Sashe 43
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Good evening sir". Cikin shagwaɓa mai narka zuciya ta faɗa. Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da. "Evening how's your day?".......... "Cool". Ta amsa kafin ta sake cewa. "Na manta wayata a hannunka". ...... Jinjina kai ya yi tamkar yana a gabanta, amma bai yi magana ba.
"Zaka kawo mun wayar gobe please? Ko in zo in karɓa?"........ Shiru ya ɗan yi, can kuma ya ce. "Gobe zan bar barrack ɗin nan saboda hutunmu, faɗa mun in da kike yanzu in kawo maki".
Shiru ta É—an yi, bata son yasan ita Æ´ar GAT ne, dan in ya sani ba zai sake kulata ba, É—an damar da ta samu na magana da shi zai gudu, ga shi tana son ganinsa yanzu, so take ta shirya mashi wata dabara, in kuwa haka ne yazama dole ta fito su haÉ—e a waje ba a gida ba, to ya zata yi da sojojin dake gidansu har ta samu hanyar fita? Ta tambayi kanta a lokacin da yake katse mata tinani da cewa. "Baki tare dani ne?".
Da sauri ta amsa da. "Ina jinka, nima gobe zan bar barrack ɗin nan, dan haka mu haɗu a wajen itatuwan zone one in karɓi wayar". Ta faɗa kirjinta na dukan uku-uku. Shi kuma bai kawo komai a ransa ba, sai ya ɗauka kenan ita da iyayenta suka zo wannan bikin passing out ɗin, gobe za su koma kenan, like wow, ya faɗa a ransa, bai san wannan kam uhm na dai yi shiru, amma akwai case a wannan alaƙa tasu, shin GAT zai yarda? Ita da take shalelensa ƴar autarsa ma kuna ji tsoron ya sani take yi, tana ma tsoron a san ita ƴar GAT ne kada alaƙar ta ruguje, kun kuwa san da matsala sosai.
"Give me 30 mins zan zo wajen". Ya faɗa a sanyaye yana miƙewa tsaye. Da okey ta amsa tare da miƙewa ita ma, ta sauƙo ƙasan bed ɗin, da gudu ta faɗa toilet dan yin wanka, su Arya suna can ƙasa suna faman zazzagawa masu aiki faɗa wai dan meyasa zasu yi girki dayawa a gidan, basu san cewa baki zasu yi ba, daddynsu ya ce ayi girki dayawa dan yaki yarda daddy Noor ya sauƙa a hotel, ya ce lallai ya sauƙa a gidansa, ya hakikance.......... Ni kam na ce ko dan Aunty Lisa da ka sakawa ido ma ai dole ka hakikance su zo gidanka ɗan....... Bari dai na yi shiru tin da daddynmu ne, kun san ni ina bayan Arya!.
A gurguje ta yi wanka, za'a haɗu da masoyi, haɗaɗun wani European wears ta sanya, wandon jeans crazy, sai kuma top mai kauri, wankan milk and maroon ta yi, ta kuwa yi kyau matuƙa, ta sanya flat shoe saboda ta ji daɗin satar hanya, ta feshe jikinta da daɗaɗan perfume na kamfanin su Noor kafin ta gyara gashin kanta, sai faman kyalli yake yi. Ta tsaya a gaban mirror tana kallon kanta kenan ta ji wayar Angelina na ƙara alamar shigowar kira. Da sauri ta nufi wajen bed ɗinta. New number ta gani, kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka.
Sanyayyan voice ɗinsa ne ya karaɗe dodan kunnenta wajen cewa. "Hello". Wani irin daɗi ta ji na ya kirata da numbersa, ko ba komai yanzu ta samu numbersa, yana son faɗa mata yana wajen yana jiranta ta zo ta karɓi wayar, amma baya son kira da wayarta dan bashi da tabbacin tana da kati ne ko akasin haka, shi ne ya ɗauki number Angelina ɗin ya sanya a wayansa ya kira.
"Sorry I'm coming now". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe. Kai kawai ya jinjina tare da katse kiran, yana tsaye karkashin wata bishiyar mangoro mai girma, ya yi wanka ya cire kakin dake jikinsa, yana sanye da sleeping silky pjs, dan a cewarsa yana miƙa mata wayar barci zai zo ya yi, shiyasa yai shirin kwanciya!..
Fitowa ta yi daga room ɗinsu da gudu, a parlo ta haɗu da su Arya, kallon tsab suka fara yi mata kafin Arya ta ce. "Are you okey? Wannan kwalliyar fa?"...... Tsakaninsu akwai tsananin kaunar da amana sai ta faɗa masu komai dake wakana, bata ɓoye ba dan basu ɓoyewa juna komai.
Siririn tsaki Arya ta ja kafin ta ce. "Soyayya yana neman sanyawa ki manta ke Æ´ar wacece ko? Da kika ce ya jiraki faÉ—a mun ta hanyar da zaki bi ki fita gidan nan?"........ Manassa ta amsa da. "Bloody, wai meyasa kike haka ne? Ba ta ji tana son shi ba? Ku kyaleta mana, in ta ga hanyar fita to ta je, mu kuma zamu rufa mata asiri".
Angelina ta karɓe zancen da cewa. "Ban ga abin hanata yin soyayya ba, ta je mana, baby ki dawo da wuri idan kin samu hanyar fita, kuma ki tabbatar kin sace zuciyansa, ki yi mashi abin da zai kwana mafarkinki, kada ki kyale zuciyansa ya huta daga tinaninki kin ji?". Cike da kwarara mata gwiwa ta yi maganar. Arya dai bata sake ce masu ko kala ba, dan ta lura dik suna supporting V.
Da sauri V ta matso ta rungumesu kafin ta ce. "I really love you my blood"..... "Love you too baby". Har suna haɗe baki wajen faɗa. Sakesu ta yi tare da juyawa da sauri ta nufi kofar fita cike da confidence ɗin zata iya da jami'an dake gate, tana jin zata iya raina masu hankali. Har zata fita waje muryan Angelina ya katseta da cewa. "Baby, make sure kin sace zuciyansa, kada ki bari ya tafi bai maki kallon da zai tabbatar maki da kin shiga ransa ba, ki rike mashi wuta da shagwaɓa da kalamai"....... Da okey V ta amsa kafin ta yi masu godiya, suna faɗin I love you ita tana basu amsa har ta fice.
A harabar gidan ta tsaya tana kallon waɗan nan jiga-jigan sojojin dake kai komo, suna wani muzurai, to ita yanzu idan suka tambayi ina zata je ina zata ce masu? Can kuma ta tina ai ta taɓa shiga gidan MG watau Major General, ta taɓa shiga a time da matarsa ta haihu, dan haka bari ta ce masu can zata je. Nufar gate ta yi ba tare da tsoronsu ko kaɗan ba, to sun saba da su, dik muzurai da jajayen idanunsun nan su V basa tsoronsu.
Tin bata iso wajen ba wasu jiga-jigan sojoji su huɗu suka miƙe tsaye suna jiran ta iso su ji dame take tafe. A daidai lokacin ana danna horn a bakin gate ta waje wanda ya ɗauke hankalin dikkan jami'an dan already an basu masaniyar zuwan baki. Da sauri suka wangale gate ɗin. Take jerin gwanon motocin daddyn Noor suka danno cikin gidan, da alama ya yarda da tayin GAT na ya zo gidansa ya kwana kenan.
Lallaɓawa ta yi, ta faki idanun jami'an ta sulale ta cikin jerin gwanon motocin nan ta nufi waje. Babu wanda ya ankara da ita, da gudu ta bar arear gidan nasu. A main gate ɗinsu da ta zo fita dakewa ta yi, sojoji shidda ne ke gadin main gate na shiga Senior staff side, sai dai yanzu ɗaya ne a wajen, saura biyar dik sun tafi masallacin sallar ishai.
Dan haka with her full confidence ta nufi gate ɗin, yana ganinta ya miƙe tsaye, tana karisowa fuskansa babu alamar wasa ya ce. "Where are you going by this time?". Ya faɗa yana kallon army watch dake ɗaure a hannunsa, wajen babu haske sosai sai hasken streetlight............. Ɗaure fuska sosai ta yi, babu alamar wasa a tattare da ita, ID card ɗinta ta ciro daga aljihun wandon jikinta, ta kunna light na wayar Angelina, ta haska mashi ID card ɗin da kyau kafin ta haska mashi fuskanta da kyau ya gani.
A dake ta ce. "Wajen daddy na zan je". Ɗan kamewa ya yi tare da shiga taitayinsa, dan matsayin biyu ta taka yanzu a gabansa, matsayin ƴa ga GAT, da kuma matsayinta a fagen aiki, ID card na aikinta ta nuna mashi, watau idan suna taƙama su jami'ai ne ita ma jami'a ce, idan suna takama da karfin dantse ita kuma jami'a ce dake taƙama da kaifin ƙwaƙwalwa, ba'a aiki sai da jami'ai irinta!........ Da kyau, abin ya bada citta.
Bata jira amsarsa ba ta nufi waje abinta, dama jami'an gate na gidansu ne take shakka, dan su ne daddynta ya baiwa cikakkiyar damar hanasu fita ba tare da babban dalili ko izininsa ba, amma jami'an dake main gate ai su dikka Senior staff side suke gadi, yaushe suke da Æ´ancin hana mutum fita? Su aikinsu su tsare masu shigowa su cajesu kada wata barazana ta gifta side É—in!.
Sauri sosai ta dinga yi tana addu'ar kada su haɗe da daddynta a hanya komai ya lalace. ALLAH ya taimaka har ta isa basu haɗe da shi ba. Tin daga nesa ta hango jarumin nata tsaye a ƙasan bishiya, ya juyawa hanyar da take zuwa baya, yana rungume da hannayensa a massive chest ɗinsa. Wani musulmin ajiyar zuciya ta sauke tare da yin gaggawar karisawa wajen.
Excuse ta yi mashi kafin ta zago ta gabansa. Slowly ya ɗan ɗago da kallonsa a kanta, bai san time da ya waro eyes ɗinsa sosai a kanta ba! Ta yi kyau matuƙa, ga hasken streetlight dake gefe-gefensu na haskata da kyau!. Ita ma ɗan ɗauke wuta ta yi a kallonsa cikin kayan barcin, sai take jin tamkar ta rungumesa saboda haɗuwansa, amma ta daure da cewa. "Sorry sir, na barka kana ta jirana ko?".
Kai ya ɗan girgiza kafin ya amsa da. "Nevermind, this is your phone". Ya faɗa yana miƙo mata wayan. A maimakon ta karɓa sai ta ce mashi. "Tin bamu gaisa ba zaka bani wayar? Ko baka son yin hira da ni ne?"........ Sauke eyes ɗinsa a kanta da kyau ya yi, sai da ya ji faɗuwar gaba, amma ya basar da cewa. "I'm feeling sleeping"...…... Ta gamsu da hakan dan ga idanunsa nan dik sun juye, a shagwaɓe ta ce. "In zo in tayaka kwanciya ne?"........ Lokaci guda ya ɗan saki one side smelling da bai san ya yi ba, wacce kuma ta ƙara fito da tsantsar kyansa, wai ta zo ta taya shi kwanciya, a ransa ya ce ƴar karama da ita sai iya magana da shegen shiga rai.