Sashe 17
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wasu ma irinsu Leo, Zaynash, da Unays sun yi gaggawar riga kowa miƙewa domin cigaba da karɓar horon. Matasan sojoji da dama sun ji ciwo a hannun da gaban goshi, amma Captain bai nuna kamar ya gani ba dik da ya ganin, ya umarcesu kawai da su tashi su koma cikin motocin da aka kawosu bari su koma.
Da kyar wasu suka iya tashi, amma ko kaÉ—an babu alamar tausayinsu a idanun manyansu, kamar ma basu san suna yi ba! Kuma da dik wani motsinsu a idanun Generals na sojojin ne.
Sun yi matuƙar mamakin ganin yadda aka ɗaukesu zuwa wajen wani bene mai bala'in tsawon da ya fi na jiya, ya fi dik benayen dake GIDAN SOJA tsawo sosai. Kallon-kallo suka fara yi a tsakaninsu kafin su mai da kallonsu a kan Captain dake tsaye ya rungume hannaye a kirji. Ganin suna kallonsa yasa ya yi masu nuni da benen a kan su haura. Dole suka fara haurawa da gudun gaske, dan ba wasa ake yi a nan ba, dik jigatar da suka yi ɗazun basu bi ta kansa ba.
A nan ana koya musu yadda za su shawo kan tsoro ne. Dole su hau kan bene mai tsayi su tsaya ba tare da motsi ba, sannan su tsallaka wani igiya daga gefe zuwa gefe, ma'ana daga wannan bene zuwa wani bene.
Wanda ya nuna tsoro, sai a barshi a can sama har sai ya cire tsoron gabaɗaya. Dayawa daga cikinsu jikinsu ya yi kermar tsoro, amma dole suka jajirce, dayawa daga cikinsu daga kan wannan horo zuƙatansu ta fara bushewa, take suka daina jin tsoron mutuwa, ace ka hau bene can sama, sannan ka bi ta kan igiya ka tsallaka daga wannan bene zuwa wani? Ai dole zuƙata su fara bushewa daga tausayi da tsoro!.
-------------------------🔥
Bayan dik wahalar da suka sha, sai aka koya musu rikon ƙananan bindigogi wanda aka karantar da su jiya, su za'a sanyasu rikewa da yadda ake sauya harsasai cikin minti biyu kacal. Idan mutum ya kasa cika wannan lokaci, sai a hukunta shi da ƙarin horo hawa bene ko rarrafawa cikin ƙasa or taɓo. Wanda ya fi kwarewa, shi ake ba damar jagorantar abokan horonsa, hakan yasa suka zage dantse.
Captain ya kura masu ido sosai yana kallon motsin kowa, tin daga kan yadda ya ga Leo yake canza bullet na bindigarsa ya gane ba yau guy ɗin nan ya fara rike bindiga ba, lallai dole yasanta sosai, saboda a ƙasa da minti ɗaya ya canza bullet ɗinsa, ba Captain kawai ba, harta manyan jami'an dake kula da dik motsin matasan sojojin sun razana da ganin abin da Leo ya yi, har ya sanya masu shakku a kansa, suka fara jin anya kuwa ba wata a ƙasa kuwa? Dan shi ba ɗan kasansu bane, saboda GIDAN SOJAN AVARIS da ya fita daban a duniya ne yasa ya ce zai yi appley a nan, zai zo ya karɓi horonsu da kyau, a gida ma sun ki, amma ya kafe shi fa lallai sai ya zo, da suka ga ya kafe kawai suka sake mashi.
In takaice maku labari haka ranansu ta biyu ma ta kasance a GIDAN SOJ, suka karɓi horo kamar jiya. Bayan horo, kamar jiya sai karfe 8:30 bayan sallar isha'i suka koma ɗakunansu. Suna shiga suka yi wanka suka hau shirin kwanciya.
Sai dai da suka shigo basu ga Noor ba, kuma basu tambayi ina yake ba. Suka hau shirin kwanciyarsu, suna cikin shiri ne ya shigo É—akin tare da rakiyar wasu sojoji guda biyu, ya ji ciwo ne a kafa sosai a dajin da aka kaisu aka É—aure masu ido, ya taka wani karfe ta fasa mashi kafa, ciwo ne da ba za'a iya kyalesa ba, dole suka É—aukesa zuwa military hospital É—insu aka wanke kafar aka gyara mashi kada wata cuta ta shiga.
Sojojin suna rakosa suka juya suka fita, shi kuma ya kariso ciki, da sauri Vash and Zaysh suka yi kansa, rirrikesa suka yi suna tambayansa me yake faruwa. Idanunsa a kumbure saboda uban kukan da ya ci, kyawawan pink lips É—insa irin na mata sun ciza sosai, saboda ya yi ta ciccizasu a lokacin da yake jin azaba, har gefen lips É—in nasa ta fashe saboda damketa da hakori da yake yi.
Kama shi suka yi zuwa saman bed, suka kwantar da shi tare da cigaba da tambayansa me yake faruwa. Idanunsa ya rufe kafin ya kwashi dik irin azaban da ya sha ya faÉ—a masu. Gudun farko kawai ya maimaita sau biyar, rarrafawa cikin kasar laka ya yi sau uku, a wannan daji sai da ya ya dinga sakewa har sai shidda, a nan ne ya taka wani karfe mai kaifin gaske ta fasa mashi kafa ta jefe wajen idon sahu ba ta wajen takalma ba.
Tin da ya fara basu labari suka yi mugun tausaya mashi, sai sorry suke ce mashi. A tare suka haɗa kai, suka shirya mashi ruwan wanka, sannan suka tallafa mashi ya shiga toilet dan yin wanka. Dik abin da suke yi Leo yana zaune yana nazarin makaman da aka kara koya masu yau, na jiya ne aka sake maimaita masu da kyau dan ya shiga kansu yadda yakamata. Bai ko ɗago ido ya kallesu ba, dan shi ba abota ya zo yi GIDAN SOJA ba! Horo ya zo karɓa.
Bayan Noor ya kammala wanka da shirinsa tsab, kowannensu ya haye saman bed É—insa, sannan suka fito da wayoyinsu kamar jita. Noor ne ya fara kunna wayansa, dan kafin a basu wayoyin sai da aka shar'anta masu cewa da daddare ne kawai aka lamunce masu su kunna waya, dan haka in zasu kwanta suka kashe wayar basa sake kunnanta sai sun dawo É—akin bayan horo.
Shi dai Zaynash yaki fito da wayansa, dan yana jin kunyarsu, dikkansu wayoyinsu manya-manya na Æ´aÆ´an manya, nasa ce kawai matacciya, sai yake jin kunyar fitarwa.
Noor yana kunna wayar ya kunna data, nan sakonni suka hau shigowa kamar ruwa, dik kuma na ƴan uwansa mata ne dake ta turo mashi saƙon kukan sun yi kewansa.
Bai bi ta kan kowannen saƙo ba, kai tsaye ya shiga kan number da aka sanya my dad. Video call ya dannawa wannan number yana ɗan gyara kwanciyarsa da kyau, sai ciza laɓɓa yake saboda zafin da jikinsa take yi mashi.
Bugu É—aya aka É—auka, dik da É—akinsu da haske amma fuskan Noor bata fita sosai a call É—in ba, hakan yasa ya kunna hasken wayar ta gaba. Yana sauke idanunsa a kan wani kyakkyawan mutum mai É—an matsakaicin jiki, suna kama sosai, fari tas da shi, ga idanu dara-dara farare tas, da alama mutumin ma a kwance yake, kyakkyawan gaske sosai.
Harara ya dallawa mutumin kafin ya ce. "My dad baka yi barci ba?"....... Wani irin cool smiling ya saki kafin ya amsa da. "I'm waiting for your call, how can I sleep?".......... Sake hararansa Noor ya yi. "Daddy gidan Soja akwai wahala, ba zan iya jura ba, ka zo ka É—aukeni". Ya kai karshen maganar cikin raunin murya. "Pleasure very soon zaka saba".... Zai yi magana daddy yai sauri sake cewa. "No, kawai ka faÉ—a mun success da ka samu a yau?".
Yana turo baki ya amsa da. "Alot my hero". Wani irin ƙayataccen murmushi dad ya saki kafin ya ce..... "Thats is my son, I know you will succeed, try to bring us a good result"..... "I will try my best dad, where's my Auntys?"....... "They're not here, they're in their room, but Lisa bata nan"....... Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Dad here is my friends da na haɗu da su a nan, they help me and they're so king and perfect". Ya faɗa tare da juyar da wayansa ya nunawa daddy bed ɗin su Zaynash dake kwance shiru.
"Zaynash this is my dad, ku gaisa". Ya faɗa yana sauƙiwa kasan bed ɗin intently, ya zo ya miƙawa Zaysh wayar. Karɓa ya yi, a mutunce suka gaisa, daga nan ya karɓa ya miƙawa Vash ma suka gaisa. Dik da basu magana da Nirash sai ya ji yana son kai mashi wayar su gaisa da daddynsa, wata zuciya ta ce a'a kada ya je, wani kuma ya ce ya je Nirash zai amsa. Daurewa yai tare da nufar bed ɗin Leo.
Sallama ya yi mashi tamkar wanda zai shiga wani ɗakin saɓanin yadda ya je wajensu Vash ba sallama. Ai cikin zafa su Vash suka ɗago kai suna kallonsa, suna jiran su ga Leo zai karɓi wayar ne ko kuwa.
A gaban bed É—in ya tsaya tare da cewa. "Here is my dad, ku gaisa"...... Leo yana kwance shiru, ya kifa littafin tasa a fuska kamar yana barci, kuma idanunsa biyu, amma babu alamar zai amsa Noor. Shiru ya tsaya zuciyansa sam babu daÉ—i na abin da Leo yake yi masu, amma ya zasu yi? Dole sai hakuri. Ko sunan Leo É—in fa basu sani ba, kuma wai suna É—aki guda.
Jin shiru yasa dad ya ce. "Are you okay pleasure?". Da sauri ya amsa da. "Yes dad". Ya faÉ—a yana juyawa ya bar wajen.
"Is there any problem?". Dad ya tambaya, da sauri ya girgiza kai alamar a'a, sai ya haye bed ɗinsa ya kwanta zuciya babu daɗi. Haka suka cigaba da hira da daddyn nasa har barci ya ɗauke su Zaynash, sun shafe 2 hours suna hira, da alamar shakuwa da kaunar juna matuƙa a tsakaninsu. Sai can suka yi sallama, ya katse kiran tare da kashe wayar bakiɗaya, daga nan ya hau barci shi ma. Ɗakin ta yi tsit alamar dik sun yi barci harta Leo ɗin ma.
--------------------------🔥
NEW YORK.
CRYSTAL PALACE.
Ayi hakuri da zaman da zan yi wajen bayanin inane CRYSTAL PALACE, zan yi hakan ce dan ba zan sake bayani a kanta ba, kuma zan yi hakance dan na tabbata ba kowa yasan irin ginin da nike nufi ba har sai na yi bayani, bugu da kari CRYSTAL PALACE tana da alaƙa da kusan kowa dake a cikin wannan littafi, dik wata rikici daga cikinta yake fitowa, shiyasa dole zan daure in sha wahalar typing dan fayyace maku tsarinta dallah-dallah!.