← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 227

Sashe 194

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dik da Arya bata jin yarensu ta gane nufin yarinyar saboda kwatancen da take yi da hannunta, ta nuna ya cire mata kaya, ta nuna ya kwantar da ita, ta kuma nuna ya hau kanta, sannan ta nuna wancan matar ta ture shi, yanzu Arya ta fahimci fyaÉ—e kenan ya so yi wa yarinyar sai ALLAH ya dawo da matar tasa, dan ta dakatar da shi tana ihu ne ya hau dukanta, abin da ake cewa borin kunya, tabarmar kunya da hauka ake naÉ—eta.

Ai wani irin tafarfasa Arya ta ji zuciyarta yana yi mata, a fusace ta saki yarinyar ta miƙe, gadan-gadan ta nufi mutumin, su dama ai aikinsu shi ne dakatar da ɓarna, kansa ta yi, ta zare ƙaramin wuƙarsu na sojoji dake da mazauni a jikin takalmarsu.

Zare wuƙar ta yi, yana wani kyalli saboda kaifinsa, mutumin yana baje a ƙasa yana nishi sama-sama. Ai tana zuwa ta damki mazargin wandonsa, zata yi mashi kaciya part two tin da shi ɗan iska ne!.

Nan fa mutanen dik suka watse suka fara ihu, wasu mata ƙalilan ne suka tsaya, basu wuce su 8 ba, suka tsaya suna kallon Arya cike da jarumta. Cikin harshen fillanci suke cewa Arya ta kashe shi, saboda dikkansu ya keta masu haddi, ya masu fyaɗe, ba mutumin kirki bane, ga shi kuma shi ne sarkinsu a wannan tafiya, haka yake amfani da matsayinsa na shugaban tafiyar yana keta haddin mata, dik kuma ƴan uwa tsoronsa suke ji, saboda zafinsa da mugunsa.

Ya dakeka ya hanaka kuka haka yake yi. Arya bata jin me suke faɗe, ita dai ta nufi yin abin da ta yi niyya kawai. Ko kaɗan Arya bata razana ba, ta zare wandon mutumin nan, da wata abar tasa kamar karas saboda ƙanƙanta sai iskanci cike da kai, aikuwa Arya ta gille abar, tai mashi kaciya part two, tin daga ƙasanta ta yanke mashi ta jefar, sai ta yi jefa da wukar tata game da zare hand groves ɗinta ta zubar a wajen. Tana wani irin huci tamar zata kama da wuta, jinin mutumin ya fallatsa har kan hand gloves ɗinta ba iya wuƙar ba.

Shi kuwa wani irin ihun azaba ya zunduma a lokacin da ta yanke, ihu ɗaya kuma ya kurma ya ɗauke wuta ɗiff alamar ya suma. Abin da Arya ta yi ya yi matuƙar gigita wannan yarinya, ihu ta kurma ita ma game da rikicewa ta rasa ina zata nufa, hakan yasa Angelina ta rikota game da rungumeta tana ɓoye mata fuskarta kan ta daina kallon mutumin ma.

Ganin haka yasa wani matashi dake laɓe yana jiran ganin me Arya zata yi wa mutumin da ta zaro wuƙa ne ya dallah da gudu ya nufi cikin daji. A razane yarinyar ta fara nuna mutumin tana ihun tana faɗin har da shi ma yana cire mata kaya idan Addar tata ta tafi yin ita ce, yana cire mata kaya ya hau kanta, shi ma ƙanin wannan mutumi ne.

Ai da gudu Arya ta bi bayansa shi ma, sai dai bai yi wani nisa ba ya ci karo da Zaynish da ya fito daga bakin ruwa, jin ihu a wajen yasa ya zo duba menene?.

Karo matashin ya yi da Zaysh, ya bugi kirjin namiji, sai ga shi a kasa wanwar, daidai lokacin Arya ta iso gaban Zaysh da gudu tana nishi sama-sama. Kallo ɗaya Zaysh yai mata game da ɗauke kai kafin ya ce. "Lafiya?". A daidai lokacin matashin ya miƙe zai cigaba da gudu kenan Zaysh yasa kafansa ɗaya ya kwashe kafafun matashin a in da ya zube ƙasa.

Ƙamewa Arya ta yi tare da sarawa Zaysh kafin ta kora mashi jawabin abin dake faruwa. Ta faɗa game da nuna mashi ƴar yarinyar da ya yi wa fyaɗen. Kallo ɗaya Zaynish ya yi wa yarinyar, take ya ɗan rintse idanunsa, jikinsa har wani tsuma ya fara yi yana wani jijjiga saboda takaici, a yadda yaga yarinyar nan ha zata wuci 10 to 11 years ba, me ta sani da zasu yi mata fyaɗe?.

Ai Zaysh bai san lokacin da ya damko matashin nan ba, wani irin jibga da ya fara yi mashi ko amaryar Aunty Ummi bai yi mata ba, ya dinga gwara kansa da jikin itatuwa. Sai da ya yi mashi lilis har matashin ya daina motsi, ya fashe mashi baki da hanci a in da ya haÉ—e mashi jini da majina.

Jifa dashi ƙasa ya yi, ya kai hannunsa ya ware zariyar wandon matashin, ɗago idanu a kan Arya dake tsaye tamkar an sassaƙata ya yi, ta gane nufinsa, da sauri ta juya ta bar wajen, watau kada ta ga sirrinsu na maza, bai san Arya kam yanzu ya gama yi wa wani sabon kaciya ba.

Tana barin wajen ya zaro wuƙarsu na sojoji dake jikin takalmansu ta jefe, shi ma babu tausayi ya datse mashi abar daga jijiyarta ya jefar. Wani irin azababben ihu da matashin nan ya kurma sai da gabaɗaya dajin ta amsa. Zaynish sai huci yake yi ya bar wajen ya bar matashin a baje a ƙasa.

Ƙarisawa wajen da su Arya suke Zaysh ya yi, dan ya duba ko akwai wata matsala. Nan ya isko Arya ta tasa wannan matar mutumin a gaba tana yi mata bayanin ƴar kurma-kurma game da wannan yarinyar. Matar ta ce. "Wannan yarinyar dai a can yawonmu na fulanin tashi muka tsintota a cikin daji, dikka ƴan uwana sunki ɗaukarta, amma ni a matsayina na wacce na taso a gidanmu ina da ƙanwa kamarta, sai na ce zan ɗauketa, mijina ya ce ba zai ciyar da ita ba, haka na yarda na ɗauketa, muna rayuwa da ita a gida, mijina baya bata abinci, ni nake shiga daji in nemo mata abin da zata ci. (ALLAH sarki shiyasa ranar take kukan yunwa su Arya suka bata abinci a kudanci) Mijina baya sonta, ya sha korarta waje ta kwana a waje ita kaɗai, ga shi bamu san kowa nata ba, mun kasance tare da ita tsawon shekaru biyu muna yawo ƙasashe, tin bata iya yarenmu ba har ta koya, bamu san danginta ba, bamu san kowa nata ba".

Hakika basu fahimci maganar matar dikka ba, amma sun É—an fahimci wasu, sun gane tsintar yarinyar suka yi, sannan sun gane cewa wannan mutumi mijin matar nan ne, sun gane yana ganawa yarinyar azaba.

Da yake ba komai suka fahimtar ba sai Arya ta miƙe tana faɗin. "V muje". Ta faɗa da nufin su tafi su barsu a wajen tin da sun hukunta mutumin........ Zaynish da yakasance namu ne, ɗan mutan Niger girman Nigeria, tsab yana jin fillanci, sai dai baya jin na bororin daji sosai, shi ma bai gane komai yadda yakamata ba, amma ya fi su Arya fahimta.

A dake cikin bada umarni ya ce da Arya. "Ki ɗauki yarinyar ku wuce da ita sansani, idan mun koma gida zamu miƙata ga gwamnati a nemi iyayenta, waɗan nan suma tsintarta suka yi". Yana gama faɗar haka ya juya. Da sauri Arya ta kama hannun yarinyar, dan dama ta shiga ranta matuƙa, tin da ta fara kallon yarinyar a kudanci ta ji ta kwanta mata.

Jan yarinyar suka yi, suka tafi suka bar matar da mijinta da sauran Fulani a wajen. Sansani suka koma, yarinyar ma ta ƙanƙame Arya sosai, da alama jininsu ya haɗu sosai, sai shasshafa hannun Arya yarinyar take yi kamar taga wani abin. Kai tsaye cikin tantinsu Arya ta shige da ita, ta zaunar da ita kafin ta ɗauko mata ragowat abincin safenta, da alama Arya na son yara, dan kuwa zama ta yi ta dinga baiwa yarinyar abinci a baki, bata ji kyamarta ba sam.

Yarinyar tana cin abinci tamkar yadda dabbobi suke ci, babu wani control, turawa kawai take yi, hakan yasa Arya ta É—aura É—amara, ta dinga nuna mata yadda zata yi a natse. Su V dik sun zuba idanu suna kallonsu.

Sai da ta tabbatar yarinyar ta ƙoshi, sannan ta bata ruwa kafin ta ce su je ta yi mata wanka, dan ta yi datti over, sai wari take yi, ga ƙananan kyawawan hakwaranta sun yi jajir saboda rashin yin brush, fuskanta dik a ƙoɗe. Su dai su V kallo ne kawai nasu, yau karon farko a rayuwansu sun ga Arya ta damu da wata, watan ma talaka, ƴar kauye, ƴar datti, kai wannan abu ya basu mamaki matuƙa, basu san so gamon jini bane, Arya irinsu ne mutanen da ake kira RESERVED PERSON, gaskiya irinsu basu da yawa a cikin al'umma, suna da tausayi amma a ɓoye, su komai nasu a ɓoye yake, basa bayyana kansu kai tsaye haka, sai dai jama'a su gane waye su ko su fassarasu yadda suke so, amma su kaɗai suka san ainahin waye su, zaku ganesu ne kawai ta aikinsu a aikace ba su fito fili su faɗa maka waye su ba, dik yaran GAT ita kaɗai ce wannan gifted ɗin.

Wanka ta yi wa yarinyar a cikin tantin da suka kafa da sunan toilet, da kanta ta É—ebo ruwa a bakin teku, ta wanke mata wannan uban gashin kan nata dake da mugun yawa, tsantsi da tsawo, dan har ya É—an zarce mazaunanta a tsawo, ga shi bakinkirin da shi har yana wani curlyn.

Da shampoo na SB-LUSH (Stars body lush shi ne na taƙaita maku da SB-LUSH) sai kamshi shampoo ɗin gashinta yake yi, take ya ɗauki kyalli. Arya ta naɗeta da towel ɗinta suka fito suka koma cikin tantinsu, ta shafe yarinyar da mayukansu masu daɗin kamshi, sannan ta ɗauko doguwar rigar dake tsaya mata a cinyoyi ta sanyawa yarinyar, ya kai mata harƙasan gwiwa.

Zaman gyara mata gashi Arya ta yi, tana tajewa yarinyar tana kuka saboda zafi, haka Arya ta dinga ce mata sorry har ta gama gyara mata, sannan ta shafa mata mai, ta É—aure mata a tsakiyar kai game da kitse mata jelar, ta yi mata rolling na jelar jikin tibka.

Take yarinta kyanta ya fara fitowa, ta ji gyara, kamanninta da Leo ya ƙara bayyana, bare ma idanun nan nasu. Wajen kwanciyarta Arya ta kwantar da yarinyar. Baiwar ALLAH, tata ci ta ƙoshi, ga wanka da aka wanke mata dauɗa, aka rabata da dattin gashinta, sai ta ji duniya sakayau, wani niimantaccen iska na shigarta, tuni ta ɓige da barci.
Chapter 194 · 0% Book details