyan Leo ɗin yana nishi kaɗan-kaɗan........ Duka Zaynish ya kai wa Noor ɗin a gadon baya yana faɗin. "Ka dai bi a hankali, kada watarana ta hanaka aiki"...….... Kukan shagwaɓa ya saka yana faɗin. "Bro ba ka gansa ba? Wai ina ruwanka dani ne?".
Shi dai Leo cigaba da tafiya ya yi bai tanka masu ba, watau Zaynish ma ya gane halin da Noor ke ciki. ....... "Akwai ruwana da kai mana, dole in saka maka ido kwana biyun nan, dan kada ka biye mace ka lalata mana aiki, yanzu ma jibeka fa? Ka biye mata ko jurar tafiya ba zaka iya yi ba sai an goyaka, dik gaɓɓanka jikinka sun mutu, ga kasala da nauyin wando"........🤯
Wasa-wasa Zaynish mafa ya iya tsiya, baya magana amma idan yana yi da Noor sai kun sha mamaki, sai ma ku zaci bashi bane yai, kuma sai ya yi magana ya fuske tamkar ba shi ya yi ba, bai taɓa murmushi ba bare dariya ko wacce iriyar magana zai faɗa. Vash dai baya tare da su a halin yanzu, yana can yana baiwa aljana hakuri.
A shagwaɓe Noor ya ce. "Ni ku kyaleni in ji da ɗaya mana, my Juliet want kill me with her sweet, na samu da kyar na shawo kaina, na danni kaina, na biyoku shi ne zaku takura mun?". Ya faɗa yana langwaɓar da kansa a gefen wuyan Leo.
"Ai zaka iya komawa ka ƙarisar da abin da ka fara, nasan ita ma tana can tana fama da abin da kake mana a nan, dan haka ka koma kawai, kuma dama ni banga amfaninka ba, ko tafiya da kafafunka baka da kuzarin yi, yanzu idan aka farmakemu fa?". Zaynish ya faɗa yana ƙara kai mashi dundu a gadon baya.
A dake Leo ya ce. "Zaysh ka yi na kuɗinka, in ka ƙara sai ka ci wahala a hannuna, babu ruwanka da my pleasure"....... Sumbata Noor ya mannawa Leo a wuya yana faɗin. "This is my brother, love you more heartbeat". Gyarasa da kyau a bayansa Leo ya yi yana faɗin. "Love you too baby".... Ƙara rukunkume Leo tightly ya yi yana ɗan sakin shirin murmushi.
Shiru Zaysh bai sake yin magana ba, sai dai ya kama kunnen Noor ya murÉ—a da É—an karfi. Turo baki Noor ya yi ba tare da ya yi magana ba. Shi kuwa Vash hankali ya yi nisa, ya shiga damuwa sosai ta yadda har zufa yake haÉ—awa, saboda aljana ta ce zata kashe Manassa a daren yau, ga shi sun barosu a sansani, ya ALLAH.