← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 227

Sashe 94

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dan kuwa yadda kuka san bar na shaye-shaye haka wajen yake, ga wani dim light purple kala, wasu manya-manyan glass ne shake da abubuwan sha kala-kala wanda na tabbatar kuÉ—insu ba zai faÉ—u ba, dan tsadaddun kayan drinks ne a wajen.

Daga gefen glass É—in can É—an nesa wasu sofa set ne a wajen, ga kuma irin torch creen computer É—in nan tangameme a wajen sofa set É—in, da alama wajen shirya project É—insu ne. ÆŠakin sai kamshi yake yi.

Wajen sofa ɗin ya karisa, a saman ɗaya daga ciki ya zauna, yana zama sai ga Dr Mark ya shigo, kai tsaye wajen glass na drinks ɗinsu ya nufa, wani tangamemen bottle ya ɗauko da glass cup, a wajen sofar ya dawo. Abin mamaki drinks ɗin da sanyi sosai, da alama glass freezer ne a wajen. Ɓalle bakin bottle ɗin ya yi, ya zuba drink ɗin a cup, sipping ya ɗan yi tare da cewa. "In zuba maka ne?".

Kai Dr Kamal ya girgiza tare da cewa no. Zama ya yi ya cigaba da sipping a hankali cikin natsuwa, babu wanda ya sake ce da wani uppan.

To mu bi sister Zinta kuma. A lokacin da suka shiga office na Dr James da sister Lazy jikinta sai kerma yake yi, umarni Lazy ta bata da ta tsaya a tsaye, ita kuma ta zauna a kan visitor chair. Tana zama Dr James ya ce. "Get out!".

Wani irin kululun bakinciki me ya turmuke zuciyanta, jikinta har kerma yake na takaici, ga shi ba yadda ta iya da shi, haka ta miƙe tsaye cike da kunyar ya walaƙantata a gaban Zinta. Tana miƙewa ya ce. "Zinta have a seat". Ya faɗa still bai ɗago ya kallesu ba. Wucewa Zinta ta yi, ta zauna a saman kujerar da Lazy ta tashi, ita kuwa Lazy da wani mahaukacin sauri ta nufi waje, dan gab take da haɗiyar zuciya ta mutu.

Kamar yadda Dr Kamal ya baiwa Maya files and documents haka Dr James ya baiwa Zinta ta sanya hannu, sannan ya ce tana iya tafiya. DaÉ—i tamkar ta mutu saboda ya ce a tare zasu yi wannan project É—in, sai sun kammala project É—in zata koma aiki a section C É—insu, ko a iya haka ta yi nasara, zata samu damar zama kusa da shi, ga shi idan suka shiga project suna iya É—aukar watanni 6 zuwa 8 kafin su kammala, gwargwadon yanayin project É—in dai. To kun ji yadda sister Zinta ma ta kare da Dr James, to mu koma kan su Dr Kamal.

Suna zaune shiru babu wanda ya yi magana Daidai lokacin Dr James ya shigo ta kofar office ɗinsa, dikkansu daga office ɗinsu suna iya shigowa cikin wajen. So ya shigo hannunsa rike da tarin takardun. Saman sofa kusa da su ya zauna tare da ajiye files ɗin a kusa da shi. Natsuwa suka yi dik suka bashi hankalinsu. Wani document ya ɗauko tare buɗe files ɗin, glass na face ɗinsa ya gyara kafin ya ce. "Information daga ƙasar AVARIS. A dikkan government hospital na 30 states da kasar Avaris take da shi mun gama rarraba files ɗin nan, a cikin ƙasa da 24 hours mun samu mahaifar mata sosai daga asibitoci sama da 20".

Dr Mark ne ya amsa da cewa. "Fin haka ma zamu samu, saboda kowa yana cikin yunwa da buƙatar kuɗi, kowa burinsa ya yi kuɗi, kunga a irin wannan yanayi ko da maginyata basu sayar dan ra'ayin kansu ba likitocin zasu cire masu ba tare da yardansu ko saninsu ba, dan 80 million ba karamin kuɗi ba!". A natse ya yi maganar, ya faɗa yana sipping drink ɗinsa.

Dr Kamal ne ya ce. "Yunwa ya cinye kowa a ƙasar na AVARIS ba dole su sayar ba, gwamnatin AVARIS bata son biyan ma'aikatan lafiyar government hospital ɗinta albashinsu yadda yakamata, basa son sauke hakkinsu, kasar ga yunwa da wahala dole wasu likutocin su yarda sayar ko majinyata basu sani ba". Cikin kwarewa suke magana, one after the other, yadda zaku san ilimi ya ratsa ƙwaƙwalwalensu matuƙa.

Bari in maku karin haske dan zaku fi gane maganganunsu, sayan mahaifan mata suke yi da kimanin kuɗi 80 million a kuɗin Nigeria, to ni kuɗin Nigeria na sani shiyasa da su nine kwatance, kuma shi masu karatu zasu fi ganewa.......😌

To sun shigar da buƙatarsu ta hanyar turawa manyan asibitocin gwammanati na kasar Avaris takarda, wani Minister suka baiwa wannan kwangila da makuɗan miliyoyin daloli, shi kuma ya shiga asibiticin gwamnati ya yi zama da manyan gurɓatattun likitoci ya faɗa masu buƙatarsa, su kuwa take suka yi na'am sun ji miliyoyi.

Dr James da kansa ya kirkiro wani magani da ya sanyawa project ɗin suna da silent killer, wanna magani ya bawa wannan minister dan a rabawa gurɓatattun manyan likitocin asibitocin, zasu baiwa mata a matsayin wani magani na karin lafiya, ko idan mace ta zo ta ce tana ciwon ciki yayin period sai su bata shi a matsayin maganin warkar da ciwon cikin, idan kin sha zaki yi ta fama da ciwon cikin ne, amma fa a farko in kin sha zaki ji saukin ciwon cikin, daga baya bayan kwanaki sabon ciwon ciki zai ɓallo maki mai zafi, da kin zo asibiti zasu ce maki mahaifarki ta samu matsala sai dai a yanke! Ba zaki kawo komai a ranki ba, zaki aminta a cire maki mahaifarki saboda a rabaki da ciwo.

Ministern da aka baiwa wannan kwamgila a kan Miliyan tamanin aka sayi kowani mahaifa a wajensa, shi kuma ya cewa likitoci in sun samu mai sayar da mahaifar ya saya miliyan hamsin, su kuma Dr É—in suna saye miliyan 30 idan kin yarda zaki sayar, kasuwanci kan kasuwanci kuke ji.

To wasu matan fa mazansu ake magana da su, wani da ya kawo matarsa asibiti za'a jasa jefe, a shirya a kuma kwaɗaita mashi kuɗin, idan likitocin sun ga ɗan kauyene ma basa ce mashi saya zasu yi, sai su ce ciwo ne, ya aminta a cire maki, wani mijin kuma azzalumi ne, bai gama sauke maki hakkinki na aure ba, zai cutar dake ya sayar maki da mahaifa ba tare da kin sani ba, idan ya shirya da likitocin kan zai sayar masu zai karɓo wannan maganin ya baki, da kinsa zaki fara ciwon ciki, idan zai kaiki asibiti wannan asibitin da suka gama cinikin zai kai, already ya karɓi kuɗin mahaifarki 30 million baki sani ba, sun san komai Doctors ɗin, kina zuwa zaace aiki za'ayi maki, daga nan a cire maki mahaifa ba tare da kin sani ba, sai dai ki ga kin daina haihuwa, kuma ba zai taɓa barinki ki je wani asibitin ba, sai dai ya dinga cewa ki je wannan asibitin da aka maki aiki sun fi kwararrun likitoci, dan bakinsu ɗaya.

Ya ilahi, sun fi yi wa matan kauye da basu san komai ba hakan, kun san dai manya matan masu kuɗi basa zuwa asibitocin gwannati ai, a kan mu talakawa abin yake karewa, babu abin da ya fi taɓa mun zuciya irin mazan dake zaluntar matansu su sayar masu da mahaifa ba da izininsu ba, ya ilahi, wlh da babu lahira akwai matsala, amma Alhamdulillahi tin da akwai hisabi, amma bin da ciwo.

Meyasa yanzu abu kaÉ—an mahaifar mace ya samu matsala? Why? Meyasa zata haihu ace ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai a mata Cs? Why? Meyasa ciwon da bai zo a da ba sai yanzu za'a ce mahaifarta ta lalace ba zata sake haihuwa ba gara a cire mata? Meyasa dikka hakan sai a kanmu mata? Me laifinmu? Wani irin cutarwa ne wannan?.

Idan an samu miji mara imani ya sayar dana matarsa bata sani ba, wani ma yaya ne mara imani yake sayarwa kanwarsa, matan kauye basu san komai ba haka za'a cutar da su daga zuwa asibiti, ace basu da lafiya sai an masu aiki, daga nan a sace masu mahaifa, AVARIS suna cikin musifa babba, Æ´an mata ma ba tsira suka yi ba, wani saurayin mataccen zuciya ne da shi, ya yaudareki ya kaiki a cire maki mahaifa, ya sayar ya yi kuÉ—i ya gudu ya barki ya nemi wata budurwar wacce take da mahaifar da zata haifa mashi yara in sun yi aure! Ya ilahil alamina, sabuwar musifar dake danno kai a AVARIS kenan.

Jama'a ku ji tsoron ALLAH, maza ku tina akwai lahira, akwai mutuwa, meyasa zaku sayar masu da abin da ALLAH ne ya basu ba ku ba? Meyasa zaku cutar da rayuwarsu ta haka? Mata masu sayarwa da kansu ku ji tsoron ALLAH, ku tuna cewa ALLAHN da ya baku a ranar lahira sai ya tambayeku komai da ya baku, wani amsa zaki bawa UBANGIJINKI ranar lahira? Dama ya baki dan ki sayar ne? Kin san me za'ayi da mahaifar ne da kike sayarwa? KuÉ—in banza mai karewa, baki san kuÉ—in haram bashi da albarka ba ko? Maza! Maza! Maza!!.
Chapter 94 · 0% Book details