Sashe 114
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karɓar wukar ogan nasu ya yi tare da nufar in da su Leo suke, dab kusa da su ya tsaya tare da zaro wukar daga kotarta, ya buɗe hannayensa yana fasa murya wajen cewa. "Dole in sha jininku, kuma nasan jinin naku zai yi daɗi, amma na ji takaicin cewa zan kasheku fa, kuna da kyau sosai, yanzu wannan kyan kawai zai tafi a banza? Gaku matasa da ku! Na tabbata baku bar baya ba, baku bar iri ba, kash wannan abu bai mun daɗi ba".
Da yake hannayensu zuwa cikinsu ne a ɗaure sai Leo ya ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tare da yin fito mai kamar sauti kafin ya ce. "Kana jan lokacinka fa, bana son ka haura lokacin da na ɗeba maka". Da harshen turanci suke magana.
Wani irin dariyar samudawa mutumin ya yi kafin ya kara taku É—aya, ya danki golden white hair É—in Leo tare da É—aga kansa sama. "Kisan da zan yi maka sai ya fi na brother É—inka munu"....... Nisawa Leo ya yi tare da yin fito da karfi. Unexpected harbi ne ya ratso cikin wajen kai tsaye sai damtsen hannun ogan nasu.
Wani irin ihu ya kurma tare da ja da haya ya saki wukar hannunsa yana dafe in da ake harbesa. Take dikka Æ´an ta'addan suka haÉ—e kai tare da É—aga bindigunsu suna Æ´an waige-waige. Leo ne cikin É—aga murya ya ce. "Fire!"....... Haba take wajen ta kaure da harbi.
Watau dama da gangan ya miƙa wuya, sun yi ƙoƙarin sanin in da ainahin tsakiyar sansanin ƴan ta'addan yake da kuma hanyar da za'a bi a je wajen, amma sun rasa ganewa, shi ne suka shigo bakin sansanin nasu, Leo ya shirya cewa shi zai je, idan suka kama shi sai sojojinsu su bi bayansu su ga hanyar da suka bi da su, daga nan sai su dawo su yi shirin gagarumin yaki su yi wa ƴan ta'addan zobe lokaci guda kawai su kamasu, kada ku manta a ƙaida an ce su kama ƴan ta'addan ne ba su kashesu ba, shiyasa suka harbi ogan nasu a wajen dantsen hannu in da ba zai mutu ba.
Sosai Noor ya ji tsoron rasa Leo a lokacin da Leo ɗin ya ce zai je ya miƙa wuya su kamasa, sai ya ce ba zai yarda ba sai dai su tafi tare, shiyasa kuka ga sun shigo su biyu kawai, tarko suka kafa ƴan ta'addan, ga shi yanzu sun kamasu a sauƙaƙe.
Kafin ƴan ta'addan su farga su Zaynish sun kewayesu sun kuma matso izuwa cikin sansanin nasu. Vash ne ya yi shahadar zuwa da gudu zai nufi in da su Leo suke dan ya kwance unexpected aka harbesa. ALLAH sarki burinsa ya zo ya kwancesu kada ƴan ta'addan su fusata su harbesu, ashe shi ne da rabon wahala, bullet bai taɓa shi a in da zai mutu ba, dan a wajen cinya ya same shi.
Faɗuwa ƙasa a wajen ya yi. Zaynish ne ya saita kullin igiyar da aka ɗaure Leo ya harbeta take ta tarwatse, hakan yasa Leo ya samu damar zame hannunsa. A gaggauce ya miƙe ya fara ƙoƙarin kwance Noor. Zaynish ya tsaya masu sosai, dan ya rike wuta ta saitinsu, yaki bada sararin ƴan ta'addan su iso in da suke bare su kashesu, da ya ga motsi ta kusa da su zai yi harbi, har Leo ya samu dama ya miƙe ya kwance Noor.
Suna miƙewa a tare Leo da Noor ɗin suka ɗaga hannu suka yi wa Zaynish jinjina, dan ya yi namijin kokari, musamman yadda ya tsaya masu ya ki bada sarari ƴan ta'addan su samu damar kashesu.
Suna sauke hannunsa daga jinjinawa Zaysh Noor ya danna da gudu izuwa in da Vash yake kwance, dan sun fi kusa. Dai juyi yake yi saboda zafi. Hannu Noor yasa ya ɗaukesa cak ya ɗaura a bayan wuyansa, ya kuma ɗauki bindigarsa dake yashe a ƙasa da ɗayan hannunsa, ya harbawa Leo bindigar Vash ɗin, sannan da gudu ya nufi in da Zaysh yake tsaye, yana da ɗan nisa da su.
Zaysh ya tsaya mashi, ya yi ƙoƙarin hana a kawo mashi hari ta baya da bindigarsa, Leo ma da ya caɓe bindigar Vash sai ya tarewa Noor ɗin samun damar kawo mashi harin baya.
Da gudu ya fitar da Vash waje zuwa in da sauran sojijinsu suke, bindiga ya karɓa wajensu Unays da jakar bullet ya nufo ciki babu ko tsoro, shi ba zai iya barin Leo shi kaɗai da mutanen nan ba, shiyasa ya nufi dawowa ciki. Cikin zafa Zaynish ya biyosa suka dawo.
Musayar wuta suka fara yi da gasken-gaske, dikkansu sojojin babu sa ran komawa a raye a cikin zuƙatansu, idan sun mutu ma dama hakance a ransu cewa in su fito ba lallai su koma ba.
Da ƴan ta'addan suka ji wuya sai suka fara dannawa a guje suna kutsawa cikin daji. Ai rakasu a guje sojijin suka, sun sha alwashin ba zasu bar ko ɗaya ya gudu ba, dik wanda suka gani sai su harbesa a ƙafa su wuce sauran sojojin dake biye dasu kuma suna tattarasu waje guda.
Leo, Noor and Zaynish babu É—aga kafa suka raka Æ´an ta'addan a guje, sun jajirce wajen ganin sun kawo good result a Mission É—insu na farko. Wani irin yaki suke yi mai salo na É—aukar hankali su ukun nan, kamar ba mutane ba.
A garin bin ƴan ta'addan ne suka shiga wajen wani sunkurun daji, fili ne dake cunkushe da bishiyoyi masu cikar ganyayyaki, sun sanya wajen ya yi duhu, ga tarin maɓoya sosai, wanna waje ake cewa fidda ran fita idan ka shiga.
Ko tsoro basu ji ba suka tsaya a tsakiyar wajen suna duba ta ina ƴan ta'adda suka yi. Zaynish ya buɗe bututun bindigarsa yana duba bullet nawa ya rage masu. Fito da karfi Leo ya yi wanda hakan yasa suka raba kansu da gudun gaske cikin zafin nama. Suna raba kansu bullet ya wuce a tsakaninsu. Ai da gudun gaske Noor ya juyo ya nufo su Zaynish, kamar Zaysh ya sani ya ɗan duƙa mashi Noor ya taka shoulder ɗinsa yakara tsawo tare da ɗaga bindigarsa sama ya yi harbi uku a jere izuwa saman bishiyar dake ta kusa da su.
Yana harbin ya faɗi ƙasa cikin ciyayi, akwai su da saiti, ƴan ta'adda ukun dake kan itacen dik ya harbesu a kai sun mutu. Kansa Zaysh ya yi dan ya duba faɗuwar nan da ya yi bai ji ciwo ba ko. Sai dai kafin ya isa ga Noor Leo ya yi tsalle ya rungumesa suka faɗa ƙasa tare, a take bullets a gere guda biyar suka wucesu fiw.
Cikin zafa suka wani irin mike a tare, sai suka yi deciding da su nemi wajen ɓuya suma, saboda sun gano ƴan ta'addan da suka ɓuya a nan suna dayawa, dole ayi yakin sunkuru yanzu.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥ï¸
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
STEP 1🔥
2025-12-3.🔥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E_____________ 36 & 37

A tare suka ɓuya bayan wasu sunkurun ciyayi, suka tsaya shiru ko numfashi basa yi suna son gano ƴan ta'addan. Ai wannan shirun da suka yi ba ƙaramin taimaka masu ya yi ba, domin kuwa sun jiyo numfarfashi da dama a maɓoyan ƴan ta'addan, wasu ma sai haki suke yi, kun san na faɗa maku sai ka sa karfi zaka iya harbi da bindiga, dan yadda bullet ɗin yake fita da karfi jijjiga mutun yake yi, sun sha harbi sun jijjiga shi ne suke ta haki sama-sama.
Can su Leo suka ji wasu muryoyi a ɗan nesa da su suna faɗin. "Nima bullet ɗina dikka ya ƙare". Ɗayan ma ya ce. "Ai dikkanmu babu mai sauran bullet a cikinmu, kawai mu fito mu yi gaba da gaba da su".
Kallon juna su ukun suka yi, Noor ne ya ce. "Dama kwana biyun ban watsa jini ba, bari mu yi wrestling da su mu gani". Ya kai karshe tare da sauke bindigarsa ƙasa, ya yi mata ma'ajiya a wajen, sannan ya miƙe. Dikkansu ma'ajiya suka yi wa bindigunsu suka ɓoyesu, sannan suka mimmiƙe suka fito tsakiyar wajen.
Suna fitowa Æ´an ta'addan ma suka fara fitowa, sun fi mutum 25 suka fito. Gyara tsayuwa su ukun suka yi, Leo ne ya ce masu. "Dik ku tabbatar idan kun masu duka É—aya ba kari!"........ Noor ya amsa da. "Angama"....... Watau matasan sojoji ukun nan suna jin jininsu a tafashe yake, suna ji da lafiya da zafin jini.
Zobe Æ´an ta'addan suka matso suka yi masu, kan kace me suka fara wrestling É—in da suka ce a kansu, wai waÉ—an da kayan maye ya gama cinye masu quality É—in jiki ne zasu gwabza da sojojin AZURE, sojojin AZURE É—in ma sabbin jini yayen bar two, ai ko Æ´an bar one in suka yi wa waÉ—an nan duka É—aya ba tashi bare Æ´an bar two.
Sosai suka gwabza faɗa, Noor kam da mai hali baya canzawa ma ai abin wasa ya mayar da su. Da ya kaiwa wani ɗan ta'addan da ya zo zai kamasa da faɗa mari sai da ya ji ƙamshin lahira, sharara mashi mari ya yi yana faɗin. "Ɗan banza dubeka dik yunwa ta kusa hallaka shi ne zaka zo in karisaka ko? Dik kayan maye ya cinye maka ƙoda da huhu".
Ai ya ji marin maza, sai da ya yi wani irin tangal-tangal kamar zai faɗi sannan ya tsaya da kafarsa. Yana ƙoƙarin ɗagowa Noor ya kama wuyansa da hannu ɗaya, ya jasa izuwa wajen bishiya, da karfi ya maka kansa da jikin bishiyan. Noor sai shirin ALLAH, sai ya ɗaukesu dik kamar abin wasa, dukan mata yake yi masu, ya ce idan ya ce zai masu dukan sojojin AZURE dik zasu mutu ba'a mai da su barrack ba.