← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 227

Sashe 175

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Leo sai da ya É—an girgiza ganin waÉ—an nan uban tulin kwalin Tramadol É—in nan, katon container irin wannan cike da manyan kwalinsa, ya rabb. Umarni ya baiwa su Noor da su mayar su rufe, sannan ya wuce gaba. A nan ma da kansa ya buÉ—e container.

Ya rabb Codeine Syrup ne a cike a ciki. Codeine a idanun al'umma ana kiransa da maganin tari, amma ana sha ne dan maye, kuma mugun illatar da lafiya yake yi. Yana lalata hanta, hassasa matsalar numfashi, mutuwa idan an sha fiye da misali, manyan ƙasashe da dama sun haramta shigo da shi ƙasashensu, amma Avaris ta zama kwandon sharar ƙasashen dake son cin karensu babu babbaka, komai shigo masu da shi ake yi, saboda ƴan ƙasar har yanzu a kwance suke, sun ki tashi su farka su fahimci dik wannan abin su tsabtace kasarsu daga gurɓatattu!.

Kai kawai Leo ya jinjina game da cewa su rufe su shiga wata container. Haka kuwa aka yi, suka mayar suka rufe, suka wuce container na gaba.

A wannan container na gaban cike yake da fake drugs, copyn magungunar gaske kenan, sunayensu da komai tamkar na gaske, sai dai ko kaɗan babu sinadarin magani a ciki, sai dai sinadarin guba mai cutarwa ne a ciki. Waɗan nan magunguna suna sanya ciwon koda, ciwon hanta, mutuwa a hankali, ka je sayen magani dan ka samu lafiya, sai a ƙara maka wata cuta, ya ALLAH kana ganin al'ummar annabi yadda ake yi mana, ya ALLAH ba zamu iya ba, sun fi karfinmu, amma basu fi karfinƙa ka ba, ya ALLAH ka kawo mana ɗauki.

Wucewa container gaba Leo ya yi. Wannan container shi kuma cike yake tab da manpower, king power, double action da makamantansu, ina maza masu shan man power? To albashirinku! Kuma ga naku ta iso! Dan balai ba zaka zauna yadda ALLAH ya ajiyeka ba, to ai zaka shawa kanka balai. To waɗan nan magunguna da ake shigo dasu da sunan man power ba ma a gwada su a asibiti ba, suna ɗauke da sinadarin da ke sa bugun zuciya su jawo bugun zuciya da sauri, mutuwar mazaje da yawa a sirrance ba tare da an san ainahin me ya kashesu ba, namiji zai mutu ba tare da yasan me ya kashesa ba, waɗan nan magunguna suna buɗe jijiyoyon namiji ne, ba karfi suke ƙara maka yadda kake tinani ba, buɗe jijiyoyinka suke yi, su bar iska ya shiga jikinka na wuce misali, su haifar maka da mutuwar gaba idan ka cigaba da sha, wlh suna sanya ciwon zuciya, saboda ita zuciyarka ba zata iya karɓar yadda jikinka zai buɗe lokaci guda ba, iskar dake shiga tana hura zuciyar take ta kumbura, idan namiji ya sha shi mai yawa a lokacin ma a take yake mutuwa. Sai ka ji masu sayarwa suna cewa baida side effects, sannu na ce, na ce sannu dan uban mutum!! Kai ni fa raina ɓaci yake in na ga ana cutar da bayin ALLAH, ina jin tamkar in zama namji irin sayyidina Ali!.

Wannan magana ta maganin karfin maza ta tina mun da wani da ya mutu a hotel bayan shan man power, ya ALLAH, maza su yi ta mutuwa a rasa me yake kashesu, jahilan cikin al'umma su yi ta tallar man power ba tare da sanin ainahin dame ake yinsa ba, suna kashe al'umma cikin rashin sani da sunan wai su suna neman kuÉ—i. To hajiya Jummai, fatan idan kin gama karantawa in ma mijinki yana sha zaki taka mashi birki! Idan kinga wani naki zai sha ki taka mashi birki! Dan zallar cuta ce a ciki! Dan haka ki yi gaggawar takawa mijinki birki, ki tattara sauran power da kuke da shi ki kunshe mashi kayansa a wando!

Idan kuwa kinƙi dakatar da shi to fa ɗan karfin da yake da shi ɗin zaku rasa, dan in yana da sauran shan ruwa a gaba bai mutu ba, to at the end abar tasa mutuwa zata yi ta daina aiki, kinga kuwa bai samu power ba wanda yake da shi kun rasata. Wata ma sai kuga ita ke sayawa mijin man power, su man power manya, zakuwa ki ga man power. Wlh mata tin wuri idan zaku tattara mazajenku ku turasu gudun motsa jiki da gym kullum dan su samo power ɗin asali is better for you, gym yana sanya jikin namiji ya yi karfi, dik wasu matattun jiyoyi zasu miƙe, yana ƙara girman gaban da kukewa haukar neman har kuke kai kanku ga halaƙar in da zaku rasa ɗan wanda kuke da shi. To maza, gym yana ƙara girman gaba da kuke so ɗin, ba sai kun sha man power ba zaku samu ingantaccen power da babu mix, sannan gym yana ware ƙasusuwan gaɓɓai yasa su yi kwari sosai, yana ƙara lafiya da daidaita zuciyar ɗan adam, kai in taƙaice maku kai da kanka in ka fara zaka ji jikinka ya canza, ya yi maka daɗi da sauransu.

Mata ku tura mazanku gym ko dan su dinga É—aukarku kamar Æ´an baby suna jefawa gado kamar matan novel, da zarar yana gym komai girmanki zai É—aukeki cak, to kashinsa ya yi kwari, amma yanzu kun kyalesa dik man gyaÉ—a da gishiri ya kashe dik wani karfin da yake da shi, ga wata musifa wai man power, ba dole a samu tangarÉ—a ba!.

(Kuma mata masu shan hips and breasts enlargement yake kome? Ku jira, zan bangaɗo maku dame ake haɗasa, naku na nan tafe, ai nai alƙawarin sai fa na faɗi komai dake cutar da bayin ALLAH!)

Container na gaba kuma maunguna ne irinsu diazepam, rohypnol, valium, magungunan bacci da kwantar da hankali a cewarsu, ana shigo da su da yawa ba bisa ƙa'ida ba, kuma ana bawa yara, mata, direbobi, musamman direbobi, za'a basu shi da sunan maganin hana barci, hakan na haifar da haɗasussuka a hanya, babban illar ce ga al'umma.

Har kan Leo ya fara ciwo ganin waɗan nan ɓarna, amma ya daure suka je container na gaba. Suna buɗewa kwali-kwali na antibiotics ne a ciki, ana shigo da su suma ba bisa ƙaida ba, al'umma suna sha ba tare da sani ba. Kwayoyin suna cutar sosai, mutane su mutu cikin sauƙi, da ka yi zazzaɓi sai mutuwa.

Time Leo ya duba a wayansa 2:30 ta yi. Cike da bada umarni ya ce su yi sauri gari ya kusa wayewa. Daga nan suka wuce container ta gaba. Suna buɗeta allurai ne dayawa a ciki, ai yana ɗaura idanunsa kan kwalaben alluran nan sai da ya ji gabansa ya faɗi. Soja da faɗuwar gaba ai kun san ba lafiya. Da yake basu da ishasshenlokaci a gurguje ya ɗauki alluran kwalba ɗaya ya zura a aljihunsa ya ce su mayar da saura su rufe tamkar ba'a taɓa taɓawa ba.

Haka suka bi dik containers ɗin da suka buɗe, a kowani container sai Leo ya ɗauki abu ɗaya har suka isa kan miyagun kwayoyi, a nan ma ya ɗauki cocain ɗaya. Suka mayar da komai tamkar basu taɓa ba, sanna ya kwance karnikansa, ya ce Noor ya rike mashi ɗaya bari ya rike ɗaya, Noor ya ce. Shi wlh yana tsoron kare, basa haɗa hanya da kare, kada ku manta yana da cutar tsoro, tin ainahi haka yake da tsoron kare, kun gansa dai jarumi, wlh zai iya kama maciji, amma baya son kare ko kaɗan tamkar mai aljanu a kai.

Miƙawa Zaynish igiyar karen Leo ya yi, ya karɓa ya rike, shi kuma ya riƙe ɗaya suka nufi hanyar komawa, yau ba barci akwai bincike kenan. Sun fara tafiya Vash ya karɓi igiyar karen hannun Leo dan ya taimaka mashi, saboda Leo ɗin ya fisu shan wahala, dik containers ɗin nan shi ya bubbuɗesu.

Suna tafiya a hanya ne Vash ya ce. "Da mun cinnawa wajen wuta ai, komai ya ƙone su rasa shi"....... Nisawa Leo ya yi tare da cewa. "Ai bombing na wajen ba shi ne mafita ba, dakatar da masu aikata hakan ba shi ne ba, mu kama masu yi mu kashesu shi ne, idan har zaku rinƙa kama waɗan nan containers ɗin dik shime ne, in mun ƙona wasu waɗan nan yau, gobe zasu sake shigo da wasu, dan haka masu aikata hakan zamu raba da numfashinsu, shi ne ɓarna zata dakata!".

Noor ya ce. "Gaskiya Avaris ta kai maƙura a wajen lalacewa"...... Leo ne ya amsa da. "A wannan case ɗin navy suna da babban kamisho, sun taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar ƙasar nan, kome za'a shigo da shi daga waje ta ruwa ne, me amfaninsu da ba zasu dakatar da ɓarna ba? Ko dai dama an ajiyesu a bakin ruwan ne dan su dinga kamun kifi ko suna zaman kirga jiragen ruwan da zasu shiga su fita?". Cike da takaici yai wannan magana, ya rasa meyasa yake jin tsananin kaunar kasar Avaris.... Ni kam na ce saboda ƙasar mahaifinka ne mana, ai jininka suna ciki, dole ka so ƙasar.

Zaynish ne ya ce. "Amma idan navy suna da laifi kaso 40 cikin ɗari na lalacewar ƙasar to fa ministar of foreign affairs yana da kaso 55 cikin ɗari, ministan tsaro yana da 75 cikin ɗari, sai number ɗaya na ƙasan yana da 100 cikin 100!".

Kai Leo ya jinjina, su Noor dik kai suka jinjina, a dake Leo ya ce. "Ni ban yarda wani soja ya bani umarni a kan rashin adalci in masa biyayya ba!"..... Dikkansu basu fahimcesa sosai ba, Vash ya ce. "Kana nufin ba zaka yi wa AZURE biyayya ba?".

Kai ya jinjina. "Ba AZURE ba, dik duniya babu wanda ya isa in yi mashi biyayya kan cutar da al'umma! Wlh yadda na yi rantsuwa da ALLAH kafin in saka wannan kakin kan zan kare rayuka, dukiya, ƙasa bakiɗaya, to billahil lazi babu wani mahaluki da ya isa ya tilastani ya bani umarnin in yi shiru ana cutarwa! Sai dai a kasheni a kan haka, amma wlh dik masu ɓarna sai na dakatar da su, Navy sun yi alƙawarin kare bakin ruwa, ba zasu bar dik wata cutarwa ta ruwa ta shigo ƙasa ba, amma me muka kama yau? Ina suke da har suka bar hakan ke faruwa? Okey baa basu izini ba ko?". Cike da takaici ya kai karshen maganar.
Chapter 175 · 0% Book details