← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 217 OF 227

Sashe 217

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da wannan tinani a ransa ya rage tsawonsa, ya gyara hannun rigansa kafin ya ɗauketa cak sai saman shoulder ɗinsa, ya juya suka cigaba da tafiya. Hannayenta tasa ta saƙalo wuyansa, bata san time da ta kwanta shiru a jikinsa ba, har barci ya fara ɗaukarta, bama ta san lokacin da suka isa sansani ba, sai ji ta yi ya kwantar da ita saman mattress ɗinsa kasancewat ta baya ya shigo dan kada kowa ya gansu, and ya yi tinanin ta yi barci shiyasa ya kwantar da ita wajen, bai tasheta bane kuma dan kada ya yi magana a waje sojojinsu su fahimci baya nan ya fita, dan wannan aiki na bincikar hukumar navy aikinsa ne shi kaɗai da yake yi wanda baya son kowa ya sani, shiyasa ya wuce cikin tantinsa da ita.

Da ya kwantar da ita sai ya suke rucksack ɗinta dake bayansa, ya tsaya kusa da mattress ɗin, murya can ƙasa ya fara kiranta da ke ta tashi ta tafi cikin tantinsu........ Da kyar ta yunkura ta miƙe zaune, ganin ta farka yasa ya koma gefe ya zauna a ƙasa game da fito da laptop ɗin nata, aiki zai dasa yi, babu alamar barci a tattare da shi.

Miƙewa ta yi, jikinta dik a mace ta nufi hanyar fita, har ta kai kofa muryansa ya katseta da cewa. "Zoki cire password na laptop ɗin"....... Nan fa ta ji kirjinta ya buga, dan kuwa ɗazun ta canza password na laptop ɗin daga sunanta ta mayar sunansa, tana zaune kawai bata san ya aka yi a lokacin ta tsinci kanta da sanya sunansa a password ɗinta ba.

Ƴan kame-kame ta fara yi, ta ɗan sosa kanta kafin ta juyo ta dawo, wannan shi ake cewa ɓoyyar soyayya, ɓoyayyar zuciya, hidden love ba.

A gefensa ta tsugunna, zuciyarta cike da tinanin yadda zata sanya wannan password É—in a gabansa. Cikin ikon ALLAH sai ya juyo mata da laptop É—in saitinta yadda ba zai ga me take yi ba, ai a bayyane ta sauke wani sanyayyar ajiyar zuciya har tasa ya É—an É—ago yai mata kallon second É—aya ya É—auke idanunsa.

Cikin girmamawa a hanzarce ta shigar da password ɗin game da juyo mashi da laptop ɗin. Bai ko ɗago ya kalli in da take ba ya fara ƙoƙarin buɗe bayanan da suka sanƙamo. Cike da shakkarsa game da tsoro da girmamawa ta ce. "Sir, zan iya taimaka maka?". Barci take ji kamar zata mutu, amma kunji wai zata tayasa aiki, kai soyayya wahala ce wani lokaci.

Shi kuma da ba'a mashi abin arziki da wani kansa tin na haihuwa irin na Lion ya É—aga mata hannu, ko kallon in da take bai yi ba mata alama da hannu a kan ta fice mashi daga É—aki...... Jikinta ya yi mugun sanyi na abin da ya yi mata, ta yi tinanin yanzu tin da suna aiki tare zai É—an rage share mutane da jiji da kai, Arya bata san cewa shi É—in jinin sarauta bane, a jininsa jiji da kai da izza take.

Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufi waje, tana fitowa suka ci karo da Zaynish dake ƙoƙarin shigowa. Baya ta ja game da kamewa ta sara mashi. Ko kallon in da take bai yi ba ya wuce ciki. A cikin ranta ta ce ita tsakanin Zaynish da Leo ɗin ma bata san wanene gwamma ba, halinsu sai su.

Wucewa tantinsu ta yi, a lokacin Jehan da Manassa sun yi barci, while Angelina ta shigo tantin yanzu, sun kammala aiki da Zaynish, sai farinciki Angelina take yi saboda Zaysh ya yabawa aikinta, ya ce ta yi namijin kokari.

Gyara shinfiÉ—arta ta yi ta kwanta tana kallon Arya da ta shigo yanzu, sai wani layi Arya take yi tamkar zata faÉ—i, jiki dik ya yi tsami. Sai da Arya ta duba Jehan, ta sumbaci yarinyar kafin ta kwanta a gefenta, ko sannu bata cewa Angelina ba. Ai tana kwanciya sai barci. Ita ma Angelina tana kwanciya sai barci.

A can gefe kuwa, Noor yana ankare da komai, ya ga fitar Leo kuma yaga dawowansu, dama saboda jiran dawowansa yasa bai yi barci ba, dan haka yana ganin Leo ya dawo ya miƙe ya nufi tantin nasa.

Baki É—auke da sallama ya shiga cikin tantin, zaune ya isko Zaysh da Leo suna tattaunawa kan wannan hayaki, Leo yana aiki da laptop na Arya.

A gefen Leo Noor ya zauna game da cewa. "Bro ina ka je?"....... Ba tare da Leo ya kallesa ba ya ce. "Idan na gama haÉ—a bayanai na tabbatar da abin da nike zargi zan faÉ—a maku in da na je, yanzu dai ya naku ayyukan?"....... "Komai na tafiya daidai". Suka haÉ—a baki wajen faÉ—e. Leo ya ce. "Zamu raba sojojinmu zuwa kaso huÉ—u, a cikin team 2 kowannenmu zai É—auki mataimaki guda É—aya, sannan 34 soldiers da suka rage zamu rabasu kaso huÉ—u".

Jinjina kai suka yi, a daidai lokacin Vash ma ya shigo cikin tantin, a kusa da su ya zauna, maimaita abin da Leo ya faÉ—a yanzu ya yi dan Vash ya ji, sannan ya cigaba da cewa. "A team two muna da UNAYS, JURAIZ, AMEER AND FAHAD". Ya É—an dakata yana dawo da kallonsa a kansu.

Sai ya ce. "Zan yi aiki tare da Unays, Zaynish kana tare da Juraiz shi ne mataimakinka, Arvash kana tare da Ameer, Nooriel kana tare da Fahad, gobe da safe In ALLAH ya kaimu zan sanar dasu hukuncin da na yanke, sojoji 34 da muke dasu kuma kowannenku zai É—auki sojoji 8 a karkashinsa, sojoji biyun da suke rage za'a barsu dan gadin sansaninmu".

Jinjina kai suka yi, Zaynish ya ce. "Wannan hukunci ya yi"...... Noor ya amsa da. "Sosaima, hakan ya yi". Kai Vash ya jinjina, kasancewar Leo yana son yin aikin sirri shi kaɗai sai ya ce. "You can go"...... Da okey suka amsa mashi, a tare suka mimmiƙe kowa ya yi cikin tantinsa.

Noor na shiga ya ɗauko blanket ɗin V daga cikin rucksack ɗinta, bai je in da take ba, ya shunfuɗa a ƙasa ya kwanta, ba zai kwanta da ita ba, ALLAH sarki, rashin sani yafi dare duhu, bai san bata da lafiya ba, ga barcin wahala ya ɗauketa, jikinta ya yi zafi raw tamkar wuta.

Yana kwanciya ba jimawa barci tai awon gaba da shi, sansanin nasu ya yi tsit, dik sun yi barci sai sojojin dake wajen wuta da kuma Leo. ASUBA TA GARI.

------------------------🧠🔥

IRON FIST. The blood of power, the blood of authority and honor, the blood of bravery and leadership!!.

Suna fira wajen CRYSTAL PALACE daddy Champion ya ɗauge saman motarsa, ya saukesa, wani irin niimantaccen iska ne ya fara ratsasu. Ai wani irin daɗi da ta ji bata san lokacin da ta ɗan rungumesa ba, ta manna mashi sumbata a cheek kafin ta sakesa ta miƙe tsaye, hannayenta ta buɗe tana shaƙar iska mai niima.

Ta É—an riko waist É—inta kafin ta ce. "Daddy i wish Rimsha tana tare da mu a wannan waje, I wish tare muke jin wannan daÉ—i, da na yi farinciki, ita ma tana son irin wannan yanayin".

Shi dai bai ce mata komai ba, sun zo sauƙa bridge ta hango irin turawa masu ice cream mai shegen daɗi a ƙananan motar nan, ai da sauri ta ce. "Daddy tsaya ka saya mana"...... Yana ƙoƙarin rage gudun motar ya ce. "In saya maki dai sarkin son zaƙi ba in saya mana ba".

Dawowa mazauninta ta yi, ta zauna tana sakin one side smiling kafin kuma ta É—an cukule fuska tana turo baki. Tsayawa ya yi, ya kira mai ice cream É—in. Wani dattijo ne a irin waÉ—an nan motoci da ake haÉ—awa É—in, ya zo da sauri, cikin girmamawa yana risinar da kai ya ce. "Wani irin za'a baka sir".

Carap ta capke kafin Aryan ya yi magana ta ce. "Milk and mango flavor"...... Da okey dattijon ya amsa game da fara kokarin É—auko roban zuba mata.

Dakatar da shi Aryan ya yi yana harararta kafin ya ce. "Give her chocolate or strawberry"....... Turo baki ta yi. "Daddy irin wannan ice cream ɗin milky ya fi daɗi"...... Banza yai mata bai sake magana ba, dattijon ya zuba mata a robar ya miƙo mata, kin karɓa ta yi, ta make kafaɗa tana turo baki har da juyawa Aryan baya wai ta yi fushi.

Hannu Aryan ya miƙa ya karɓa, sannan ya zaro kuɗi daga jikin kujerar motar, ya miƙawa mai ice cream ɗin dala 100. Dattijon ya ce. "Bani da canji".

Aryan ya É—aga mashi hannu alamar ya je kawai. Godiya ya dinga yi, Aryan ya tada motar da hannu É—aya suka fara tafiya. Juya mashi baya ta kara yi tana kallon hanya, taki yi mashi magana.

Oh manyan kasashen duniya sun cigaba, dare tamkar rana, ba rashin tsaro ba hayaniya, wlh ko'ina ka gani lantarki tankar kamar rana, abin gwanin ban sha'awa, ALLAH ka gyara mana kasarmu ta zama fiye da hakan! Ku ce Amin.

Ya É—an yi tafiya mai É—an nisa kafin ya tsai da motar a wani haÉ—aÉ—É—en waje da ake sai da flowers, kun san su Æ´an rose ne, akwai iya baiwa flower muhimmanci.

Wani haɗaɗɗen bunch of flowers ya saya tare da karɓa ya ajiye a gefensa. Ice cream dake ɗayan hannunsa ya kai saitin ɗan bakinsa, baya shan irinsu ice cream da kayan zaƙi, amma yau saboda ita zai sha........ Kaɗan ya ɗan lasa, sai ya ɗan tsuke fuska alamar batai mashi ba. Ɗan daurewa ya yi game da sake ɗeba mai ɗan yawa a bakinsa.

Bai gaÉ—iye ba ya rike a bakin nasa, ya kai hannu ya jawota jikinsa, tana tirjewa aikuwa ya matse É—an bakinta game da sunkuyowa kanta, ya tura mata ice cream É—in dake bakin nasa cikin nata.

Ji kake diff ta natsu ta daina ƙoƙarin kwace kanta, ta kwanta a jikinsa tana turo baki, sai kuma ta hau haɗiye ice cream, harda ɗan lashe baki. Zuba mata ido ya ɗan yi kafin ya ce. "Sarkin kwaɗayi, me na lashe baki kuma bayan kin ce ba zaki sha wannan ba?".
Chapter 217 · 0% Book details