← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 227

Sashe 147

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A saman chair ɗinsa ya koma ya zauna, ya ɗauki table phone, sister Lazy ya kira, bugu ɗaya ta ɗaga, cike da bada umarni da izza ya ce ta je sashen drugs ta ɗauko mashi naproxen yanzu ta kawo mashi. Ba tare da ya jira amsarta ba ya katse kiran. Tamkar zata fashe, tana wani irin huci ta miƙe, badan bata da tabbacin ba zai zuba maganin ba idan ta kawo da wlh wani maganin daban zata kawo, dan dai tasan zai duba ne, in kuma ya ga ba wanda ya ce ba to da matsala ta sani, ga shi bai iya hukunci ba, sai yasa ka gwammaci mutuwa a kan rayuwa!.

A fusace ta miƙe ta nufi wajen tana huci, shi kuma ya jawo laptop ɗinsa ya fara duba ayyukan da suka yi jiya, wanda yakamata ya sanya hannu ya fara sanyawa, wanda yakamata yai cancel ya yi.

A can ɓangaren kuwa, Sister Maya ce tsaye gaban table na Dr Kamal tana miƙa mashi cup da ta haɗa mashi tea, karɓa ya yi, ta ɗan risina alamar girmamawa, sannan ta juya zata tafi, hannunta ya riko da sauri, cikin sanyin murya ya ce. "Ina zaki je?".

Ras ta ji gabanta ya faɗi, ɗan zazzare eyesball ɗinta a kansa ta fara yi kafin ta ce. "Zan je wajen babies ɗinmu ne, lokacin yi masu wanka yana ta ƙurewa, ga shi ba'a basu madara ba". Tana ɗan sunkuyar da kai ta faɗa. Cikin wani irin karuwan salo ya ɗan jawota ta faɗa jikinsa, ya zaunar da ita a saman laps ɗinsa, ai gabaɗaya ɗan ɗauke wuta ya yi, ita kam sai ji ta yi tamkar bata duniya, ta zaci mafarki take yi.

Haɓarta ya ɗago suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ya ce. "Kina ganin ba kamata ya yi ace yanzu naki babys ɗin kike kula da su ba? Ko ke baki son yaran kanki ne?"........ Ai muryanta na rawa, da sauri ta ce. "Ina son babys sosai, ina son nawa ma, kuma ina son waɗan can ma sosai".

Ɗan rankwafowa kanta kaɗan ya yi, tamkar mai raɗa ya ce. "Kin shirya karɓar baby in baki? Zaki haifa mun yara kyawawa irinki?"........ Da sauri ta shiga gyaɗa mashi kai alamar e. Sumbatar cheek ɗinta ya yi kafin ya ce. "Na jima ina fatan naga kin haifa mun magada, ga shi yanzu lokaci ya iso"....…. Shiru ta yi, ta gagara yin magana.

Hannunsa ya É—aura a saman cikinta, yana É—an shafawa ya ce. "Wannan É—an karamin cikin anya zai É—auki twins kuwa?"...... Watau shi Dr Kamal yadda kuka ga Maya haka yake, akwai jarabar son yaran kansa fa amma, kuma shi a tsarinsa idan ya tashi dasa mata cikin zai yi, dashe zai yi mata, dan twins, triplets and quadruplets yake so, baya son É—aya, shiyasa zai dasa mata.

Me kuke tinanin zai faru idan yasan Maya ba zata taɓa haihuwa ba? Dan shi bai san Dr James ya cire har da mahaifarta ba, ya saka burin haifar yara kyawawa kamarta da ita. Watau akwai wani gagarumin yaki a hospital ɗin nan dik ranar da Dr Kamal ya gano bata da mahaifa, shikenan ba zai samu magada ba, har na hango kalar guguwar da zata tashi!.

Ɓoye fuska ta fara yi a jikinsa, ta sunkuya tana ɗan murmushi, irin maganar tai mata nauyi. Haɓatar ya ɗago da hannu ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma yana shafa bayanta izuwa kan mazaunanta, ya ɗan kwanto da gefen fuskansa a kan hair ɗinta. Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin daga bisani ya ce. "Jeki kula da babys ɗinki, anjuma in mun tashi aiki ki zo mu tattauna".

Ai da sauri ta miƙe tamkar wacce ke kan ƙaya, dan dama ya sakata wani hali, bata taɓa zatan zata jita a jikinsa ba. Waje ta nufa tana ɗan kame jikinta, binta da kallo ya yi yana jin wani irin sonta na ƙara ratsa shi. Dab zata fita ta ɗan waigo dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa ido, kashe mata ido ɗaya yi, hakan yasa ta juya, da sauri ta fice tana murmushi, dimple ɗinta irin na Leo yana lotsawa gwanin burgewa.

Tana zuwa ta isko wasu babys biyu suna kuka, an masu wanka an shiryasu tsab. Ɗaukansu dikka biyu ta yi, ta ɗaura ɗaya a shoulder ɗinta, ɗaya a cinyarta, ta fara jijjiga babys ɗin, da kyar wanda yake kan cinyarta yai barci, a hankali ta kwantar da wanda yake hannunta yana ɗan kuka, ta miƙe ta mai da wanda yake saman laps ɗinta saman gadonsa, ta dawo ta ɗauki ɗayan, tana jijigasa tana zarya a cikin ɗakin, sai take jin tamkar darling ɗinta ne, da yake kunga shi ne rigimammen yaro, so wannan mai kuka na yau ta ji kamar an dawo da darling ne.

A can kuwa, sister Lazy ta kawo drugs ɗin, har ƙasa ta tsugunna ta miƙo mashi, karɓa ya yi tare fitarwa ya duba. Ganin wanda ya buƙata ne ya ce mata. "You can go". Ya faɗa yana miƙewa, ya nufi gaban sofar da Zinta take bayan ya ɗauko mata robar ruwa daga freezer ɗinsa.

Tamkar sister Lazy zata haɗiyi zuciya ta mutu tsabar taƙaici, tana gani sai faman cewa Zinta sorry yake yi, yanzu ya kara sakar mata zuciyansa, tin da ya yi wasa da jikinta, ya ji ɗuminta, ya ji sa a duniyar Jupiter, daga nan ya sake narke mata.

Da kansa ya ɓalle drugs ɗin, sannan ya ɗagota ya zaunar, ya sanya mata drugs ɗin a baki, ya ɓalle bakin robar ruwan, ya bata. Tana ɗan shagwaɓe fuska ta karɓa, sai ce mata sorry yake yi. Bayan ta sha ya rufe ruwan, sai ya ce ta kwanta ta yi barci sai zuwa yamma, yau ba zata yi aikin komai ba. Sai da ya tabbatar ya kwantar da ita, sannan ya miƙe zai koma chair ɗinsa kenan sanyayyar muryarta ta katse shi da cewa.

"My oga, please our darling, jiya har mafarkinsa na yi, na yi mafarkin yana ta kuka yana son shan madara, please ka kaini wajensa ka ji?". Idanunta na ciccikowa da kwallah ta faÉ—a. Bata san darling yana can cikin mawuyacin hali ba, yana faÉ—a tsakanin rayuwa ko mutuwa, ALLAH ne kaÉ—ai yasan kalar azaban da bawan ALLAHN nan yake ciki, cutar ta huda jikinsa sosai, wani lokaci har bleeding hancinsa yake yi, sun sanya shi cikin wani glass transparent haka, wanda suna iya ganinsa, ta nan suke bashi madara, dik wannan rikici nasa da kukan ya daina, ko motsin kirki baya yi, a iya kwana É—aya kawai fa kenan.

Ya ALLAH me kuke tinani zai faru bayan kwanaki 5! Ya kuke tinanin wannan cuta zata yi wa al'ummar duniya? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun........ Ayi hakuri da abin da zan rubuta daga yanzu har gaba, ta yiwu yai maku daɗi ko akasin haka, amma dole zan rubuta! Dan labari ne kan halin da duniya take ciki! Burina in wayarwa da mutane kai, in farkar da kowa yasan halin da ake ciki, dan haka ku yi hakuri da abin da zaku ji kuma zaku ga na rubuta, nasan akwai tashin hankali da jefa zuƙata cikin damuwa har ma da kuka, saboda waɗan nan jarirai, jaririn da bai san komai ba, dole nasan hankula zasu tashi, amma ba yadda zan yi ne! Dole ku san me ake ciki, ku daure ku cigaba da karatu, zaku ci ribar karatun ko ba'a kanku ba, ko a kan ƴan uwa, kunga yanzu idan kun ji za'a cirewa wata mahaifa ai ko shawara ce zaku bata, idan yazamana dole za'a cire mata sai ku ce mata in an cire ta ɗauke kayanta ta koma da shi gida ta je ta binne. Wlh tashin hankalin dake cikin wannan duniya ta zarce bakin ɗan adam ya zayyano shi, wani fitinan idan kuka ji sai ku zaci ba gaskiya bane! Amma wlh abin da ya fi ɓarnar da su 3D suke yi yana iya faruwa a duniyar yau, fatanmu dai ALLAH ya karemu daga dikkan azzaluman nan, ya kawo mana karshen zalunci, ya bamu kwanciyar hankali da zaman lafiya, daga karshe ya bamu dacewa da lahira game da cikawa ta hanyar shahada.

Jikin mace gabaɗaya kadara ce, mu mata muna ganin rayuwa a yanzu, tin da aka gano jikinmu kadarori ne shikenan, kowacce ta dage da addu'a, babu abin da ya fi karfin ALLAH, idan kika riki ALLAH dole a ganki a barki....... Magana ta karshe kuma shi ne ƙasar AVARIS ƙasa ce ta kirkira, babu ƙasar a zahiri, na kirkiri ƙasar ce saboda bana son in ɗaurawa wata ƙasa wani abin da ba shi ba, kunga yanzu ƙasa ta ce Avaris, dik ɓarnar da na ɗaura mata babu wani shugaban da ya isa ya fito ya ce na ɗaurawa ƙasarsa wani abin, sannan a bisa dokar ƙasa kuskure ne ka ɗaurawa wata ƙasa irin wannan abin kai tsaye, shiyasa na kirkiri tawa ƙasar, dan haka Avaris ƙasar kirkirace! Fatan kun gane kun kuma ɗauki haske?.

"My oga, please our darling, jiya har mafarkinsa na yi, na yi mafarkin yana ta kuka yana son shan madara, please ka kaini wajensa ka ji?"..... Jinjina mata kai ya É—an yi. "Ki yi barci zuwa dare zan kaiki". Ba tare da ya jira amsarta ba ya wuce ya koma wajen chair É—insa, lumshe idanunta ta yi, tana jin ciwon cikin na raguwa, har barci yai awon gaba da ita. Ita kuwa sister Maya tana can tana fama da jijjiga wani baby da yaki yin shiru, amma zuciyarta na can wajen tinanin Dr Kamal da abin da yai mata É—azun, yadda ya jawota jikinsa, ya ALLAH, abin ya tsaya mata a zuciya, sai take jin tamkar ta sake komawa wajensa, dan bata gaji da kallonsa ba.

Wasa-wasa sonsa na shiga zuciyarta, watau 3D tantirai ne, sun iya sanyawa mutum soyayyarsu a rai cikin ƙanƙanin lokacin. A haka suka wuni yau, sister Maya ta yi ta fama da babys ɗin, hankalinta ya rabu kashi uku, tana fama da babys, tana tinanin Dr Kamal, tana kuma tinanin sister Zinta dake fama da ciwon ciki, bata san a wani hali take ciki ba, ta damu sosai tana son sani, ga shi ba damar ta je 3D side idan ba su suka nemeta ba.
Chapter 147 · 0% Book details