Sashe 186
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daidai lokacin ya É—an motsa kaman zai juya kamar kuma zai yi gaba, hakan ba karamin razanata ya yi ba, ta zaci damketa zai yi, ai take numfashinta ya É—auke, ta yi gamo da aljani a cikin ruwa.
Sulalewa ta yi zata faÉ—a cikin ruwan, daga ta cikin ruwan yasa hannu ya riko waist É—inta, da yake ta suma sai ta tafi gabaÉ—aya saman buÉ—aÉ—É—en kirjinsa. Hannu yasa ya tattare gashin dake ta kan fuskansa, ya watsa bayansa tare da bin fuskanta da kallo, babu haske sosai, bai iya banbance wacece bace, ya zaci ma ta Noor ce watau V.
Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi tare da matsawa da ita izuwa bakin dutse, ya ɗagata cak ya kwantar a saman dutsen, sannan ya ɗauki gel ɗinsa, ya wanke kansa sosai, ya yi wankansa, ya fito ya sanya bathrobe a jikinsa, ya ɗauki ƙaramin towel ɗinsa ya fara goge kansa.
Bayan ya kammala ya ɗauki kayansa, sannan ya wuce abinsa, bai sake bi ta kanta ba. A lokacin 5:45 ta yi, lokacin sallar asuba ta kusa wucewa. A gaggauce ya shirya cikin tactical t-shirt and army trouser. Ya yi matuƙar kyau, ya ɗaure gashinsa domin ya je ya yi sallah, sai tashin kamshin turaren kamfanin su Noor yake yi, ya fito daga cikin tantinsa.
Fitowarsa yasa dik sojojin dake wajen suka ƙame suka sara mashi, cike da jarumta ya taka ya nufi in da suke yin sallah. Nan ya iso su Zaynish dik sun yi wanka, Zaysh ɗan albarka yana koyawa Noor yadda zai yi alwala, Noor akwai barisa har ya haddace yadda ake yi. A wannan rana sun yi sallar asuba tare da Noor, sallarsa ta farko a arayuwarsa, lallai munai mashi fatan nasara tin da ya fara da sallar asuba, In Sha ALLAH tasa zata yi kyau, domin kuwa sallar asuba ba karamar sallah bace, ita ce sallar da in kana yinta a kan lokaci kafin fitowar rana ba zaka taɓa taɓewa ba a rayuwarka, a cikin salloli sallar laasar ce kawai ta fisa, sallar laasar karshe ce, idan kika rasa sallar laasar a kan lokacin tamkar kin yi asarar duniya ne da abin dake cikinta gabaɗaya.
Ina son jan hankali mata masu jinkirta sallar laasar, ita ce kawai sallar da ALLAH yake rantsuwa da ita, wal asir, sallah ce da take ta musamman, mata ku kiyaye, kada rana ta faÉ—i baki yi sallar laasar ba.
Bayan sun idar da sallah suka zauna yin askar, Leo and Zaynish suka yi karatun Alkur'ani mai girma. Sai da gari ya yi haske, sannan Leo ya umarci da a kira surgeon Manassa ta zo ta wanke hannun Zaynish ta yi trea ting ɗinsa. Da sauri Vash ya miƙe ya nufi tantinsu.
Zaune ya iskota ita da Angelina suna shafa lotions a jikinsu, ga shi ya shigo ba excuse saboda bai yi tunanin zai samesu haka ba, dan yaga Manassa tana da son barcin safe, ya yi zaton ma barci suke yi, yasan Arya ce kawai mai tashi sassafe ko in ce asussuba, amma su Angelina suna kai 7.
Yana shigowa da sauri ya juya masu baya yana faÉ—in sorry. Daga su sai towel da bai kai rabin cinyarsu ba, da kaÉ—an ya rufe mazaunansu, ga shi suna tsaye. Shi a matsayinsa na musulmi ya ji hakan tai mashi nauyi, su kuma da basu da addini sai basu wani damu ba, Manassa har da cewa. "Sir Arvash ya da juyawa haka?".
"Zo ki duba Zaynish ya samu matsala a hannu". Yana gama faÉ—ar haka ya wuce ba tare da ya sake juyowa ba. Kallon juna suka yi da Angelina, zazzaro idanu Angelie ta yi kafin ta ce. "Ke yi sauri ki zo ki je ki duba shi, wayyo, kome ya same shi?". A kiÉ—ine ta yi maganar.
Ganin ta shiga damuwa ne yasa Mannassa fara ƙoƙarin kwantar mata da hankali, ai ina, uniform ɗinta ta sanya a gaggauce, ta ce su je kawai. Shiryawa Manassa ta yi, ta ɗauki rucksack ɗinta suka fito.
Kai tsaye in da su Leo suke sallah ta nufa, a lokacin dik sauran sojojin sun tashi, ya rage daga Leo, Noor, Zaynish, sai Vash, watau ƴan team ona kawai. Su Manassa na zuwa kallo ɗaya Leo yai masu ya ɗauke kansa game da miƙewa, ya nufi tantinsa bai yi magana ba.
Ai Angelina bata san lokacin da ta ƙarisa gaban Zaynish ba ganin yadda hannunsa yake jini, dan Leo ya kwance mashi ɗaurin da ya yi wa hannu, yanka ce sosai aka mashi. Hannun nasa Angelie ta kama, tamkar zata yi kuka ta fara ce mashi sorry.
Mamaki ne yakama shi, shi dai yasan ko sannu bai taɓa haɗa shi da waɗan nan yara ba, meyasa ta damu da shi har haka?. Ɗago kai ya yi slowly ya sauke idanunsa a kan Noor dake kallonsa shi ma. Kashe mashi ido ɗaya Noor ya yi yana sakin one side smiling.
Matsawa Manassa ta yi game da riko hannun nasa, cikin raunin murya Angelina ta ce. "Manassa ki yi mashi a hankali kin ji?"......... Awwww, sai kawai Zaynish ya ji daÉ—i a ransa, to zuciya tin da ha dutse ba ai tana son mai kyautata mata ko.
Ɗauke kallonsa daga kan Noor ya yi, ko sau ɗaya bai kalli Angelina ba, ya yi ƙasa da idanunsa, yana jin Manassa tana wanke mashi hannun, abinku da mazajen AZURE, ko kaɗan bai nuna kamar jikinsa akewa wannan abin ba, ya yi ƙasa da kai kawai. Sai faman ce mashi sorry Angelina take yi cike da nuna kulawa da tausayawaq
, idan Manassa zata zuba mashi magani sai ku ga Angelina ta datse idanu tana faÉ—in ayi mashi a hankali.
Miƙewa Noor ya yi game da cewa. "Let me check on my wife ina zuwa". Ya faɗa tare da nufar hanyar shiga tantinsa, dik in da zai wuce sojojin sai sun kame sun sara mashi.
(Jiya na ji kunce Noor ne ya É—auki mutanen nan dik, hala kun manta in da na ce dakatawa daga É—aukar mutumin Leo ya yi ya nufi Noor yana faÉ—in ya faÉ—i kalmar shahada? Ya za'ayi Noor ya É—auki mutane huÉ—u shi kaÉ—ai fisabilillahi? Ku gayawa kanku gaskiya mana, ga Leo ga Zaynish dikka.)
Gyara mashi hannu tsab ta yi, ta ɗaure da bandeji tare da ɗago kai ta ce. "Headlock sir"....... Kai kawai ya jinjina mata, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Thank you". Daga haka ya miƙe ya nufi tantinsa shi da Vash. Jim kaɗan ya fito ya shiga tantin Leo dan su yi bincike kan mutanen da suka kamo ɗin nan. While sun ɗaɗɗaure karnukansu a wajen da suke zama hura wuta.
Gabaɗaya sojojin dake sansanin ne suka tattara a wajen da suke huta wutar nan except team 1 and matan, dan matan suna ɗaki, team 1 suna ɗakin Leo suna tattaunawa kan abin da suka yi daren jiya, suna shirya yadda zasu tsabtace ƙasar Avaris.
Sojojin dake yi masu girki ne suka kammala game da fara raba masu, suna bin kowa su bashi na shi, sun kaiwa team one nasu a ɗakin Leo, while sun kaiwa su V nasu, sai suka nufi sauran sojojin dake wajen karnukan nan suka fara raba masu, kowa ya ga karnukan nan sai ya yi santinsu, sun haɗu matuƙa.
Babu wanda ya lura da cewa Arya bata a cikin sansanin, dik suna ta harkokinsu, ita kuma tana sume kwance kan dutse yadda Leo ya kwantar da ita.
------------------------🔥
WS-HOSPITAL.
Tsaye 3D suke a ɗakin kyankyasan jariransu, sun rabu suna aikinsu cike da kulawa da taƙatsantsan. While sister Lazy na biye da Dr James tana ɗaukar rahoton komai yadda yakamata.
Freezer Dr Kamal ya nufa, kwalaben dake ɗauke da eggs ɗin da suka cire jikin yaran can ya ɗauko, wanda suka samu 50 eggs ɗin ya ɗauko, a natse ya koma wajen aikinsa. Buɗe kwalbar eggs ɗin ya yi, yana ƙoƙarin zubawa a cikin dish da zai haɗe da sperm da suka fito da shi. Ga mamakinsa sai ya ga eggs ɗin sun canza kala, mamaki ne yakama shi, sun yi wani iri sosai.
Sosai Dr Kamal ya girgiza da yanayin waÉ—an nan eggs É—in, ya yi dik gwaje-gwajensa the same thing yake bashi, É—ago kai ya yi, ya kalli Dr James dake faman zuba eggs É—in hannunsa cikin dish.
"Jammy, I think there is a problem, meyasa eggs ɗin nan suka canza kala? Na yi iya gwajina amma basu nuna mun wani dalilin canjin kalar ba". Zuciyansa na rawa ya yi maganar, saboda a tsawon shekarun da suke aikin nan bai taɓa ganin irin wannan abin ba, meyasa eggs ɗin suka canza kala? Ko dan sun cirosu daga jikin matattu ne? To amma gwajinsu bai nuna masu eggs ɗin suna da wani matsala ba, meyake shirin faruwa ne.
Har yanzu sun gagara tinanin su hakura da waɗan nan eggs ɗin, basu taɓa tinanin ALLAH zai kamasu ta wata siga ba, kai bama su taɓa tinanin akwai wanda ya isa ya kawo karshensu a duniya ba, sun ɗauka a kullum sune da nasara.
Dr Mark ne ya ce. "Kamal kana buƙatar wankin brain"........ Dr James da bai ko kalli in da suke bane ya amsa da. "Ku zubawa eggs ɗin sauran sperm na Haiza'an". Babban magana! Watau komai ta fanjama fan jam, shi baya tsoron komai.
Dr Mark ne ya ce. "Ka manta zaka yi wa Zinta dashen sperm É—in ne? Idan aka zubawa eggs É—in zaka rasa"...... ÆŠago idanu ya yi da sauri, da ya mance ai, da sauri ya ce. "Ku dakata, ku duba wani sperm É—in, ku barmum wancan".
Kai suka jinjina alamar to, a natse da taƙa tsantan suka fara aikinsu, zasu yi dashe yara 500 yau, sun ce nan da two months masu zuwa in suka sake cire eggs ɗin yaran sai su sake dashen wasu yaran ko da 300 ne, a wannan karon ba zai yiwu su kyankyashi yaran lokaci guda ba, dole a samu ratar watanni in dai suna buƙatar 2000 babys.
Dr James ne ya gyara hand gloves ɗin hannunsa, lokacin fertilization ya yi kenan, gaban wasu naurori ya tsaye, sannan ya ɗauki wannan karamar na'ura mai kama da eyes care ya sanya a idanunsa, wannan na'urar ce dake iya zuƙo komai ƙanƙantar halitta a wajen shiyasa suke sanyata, kamar microsoft take.