← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 227

Sashe 180

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rungumota Ammie ta yi, ta hau rarrashinta tana bata baki, sai dai ina Rimsha taki yin shiru, in short sai da ta É—auki kwanaki uku tana wannan kuka na ta shiga uku, dik Abba bai san tana yi ba, a rana ta huÉ—u ne ta kama Monday, a wannan ranar da asuba Faryan ya ce ta shirya ya kaita school.

Jin cewa aurenta ba zai hanata school bane yasa ta É—an saki jiki, burinta dik ta je makaranta su haÉ—u da Seraphina ta faÉ—a mata abin da aka yi mata, dik tayi sanyi baiwar ALLAH, daga umm sai uhm-uhm ta zama, bata hira, ta takura kanta sosai, amma yau da zata je school har da É—an murmushinta.

Ta shirya tsab cikin uniform ɗinta, har ta rame uniform ɗin yai mata yawa. Faryan na tsaye a parlo ta fito rike da rucksack ɗinta, karɓa mata ya yi yana faɗin. "Mu je in kaiki da wuri, Abba na jirana zamu je mu ɗauki amaryar Yah Harleen".

Kallonsa ta yi, muryarta a dashe sosai ta ce. "ALLAH yasa tana da kirki"....... Da amin ya amsa game da riko hannunta, suka nufi waje yana kara yi mata nasiha, yana tausan zuciyarta, yana faÉ—a mata kalamai masu daÉ—i, yana tunatar da ita ALLAH ya ce Annabi ya ce, a haka suka nufi school ni kuma na nufi DOL kafin mu dawo mu bisu school É—in.

--------------------🔥

D-O-L

Nutso take yi a cikin ruwan cike da farinciki, yana tsoma gashin kanta can kasan ruwa tana ɗagosa ruwan dake biyo gashin ya ƙara wanke mata fuska, hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba. Shi kuwa tamkar gunkin da aka sassaƙa haka yake tsaye a cikin ruwan ware kitson kansa dan ya wanke golden hair ɗinsa.

Tsoma kanta ta yi cikin ruwan tana É—an juyawa, É—agowa da zata yi tana faman yin sama da kanta sai ji ta yi...........

Likes comments and share fisabilillah.

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

For more information 08161390581 Whatsapp me only.

STEP 1🔥

2025-12-22.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Dedicated to all Aryan and Zayra'an fans.🫀♥️

E_____________ 59 & 60

DEATH OR LIFE. (DOL)

Waɗan nan wasu magunguna ne da ake yi wa yara da sunan rigakafi, amma batu na gaskiya magunguna ne dake kashe garguwar jikin yara, tin yaro yana ƙarami zasu kashe mashi garkuwar jiki, hakan zai sanya jikinsa zata yi saurin karɓar kowacce irin cuta ce ta shigo, sannan jikinsa za yi wahalar karɓar magani.

Kuga yaro yana ciwo ayi ta magani amma dik na banza, sai kuga kamar ba'a mashi komai, kuma ko sun girma jikinsu ba zai dinga karɓar magani ba, already an kashe masu garkuwar jiki tin suna yara, ba wanda zai zaci cewa maganin matsala ce, za'a ce rigakafi ne kawai, hmmmm bayan rigakafi babban cutarce a wajen.

Al'ummar ƙasar Avaris sun gagara gane wani abu ɗaya, babu ta yadda za'ayi gwamnatinsu ta basu abu kyauta, kuma ta dinga binsu har gidaje da sunan yi masu, idan gaskiya ne a bisu gidaje ana raba masu kayan abinci da jari da ake cewa ana fitar masu mana, meyasa idan sun fitar da tallafin gwamnati sai dai su ce ka je ka cika form, ka bi layi, ka yi kaza, ka yi kaza?.

Amma shi rigakafi za'a bisu har gida ne ana masu, har da rabawa yara sweet ko wani abin makamancin haka idan sun yi, kai mutanen cikin Avaris wani lokaci tamkar an toshe ƙwaƙwalwalensu, abin takaici sun kasa ganewa, wlh tallahi gwamnatinku ba zata taɓa binku in da kuke ta baku abin arziki ba, sai in cuta, cuta ce wannan za'a biku ko'ina a lallaɓaku, har kuɗi zasu raba maku dan ku yarda da su, da yake cutarku za'ayi, wlh dik wanda ya ci abin gwamnatin kyauta yasan akwai abin da zaka biya da shi, waɗan nan mutane nasa bada abu haka kawai, sai da babban dalili! Ku rubuta wannan ku ajiye.

Ya rabb, ya ALLAH, ALLAH ka karkato da hankalin jama'ar annabi, ka ganar dasu! Musamman iyaye mata, sune ke bari anaiwa yara wannan gayyar tsiya, basu san cutar da rayuwar yaransu suke yi ba, da anyiwa yaro sau ɗaya shikenan an gama da garkuwar jikinsa, ya ALLAH ko shekara ɗari zai yi a duniya jikinsa ba zata dinga karɓar magani ba, sai dai ya samu sauki daga ALLAH, amma in bai da lafiya kun dinga kashe kuɗi a banza.

Zubawa maganin idanu Leo ya yi, sai da ya karance rubutun jiki kaf, sun ɓoye ainahin manufar maganin da rubuce-rubuce na karya. Nisawa ya ɗan yi tare da zarar magani guda ya zura a cikin aljihunsa, ya sanya su Zaysh suka mayar da sauran a cikin kwali, da alama bincike zai yi a kan wanda ya ɗauka.

Wucewa container gaba suka yi, a nan ma shi ya buÉ—e container. Ya rabb, Tramadol mai karfi sosai ne a cikin wannan container, waÉ—an da basu san me Tramadol ba, wani maganani ne da ake shigo da shi daga India, China, Pakistan, ana sayarwa da sunan maganin cuta, amma batu na gaskiya wannan magani yana haddasa lalacewar kwakwalwa, in kasha sosai yana sanya hauka, tashin hankali, mantuwa, ga sa jaraba sosai.

Leo sai da ya É—an girgiza ganin waÉ—an nan uban tulin kwalin Tramadol É—in nan, katon container irin wannan cike da manyan kwalinsa, ya rabb. Umarni ya baiwa su Noor da su mayar su rufe, sannan ya wuce gaba. A nan ma da kansa ya buÉ—e container.

Ya rabb Codeine Syrup ne a cike a ciki. Codeine a idanun al'umma ana kiransa da maganin tari, amma ana sha ne dan maye, kuma mugun illatar da lafiya yake yi. Yana lalata hanta, hassasa matsalar numfashi, mutuwa idan an sha fiye da misali, manyan ƙasashe da dama sun haramta shigo da shi ƙasashensu, amma Avaris ta zama kwandon sharar ƙasashen dake son cin karensu babu babbaka, komai shigo masu da shi ake yi, saboda ƴan ƙasar har yanzu a kwance suke, sun ki tashi su farka su fahimci dik wannan abin su tsabtace kasarsu daga gurɓatattu!.

Kai kawai Leo ya jinjina game da cewa su rufe su shiga wata container. Haka kuwa aka yi, suka mayar suka rufe, suka wuce container na gaba.

A wannan container na gaban cike yake da fake drugs, copyn magungunar gaske kenan, sunayensu da komai tamkar na gaske, sai dai ko kaɗan babu sinadarin magani a ciki, sai dai sinadarin guba mai cutarwa ne a ciki. Waɗan nan magunguna suna sanya ciwon koda, ciwon hanta, mutuwa a hankali, ka je sayen magani dan ka samu lafiya, sai a ƙara maka wata cuta, ya ALLAH kana ganin al'ummar annabi yadda ake yi mana, ya ALLAH ba zamu iya ba, sun fi karfinmu, amma basu fi karfinƙa ka ba, ya ALLAH ka kawo mana ɗauki.

Wucewa container gaba Leo ya yi. Wannan container shi kuma cike yake tab da manpower, king power, double action da makamantansu, ina maza masu shan man power? To albashirinku! Kuma ga naku ta iso! Dan balai ba zaka zauna yadda ALLAH ya ajiyeka ba, to ai zaka shawa kanka balai. To waɗan nan magunguna da ake shigo dasu da sunan man power ba ma a gwada su a asibiti ba, suna ɗauke da sinadarin da ke sa bugun zuciya su jawo bugun zuciya da sauri, mutuwar mazaje da yawa a sirrance ba tare da an san ainahin me ya kashesu ba, namiji zai mutu ba tare da yasan me ya kashesa ba, waɗan nan magunguna suna buɗe jijiyoyon namiji ne, ba karfi suke ƙara maka yadda kake tinani ba, buɗe jijiyoyinka suke yi, su bar iska ya shiga jikinka na wuce misali, su haifar maka da mutuwar gaba idan ka cigaba da sha, wlh suna sanya ciwon zuciya, saboda ita zuciyarka ba zata iya karɓar yadda jikinka zai buɗe lokaci guda ba, iskar dake shiga tana hura zuciyar take ta kumbura, idan namiji ya sha shi mai yawa a lokacin ma a take yake mutuwa. Sai ka ji masu sayarwa suna cewa baida side effects, sannu na ce, na ce sannu dan uban mutum!! Kai ni fa raina ɓaci yake in na ga ana cutar da bayin ALLAH, ina jin tamkar in zama namji irin sayyidina Ali!.

Wannan magana ta maganin karfin maza ta tina mun da wani da ya mutu a hotel bayan shan man power, ya ALLAH, maza su yi ta mutuwa a rasa me yake kashesu, jahilan cikin al'umma su yi ta tallar man power ba tare da sanin ainahin dame ake yinsa ba, suna kashe al'umma cikin rashin sani da sunan wai su suna neman kuÉ—i. To hajiya Jummai, fatan idan kin gama karantawa in ma mijinki yana sha zaki taka mashi birki! Idan kinga wani naki zai sha ki taka mashi birki! Dan zallar cuta ce a ciki! Dan haka ki yi gaggawar takawa mijinki birki, ki tattara sauran power da kuke da shi ki kunshe mashi kayansa a wando!
Chapter 180 · 0% Book details