← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 227

Sashe 123

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

One thing about mutanen Ring Of Power rana suke bautawa ba ALLAH ba, so ba musulmai bane, harta kakan Lion ba musulmi bane, yanzu haka basu san Lion Musulmi bane da abin ya tsananta, shi daddyn Lion ALLAH ne ma ya tsaga da rabon musuluntarsa, ALLAH ya tsaga bai da rabon wahala, da ya bar masarautar ne ya samu damar musulunta ta dalilin mom ɗin su Lion ɗin, kun san ba zai auri musulma yana matsayin mai bautar rana ba ko? To dalilinsa kenan na musulunta a farko, ita ta koya mashi komai na addini kafin addinin ta tsara shi ya shiga neman ilimi gadan-gadan, dan haka family ɗin Lion masu bautawa rana ne, kuma basu san shi musulmi bane! Bama su san daddynsa ma ya musulunta ba, and Lion bai taɓa zuwa masarautar ya kwana ba, idan ya yi wuta ne ya yi awa biyu a ciki ya koma, da sun san Musulmi ne ai da bala'in sai ya fi haka, rikicin ba zata kare ba!.

Tin da motocinsu suka shigo dik wani mai rai ya natsu tsit, kowa ya shiga taitayinsa, dan ba'a taɓa wanda ya taɓa fuskantar Iron Sovereign ya faɗa mashi magana kai tsaye ba sai Lion, ko daddynsa a lokacin da ya yi taurin kai wlh baya fuskantar baban nasa gaba da gaba ya faɗi magana, sai dai ya faɗa a bayansa a mayar mashi.

Amma shi Lion ido cikin ido ya dubesa ya ce. "Da in durkusa in baka hakuri gwara na kashe kaina! Kuma ni ban ce maka ina da buƙatar a karɓeni a matsayin magaji ba! Bani da buƙatar sarauta a rayuwata, haka kuma bani da buƙatar family!". Wannan magana ta yi matuƙar gigita Iron Sovereign, domin babu wanda ya taɓa kallon cikin idanunsa ya bashi martani, Lion ne na farko, kuma daga kansa baa sake samun wanda ya yi hakan ba!

To wannan dalilin yasa kowa yake shakkar Lion, idan ya zo waje dik wani halitta mai rai natsuwa yake yi. Suna parking na motocin aka buɗe mashi kofa, take busa ya karaɗe ko'ina a cikin masarautar, The Crown Sentinel ya iso, ta ko'ina taken girma ake mashi, dik wasu bayi da kuyangu zubewa ƙasa suke yi a in da suke suna bashi hanya har sai ya wuce.

Wlh The Iron Sovereign yana mugun son Lion, kawai ɗan banzan girman kansu na gado ne yasa yake ganin ba zai iya janye batun sai Lion ya bashi hakuri zai karɓesa matsayin Crown Sentinel ba, amma da ya ji ya zo ba ƙaramin daɗi ya ji ba, har da leƙasa ta view ɗin ɗakinsa saboda yana cikin room ɗinsa can saman bene mafi tsawo a masarautar.

Kai tsaye babban sashen masarautar Lion ya nufa, in da uwar gida kuma amarya take kenan, kuma ita kaÉ—ai ce matar sarkin, dan su a al'adarsu mace É—aya suke aure, shiyasa yake da ita kaÉ—ai.

Tin daga nesa ake zube gwiwowi a kasa ake kwasar gaisuwa, idan sun durkusa ma sai sun kifa kansu a ƙasa, al'ada ce haka suke yi wa Iron Sovereign ɗin nasu, so shi ma Lion kamar haka suke girmama shi. Kai tsaye cikin katafaren ginin ya shiga.

Dik masu gadi a wajen sai da suka zube ƙasa, tare da guards ɗinsa suka shige, sai da ya zo kofar babban parlonsu ya ɗagawa guards ɗin hannu alamar su tsaya. Tsayawa suka yi shikuma ya wuce ciki.

Yana shigowa wasu mata suka fara buɗe shi da hayaki wai na addu'ar da aka yo daga rana, Lion zai yi albarka. Ai yana ɗago idanu gabaɗaya matan suka dare suka bashi hanya, wasu har da faɗuwa a garin gudu, ƴan hayakin ƙaniya, ashe wargima waje yake samu, har da wani munafikin fure a kan tiren hayakin da wani munafikin tiraren wuta na tsinke.

Dama sai da matan suka ce su suna tsoron yi mashi wannan hayaki, amma granny ta kafe lallai su yi mashi ai ita ta ce. Wai tana jin kamar ba zata sake ganinsa bane, shiyasa tasa a nema mashi rahama daga rana, ai mashi addu'a, dan tana ganin kamar ganin karshe zata yi mashi.

Ta tsufa sosai da sosai, komai yi mata ake yi, zata kai 65 years a duniya, to tana jin kamar lokacin tashin ruhinta sama izuwa wajen hasken ranar da suke bautawa ya kusa, dan su basu yarda da akwai mutuwa ba, sun ce tashi sama ruhunsu yake yi, ya shiga cikin hasken rana ya zauna, to kunga wanda ya mutu baya dawowa bare ya dawo ya basu labarin ba haka abin yake ba sun canza salo da dabara, and su a nan gawa konawa ake yi, hasa binnewa, idan ruhu ya tashi sama ya shiga hasken rana, sai shi kuma gawa a konesa a hure tokar ta tabi iska.

Kafin Lion ya yi magana ko mutum ɗaya bata rage a cikin room ɗin ba, dik sun fice da gudu. Takowa ya yi izuwa gaban gadon da granny ɗin nasu take kwance. A gefe ya zauna tare da yin ƙasa da kai. Da sauri dik kuyangun dake hidimta mata a cikin ɗakin suka nufi waje, dattijuwar tana ƙudundune cikin bargo kato na alfarma, ga king bed ɗin nata ya yi wani irin masifaffen haɗuwa.

Ɗakin haske tankar tamkar tsakiyar rana suke saboda kwayayyen chandeliers na alfarma dake haske ko'ina. Shiru bai iya yin magana ba, yana dai duke da kai, umarnin daddynsa kawai yake bi, ba dan haka ba shi ba zai zo wannan masarauta ba, ba zai sake zuwa kusa da mace ba, amma daddynsa ya ce ya ɗauki granny a matsayin shi ne, idan ya saɓa mata tamkar shi ya saɓawa.

Amma fa dik da wanna wasiya baya wani bi, yanzu haka sai da tai mashi kira ya fi sau goma, yaki ɗagawa ma bare ya ji menene, sai da ta sanya aka rubuta mashi saƙon tana gadon jinya, sannan ne ya yi reply da yana zuwa, tin last month aka yi hakan sai yau yaga damar zuwa ɗan duniya.

Jin shirun ya yi yawa ne yasa ta ce. "Edward Harrison ba zaka mun magana bane yau ma?"..... Da kyar maganarta yake fita. Edward Harrison shi ne sunansa da suna sanya mashi, Harrison sunan babansa ne, basu san ya koma Muhammad ba.

Lion da iskanci yake, akwai wata shekara da ya taɓa zuwa, tin da ya zo har ya ɗauki awa ɗaya a zaune ya koma bai yi wa kowa magana ba har dattijuwan, kuma tin daga wannan zuwa bai sake ba sai yau, shi ne take tambayar ko yau ma ba zata samu damar yai mata magana bane.

Shiru babu alamar zai amsa mata, ganin haka yasa ta sake cewa. "Edward ina ganin kamar lokacin É—aukakata izuwa sama ya yi, shi ne yasa na ce a kira mun kai". Ta dakata saboda yanayin jikin bata iya magana mai tsawo. Babu alamar Lion zai tanka mata bawan ALLAHN nan, ko motsi bai yi ba.

"Idan ruhunana ya ɗaukaka zuwa sama Edward kai nike son ka zo ka ƙona gangar jikina, ka sheke tokata mai daraja". Ta sake yin shiru cike da sa ran zata ji muryansa, amma ina bai motsa ba.
"Edward iyayenka Harrison da Robertson kawai dudu (ranan da suke bautawa suke kira da dudu) ya bani, yanzu kuma kai kaÉ—ai suka bar mun, Edward ka yi magana mana in ji daÉ—i, ina jin kamar Harrison ne yake magana idan ka yi, ka bani kalamanka na karshe".

"Zan tafi". Shi ne kawai abin da ya furta tare da miƙewa tsaye...... "Edward please ka fuskanci kakanka ku sasanta, ka mashi abin da.....". Kasa karisawa ta yi saboda ɗago idanun da ya yi a kanta, kara ɗaure fuska tamau ya yi, bai sake yin magana ba ya juya ya fita abinsa.

Bai sake bi ta kan kowa ba, ya wuce ya shiga mota dan komawa, Iron Sovereign yana ta faman leƙansa ta view, yana gani Lion ya koma sannu bata haɗasu ba. Ko yaushe wannan gaba zata zo karshe kuma? Kowa sai ji da girman kai da zafin rai game da taurin zuciya. Wannan kenan a ɓangaren Lion, to mu leƙa ɓangarensu Seraphina.

Har cikin gida Rimsha da Faryan suka ni Seraphina, sai murna take yi, ta kaisu wajen Madam suka gaisa, Faryan ya zauna a parlo yana ta bin Seraphina da ido, dik in ta gifta sai ya ganta, while ita kuwa sun shige É—aki da Rimsha, sai kai komo take yi tana É—aukiwa Rimsha kayan cima.

Yau wunin farinciki suka karisa, sai ana kiran mangrib Faryan ya ce Rimsha ta zo su wuce gida, tamkar zata yi kuka ta ce. "Uncle yaushe zamu sake zuwa?". Shi ma da yake ya ga abin da zuciya ke so sai ya ce. "Ai bamu da nisa, dan haka zan dinga kawoki". Haba take ta fara murna.

Dik abin da suke yi Aryan yana zaune gaban computer yana kallonsu, dik kalle mashi baby Cherry Bloom da Faryan yake yana ganinsa, kishi ya gama tsumasa, jikinsa har wani tsuma yi, ga shi ba wani dressing na suturta jiki sosai take yi ba, ya dinga kiran wayarta dan ya faÉ—a mata ta sanya wasu kayan, amma tana can an samu Rimsha wayar ma bata san in da yake ba.

Bai tashi shiga damuwa ba sai da ya ji Rimsha ta ce da Seraphina su je cikin toilet su yi wanka, a boarding school haka suke yi, tare suke wanka.

Wannan abin ya yi matuƙar tayar mashi da hankali, jikinsa har wani tsuma yake yi, haka yana ji yana gani suka shiga toilet, babban abin da ya kara kiɗima shi ma yadda suka cire kaya a tsakar ɗakin, kuma ko kunyar juna basu ba, tambayar kansa ya fara yi menene amfanin boarding school ne ma a rayuwar ɗiya mace? Amsar da ya rasa kenan, amsar da ni kaina na rasa kenan, a zamanin yanzun nan menene amfanin boarding ga ɗiya mace, yadda zamani ta lalace, hmmm!.
Chapter 123 · 0% Book details