← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 227

Sashe 141

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cigaba guru yai da cewa. "Aryan, bayan gold ma akwai manyan ma'adanai kamarsu tantalite wanda da shi ake yin capacitors a wayoyi, taba da laptops, akwai Tin wanda da shi akeyin solder, kayan lantarki, kwalaye masu hana abu yin tsatsa, suna da columbite da shi akeyin kayan jirgin sama, roba mai jure zafi, alloy, amma yau an wayi gari Avaris bata da jirage guda 10 masu kyau na kanta, ko in ce na ƴan ƙasa, sai kame-kame, idan gwamnatin ƙasar ma zata sayi jirgi sai second hand, idan kaga jirgi mai kyau a Avaris to na ƴan kasuwa ne bana gwamnatin ƙasar ba, ga shi kuma suna da columbite da suke sayarwa ƙasashen dake son cigaba suna haɗa jiragen sama suna keta hazo!".

Ya ja dogon numfashi kafin ya cigaba da cewa. "Suna da iron ore wanda da shi ake yin karafuna, siminti, injuna da ginin layin dogo, amma yau an wayi gari Avaria dik wani inji mai kyau idan ka gani daga wajen Avaris aka saya aka shigo masu dashi, basu da kamfanonin haɗa dik waɗan nan, sai dai a ɗebi ma'adanan a sayarwa waje, ƴan ƙasan dik basu san da akwai wannan ba! Baya ga shi akwai lead zinc, akwai lithium, gemstones, sapphire, garnet, amethyst, tourmaline, sannan suna ma da coal dayawa, musamman arewa maso gabas na ƙasar".

(Gombewa how far? A Nigeria kuma nasan kuna da arzikin coal sosai! Hakane ko? Ba iya Avaris ba, kuma kuzo ku faɗa mun me kuke yi da naku? Gombawa daku nike fa, Gombe ikon God, kuma kuna da tatalin arzikin ƙasa dayawa fa, to ALLAH yasa ya amfaneku idan kun gano kuna da shi!.)

Cigaba guru yai da cewa. "Akwai limestone wanda ake siminti da shi, suna da gypsum, kaolin, bentonite, manganese, phosphate, granite, dolomite, quartz, copper, nickel, graphite, asbestos, uwa uba suna da uranium wanda da shi ake haɗa wutar lantarki, nuclear, nuclear da manyan ƙasashe ke ta faman rikici a kansa, wanda dik ƙasar da ta mallaketa ake mahaukacin tsoronta, amma yau an wayi gari abin da ake haɗata yana a Avaris, amma Avaris bata da ishasshen wutar lantarki ma bare aje kan nuclear wanda kun sani ko family nuclear basu da shi bare asalin nuclear wanda zai iya tashin ƙasa gabaɗaya, abin taƙaici sai dai wasu can su zo su masu dabara su kwashi uranium a fita da shi, su je su wadata ƙasashensu da wutar lantarki, su kuma wadata ta da makamai da suke dawowa su sayarwa Avaris ɗin".

Lion ya tari nunfashinsa da cewa. "Kuma makaman da suke sayarwa sojojin Avaris ɗin ai very local ne! Basa taɓa sayar masu masu inganci, alhalin daga ƙasarsu suka kwashi uranium ɗin". Ya kai karshe yana sunkuyar da kai, tin ɗazun shi da Vir sun yi shiru ne saboda tafarfasar da zuƙatansu yake yi, idan suka ce zasu buɗe baki zasu iya haɗiyar zuciya su mutu tsabar takaicin abin da ake yi wa al'umma!.

(To mutanen Adamawa state sannunku, na ce ba a Nigeria kaf na ji ku ne kuke da arzikin uranium a ƙarƙashin ƙasarku kamar na Avaris, na ce fatan kuna yin abin da ya dace da shi ko? Fatan kun san da shi kuma kuna ƙoƙarin ganin ko an sayar a gyara maku gari da kuɗin ko?😭💔)

Guru ya cigaba da cewa. "Suna da crude oil, watau ɗanyen man fetir wanda a cikinsa ake cire maku su gas da sauransu, baya ga haka kuma suna da natural gas, Iskar gas, suna da bitumen, glass sand, kaolin, gypsum, granite, laterite, manganese, talc, wolframite, lignite". Ya kai karshe yana girgiza kai, takaici tamkar zai haɗiyi zuciya ya mutu, ace dikka wannan uban tattalin arzikin, kuma dik masu mugun tsada da duniya take nema, amma ace yunwa kawai ta gigita ƴan ƙasar, basu da abin da zasu ci, alhalin da kuɗin uranium da zasu dinga sayarwa ƙasashen waje kawai zai wadaci ƴan ƙasan dik abin da suke so, sai dai ina........
Abin mamaki da takaici sai su tara kuɗin da har ɗan auta a zuriarsu ya girma ya kare rayuwansa da zuri'arsa kuɗin da suka tara rabi bai ƙare ba, kuɗin da ɗan adam bai isa ya karan da shi ba, kuma kullum ƙara sata suke yi, sai ka rasa me zasu yi da kuɗin! Ka rasa ina zasu kai son duniyar da zamu tafi mu barta, duniyar da tamkar wuni muka zo, babban abin takaici sai su kai kuɗaɗɗen kasashen waje su ajiye, ƙasar da suka ajiye kuɗin ta yi ta juya kuɗin tana amfanuwa, su nan suna sake satar wasu su fitar, wani ma yawan kadarorinsa dake wasu ƙasashe wlh har ya mutu ba'a san in da suke ba, wani ma tsabar ya sata ya sata idan ya sayi wasu kadarori a ƙasashe yana mancewa da wasu su salwanta, wani kuma ya mutu iyalansa ma basu san yana da kuɗi a ƙasa gaza ba! Sun dai sata sun fitar, ya ALLAH ka dubemu da idanun rahma!!.

Aryan da jikinsa har wani tsuma yake yi saboda takaici ne ya ce. "Dik wannan tattalin arzikin da ALLAH ya mallaka masu amma ƴan ƙasar basu da wani abin yi, sun zauna basu da aiki kullum sai dai ka gansu a media suna faɗar addini, aƙida ko ƙabilanci, ko yunwar cikinsu basu iya gama maganinta ba, kaga matashi har matashi, mai ji da rai da lafiya, madaki karti, sai ya shiga ɗaki ya saita camera ya hau zagin wata ko shiga faɗar da bata shafesu ba, wasu matasan da basu san ciwon kansu ba ma sai ka samesu da musayar yawu a media a kan kwallon kafa, ko faɗa da mata"..

Wani irin numfashi Vir ya ja tare da saukewa a hankali, ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa na takaici kafin ya ce. "An kashe masu zuƙata ne, an dasa masu tsoro, an kashesu da yunwa, ai babban makaman da suka rike shi ne rikita al'umma da yunwa, kana jin yunwa kowani irin aiki aka baka zaka yi dan ka ci abinci, sannan wannan tsoro da aka dasa masu ba zai taɓa barinsu ba, and kada ku manta WS bata ɗaura shugaban da ƴan ƙasa suka fi karfinsa!!".

Aryan ya amsa da. "Ai idan ba ga ALLAH mutanen Avaris suka koma ba wlh babu abin da suka isa yi wa shugabanninsu! Saboda WS bata ɗaura shugaban da ƴan ƙasa zasu iya fito na fito da shi, suna gani ana zalunntarsu amma ba zasu iya yin komai ba, sai dai su yi ta banbami suna cika baki a media!".

Iska mai zafin gaske Lion ya furzar daga bakinsa, wai yana matsayin leader na IRON FIST kuma ace a ƙasarsa, ƙasar mahaifinsa ake wannan ɓarna? Ya ALLAH, shi kam zai iya haɗiyar zuciya saboda takaici, lallai lokacin yin aiki ya yi, lokacin kawo karshen dik wani azzalumi ya yi. Dama ina baku manta ba IRON FIST sun tafi hutu ai! Tin da suka kashe ministar ba sun ce sai bayan shekara ɗaya ko biyu zasu sake yin aiki ba? To shiyasa kuka ji sun yi shiru suna ta bincike kawai, yanzu lokacin komawa bakin aiki da gaske ya yi, Seraphina zata rage ganin daddy Aryan, dama san suna hutu ne yasa yake da ishasshen lokaci!.

Da kyar Lion ya iya cewa. "Gano WS babban abu ne, aiki ne ma matuƙar wahala, amma zamu tsokanesu ta yadda da kansu zasu bayyana kansu!"..... Kallon juna suka yi, basu gane in da Lion ya dosa ba, suna son karin bayani, hakika sun san gano WS ba abu bane mai sauki, dan WS ɗin na farko ba mulki suke yi, basu a cikin siyasa, su mutane ne dake rayuwa kaman sauran mutane, kila ma suna kusa da kai a halin yanzu, suna rayuwa very simple, amma suke naɗa masu mulki, abin mamaki, su fa basa son hawa gujerar mulki, da suna son hawa da sun hau, su dai suna gefe, amma dik wata kafunci da zalunci suke shiryasa, idan kuna jin ana faɗin masu naɗa masu mulki to su ne.

Tsabar ɓadda kama ma suna tafiya ba security, ba ɗan sanda, babu sojoji, ba zaku taɓa tinanin su bane, kuma suna ko'ina, kunga kuwa kamasu abu ne mai matuƙar wahala, dik duniya harta shugabannin da suke ɗaurawa a kan mulki babu wanda yasan kamanninsu, kai haɗarin mutanen nan ya zarce yadda kuke tinani, su ne mutanen da ko kana kan mulki in baka bi umarninsu ba a cikin ƙasa da 5 mins zasu iya kasheka, baka isa ka guje masu ba, suna koina, suna da ido dake ganinka a dik in da kake, wlh haɗarinsu ya fi na nuclear, sai dai mu ce ALLAH ya karemu ya kawo mana karshen dikkan wasu azzalumai!

Aryan da ya fi kowannensu fahimtar Lion ne ya ce. "Kana nufin siyasar Avaris zamu shiga?"....... Vir ya amsa da. "Ta hakance kawai zamu tsokanesu su bayyana kansu, dan a halin da ake ciki ka kuskura ko magana ka yi a kan shuwagabannin Avaris ɓatar da mutum ake yi, idan kana da rabon rayuwa a daka maka warning a sanya maka tsoro!".

Jinjina kai dikkansu suka yi, dan kuwa haka ne, suna gani a media ta kasar, suna bibiyar dik wani motsin Avaris sosai......... "Ba zamu shiga siyasar Avaris ba, amma dik wani gurɓatacce shugaba zamu tugesa, zamu farkar da matasan Avaris mu cire masu tsoro, hakan zai yi matuƙar tayarwa da ws hankali, dole zasu nememu da kansu dan su ga bayanmu! Kunga daga nan zamu kamasu a sauƙaƙe". Cewar Lion ɗan baiwa mai basira da wayon kama azzalumai, kai Lion ne ya cancanci sunan Smart fa!.

Jinjina kai suka yi, lallai haka ne, wanna shawara ta yi, zasu kamasu a sauƙaƙe!
A natse Vir ya ce. "Ya batun bank ɗin can?"....... Zuba mashi idanu suka yi, alamar suna jiran karin bayani, Lion ne ya ce. "Zamu gane wace bank ce kuma a wace ƙasa take". ....... Aryan ne ya ce. "Awww bank da suke kai kuɗin Avaris ko?"........ Jinjina kai Vir yai. Lion ya ce. "Zamu gane, kuma zamu kwashe dik kuɗin Avaris dake wajen, In Sha ALLAH zamu gina ƙasar Avaris da shi!".
Chapter 141 · 0% Book details