← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 227

Sashe 51

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin Ummie yasa Leo ya ɗaure faska yaki amsawa Zaysh, dan a tunaninsu budurwar Zaysh ne, kun san tana da kyan jiki, ga shi yanzu ya fita tsawo, ga jikinsa a murɗe, in kuka gansu zaku zaci saurayi da budurwa ne. Shi dai Noor cike da farinciki ya tarbi Ummie hannu bibbiyu, dan in baku manta ba sun saba da ita a waya, har video call suna yi, dan haka da suka ganta a zahiri ba karamin daɗi suka ji ba. Noor ya bata kyautar 5000$, kin karɓa ta yi, sai da ya sanya mata a jaka, haka da suka yi sallama da Vash ma, 5000$ ya bata, nan ma taki karɓa, sai da ya sanyawa Zaysh a aljihun jaka kan ya bata, daga nan suka yi sallama a mutunce ya kama hannunta suka bar gidan, sai tambayarsa take yi meyasa Leo bai amsa masu ba, ya ce ta kyale wannan mahaukaci ne, ɗan zafin kai ne da shegen girman kai, haka suke fama da shi.

Da yake tana da hankali sai ta ce. "Anya kuwa ba wani laifi kuka yi mashi ba? Haka kawai mutum ba zai yi gaba da ku ba! Dole kun mashi ba daidai ba, faɗa mun me kuka yi mashi?"......... Dole ya bata labarin waye Leo, tin farkon haɗuwarsu a zone one har yau, ta sha mamaki sosai, sai dai kuma bata ce komai ba face ALLAH ya shirya Leo kawai. Da amin ya amsa, daga nan suka fito suka sami abin hawa, suka hau sai hotel da ta sauƙa. A nan suka kwana washegari suka hau jirgi sai Naija.

A washegari suma Leo suka wuce US da yayansa...... To dikkan mazajenmu sun tafi hotu, me kuke tinani? Kai dik fa yanzu sharan fage muke yi, yanzu muke shirin afkawa cikin labarinmu gadan-gadan, dama wuyarta su gama horo su shirya zuwa Mission ne, yanzu ainahin labarin zai fara, get ready!.

-----------------------🔥

SERAPH.

A hanyar komawarta cikin school ta haÉ—u da Rimsha tana zuwa in da take. Da ganinta da sauri Rimsha ta zo ta riketa tana faÉ—in. "Madam said it was your uncle who pick you up?"........ Kai ta jinjina alamar haka ne, sannan ta kama hannunta suka nufi class, tana son Rimsha sosai, saboda kaunar da yarinyar take nuna mata, shiyasa ita ma ta saki jiki sosai da ita, ta É—auketa tamkar Æ´ar uwa!.

---------------------🔥

Basu suka fita daga wannan ɗakin aikin nasu ba sai da rana ta faɗi, sannan suka ɗauki wayoyinsu, yadda kuka san wasu gumaka haka suke aiki, babu uhm bare umm umm ko hira a tsakaninsu, aiki kawai babu kama hannun yaro. Da suka miƙe dikkansu Lion ya fisu tsawo da faffaɗar kirji, dik da suna sanye da jacket saboda sanyi, amma shi zaku iya ganin yanayin murɗewar jikinsa shi da Champions sun fita sosai.

Waje suka yo, ɗaki ɗaya suka shiga. After 1h suka fito cikin shiga iri guda, fuskokinsu sanye da nose mask, daga ta ciki ƙasa wandon jeana ne baki, sama kuma white polo t-shirt, sai suka ɗaura winter jacket zuwa gwiwa a jikinsu, sun sanya hular kayan a kansu, kafafunsu da socks baki, while sun sanya boot mai zubin waterproof haka shi ma baki. A ido dai sun yi mugun kyau sosai, amma kada a tona zuciyansu.

A tare suka sauƙo ƙasa, kowanne ya shiga motarsa daban, Champion ne ya fara yin gaba lafin guru, sannan Lion ya rufa masu baya a karshe. Kai tsaye star hotel suka nufa, a wajaje daban-daban suka paka motocinsu, da yake parking space na hotel ɗin yana mugun girma, sai suka bada rata sosai a tsakanin motocin nasu.

Lion ya rigasu fita ya nufi elevator, amma kafin nan sai da ya kama ɗaki a hawa na goma sannan ya nufi elevator ɗin, yau sun sanya korean face ne, dan kana ganinsu zaka ɗauka koreans ne, saboda ɓadda kama ma Lion Chenise face ya sanya, guru and champion suka sanya korean face.

Kai tsaye hawa na 10 Lion ya haura, Champion yana fita daga motarsa ya wuce izuwa bakin ruwan dake gaban hotel É—in, cikin takun jarunta da kwazo, zallar kwarewa a iya aiki. Shi kuma guru ya wuce wajen kayan kwalama, ya sayo masu chips and drinks, ya zo ya isko Champion a bakin ruwa yana zaune saman É—aya daga cikin chair na table da aka shirya a wajen dan kara É—aukar hankalin jama'a su ziyarci wajen.

Zama suka yi tamkar wasu bayin ALLAH, cikin natsuwa suka zame nose mask dake fuskokinsu, dan dole suka hau cin chips É—in nan ba wai dan suna so ba. Kana ganinsu ka ga abokai Æ´an korea.

Lokaci guda tsaro ya kewaye wajen, wasu manya-manyan jiga-jigan sojoji ne suka kewaye bakin ruwan, wasu mada karti da su, suna wani muzurai, kai ka ce zasu iya hana mala'ikan mutuwa ratsawa ya É—auki rai. Kallon gefe-gefen ido su Champion suka yi wa jami'an, sai kuma suka haÉ—a ido.

A lokacin da dattijon ya sako kafafunsa bakin ruwan sai da ko'ina ya yi tsit, a natse wannan dattijo ya tako ya shigo ciki. Ɗaukar drinks a glass cup Champion ya yi tare da kashewa guru ido ɗaya, kamar zai kai drinks ɗin bakinsa sai ya kauce, ya sanya lips ɗinsa ya ɗan taɓa gefen babban yatsansa dake rike da cup ɗin, take wajen ya kawo wani haske blue sau biyu a jere sai kuma ya ɗauke. Tsabar bala'i da kwarewarsu a aiki jikinsu ma da na'urorin isar da saƙo tamkar wasu saƙaguna. Saƙo ya isarwa da Lion cewa dattijon ya iso, tsaro ya yawaita a wajen, idan suka ce zasu yi waya ko typing message in an zo binciken gawa ana iya cewa a nemo masu yin waya tin bayan shigowar ministan ko a nemo masu typing, kun ga zasu shiga alamar zargi, bugu da kari idan aka kalli irin wayoyin da suke rike da shi, da sh ma ana iya amfani wajen kamasu, dan haka ba ruwansu da waya, suna da hanyar isar da saƙo a natse ba tare da barin wata alama ba. Kai ku dama ai tin da aka ce maku duniya dikka nemansu take yi kun san haɗarinsu ya zarce yadda ake zato, fin haka ma zasu aikata.

Lion dake kwance a saman bed na ɗakin da ya kama ne ya samu saƙon Champion, shi ma gefen babban yatsansa ne ta kawo blue light sau biyu. A natse ya miƙe tare da nufar restroom na ɗakin. Jim kaɗan ya wuce WC side. Wani abu kamar powder ya buɗe a leda tare da fito da handkerchief fara daga aljihunsa, sai da ya gyara nose mask ɗinsa kafin ya yaga ledar wannan powder ya zuba a saman handkerchief ɗin, ya sanya hannunsa dake ɗauke da dogayen yatsu sosai, ya jujjuya powder a saman handkerchief ɗin sosai, sannan ya zubar da powder ɗin a cikin WC, ya yi flushing da ruwa. Ya ninke hankey ɗin ya tura a aljihunsa tare da fitowa, sai ya dunkule hannunsa da ya taɓa powder.

Ƙasa gabaɗaya ya sauƙo, cikin takun zallar jarumta kai tsaye ya tinkari wajen. Sai shiga side ɗin jami'an dake tsaron ministar suka dakatar da shi, ɗaya daga cikinsu ne ya ce ya nuna masu card ɗinsa dake nuna cewa ya kama ɗaki a hotel ɗin nan, idan ba haka ba ba zai shiga wannan waje ba, saboda tsaron lafiyan ministar.... KUN GA AMFANIN KAMA ƊAKIN NASU KO? Shaggun kai ne, akwai basira sosai.

Card na buɗe door na room da ya kama ya fitar daga aljihunsa da ɗayan hannunsa ya miƙa masu, ɗayan hannun nasa dai har yanzu a dunkule. Tsabar yarda da kansa a kwarewar aiki har da zame nose mask ɗinsa ƙasa dan ma su ga face ɗinsa da kyau. Duba card ɗin da kyau suka yi kafin su miƙa mashi kayansa, ko sannu bai ce masu na tamkar kurma, ya karɓa ya wuce cikin wajen.

Yana takowa a natse cikin jarunta ya nufi jerin securitys guda shidda take takewa mai kawo abinci a wajen baya, ya É—auko abincin ministar ne suka take mashi baya dan tsark. Babu shakka ko tsoro Lion ya tinkaresu gadan-gadan. Sai da ya iso tsakaninsu taku biyu sannan ya É—an kauce masu hanya, kaÉ—an suka É—an bugi juna da jami'in dake gefen mai É—auke da abincin. Sorry ya yi wa jami'in tare da ware tafin hannunsa ya É—an yi wa jami'in alamar ban hakuri, juyawa jami'in ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya dai jinjina kai alamar to. Daga nan Lion ya wuce ya nufi in da ake oder abinci.

Su kuma suka wuce suka kaiwa ministar abincinsa. Kunsan waje da ake oder abinci dole akwai fili na musamman dan wanke hannu, nan Lion ya shiga ya wanke hannunsa kafin ya fito ya saka oder abinci, sannan ya koma saman chair daban nesa da su Champion ya zauna yana jira.

After 5 mins sai ga masu kawo abinci sun kawo mashi abin da ya yi oder. Kan babban yatsansa ya danna, take red light ta bayyana sau biyu a wajen, red light alama ce ta zubar jini, saƙo ya turawa su Champion a kan lokacin zubar jini ya yi, dik yatsun hannunsu cike yake da na'urorin dan balai, kuma kowanne sun san saƙon da suke aikawa da shi, kai sun zarce yadda kuke tinani. Ni kaina sun zarce yadda nike tinani, makasa ne masu bala'i basira, kun ga kuwa kama waɗan nan ba abu bane ma mai yiwuwa, amma a haka wai suna cikin list na FIVE MISSION nasu Noor namu! Kuna ganin hakan zai yiwu kuwa? Su Noor zasu iya kamasu? Tsorona ALLAH tsorona rasa ko mutum ɗaya daga team ɗin su Leo, wannan Mission ɗin babbar abu ce, kai na ce yanzu wasan zai fara.

Wannan saƙo na isanwa su Guru ko second goma ba'a ƙara ba ministar ya fara tari, ai sai jini daga bakinsa. Da wani irin masifaffen gudu jami'an dake tsaronsa suka yi kansa, Lion kuwa drink na kankana da yasa a kawo masa ya ɗauka ya ɗan yi sipping ya ajiye kafin ya motsa daga in da yake.
Chapter 51 · 0% Book details