← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 227

Sashe 18

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

CRYSTAL PALACE. Watau duniyar glass masu bala'in kyau da kyalli game da É—aukar hankali, duniya ce guda mai zaman kanta, cikin CRYSTAL zaku rantse da ALLAH kasa ce or gari mai zaman kanta, wajen da ke haskakawa kamar rana, amma mu shiga cikin domin ku ganewa idanunku.

Katafaren yankin da na tabbata baku taɓa cin karo da irinsa ba. Wasu irin jiga-jigan hyper glass skyscrapers a wajen, gine-gine masu hawa 30 zuwa 50, dik na glasses masu canza launi bisa yanayi gari, suna ƙyalli kamar lu'u-lu'u, tare da golden edges.

Akwai manya-manyan solar gardens, lambunan zamani masu amfani da hasken rana, sannan suke canza launi da dare su bada sky blue light mai ƙara ƙawata wajen da ɗaukar hankali. CRYSTAL PALACE gamayyan gidaje ne masu hawa 30 zuwa 50 da a ƙallah zasu kai 20 a wajen, dikka ƴan haya ne cike a cikin, idan har aka kama maku kuɗin da suke biyan hayan kowani hawa ɗaya a shekara ya isa sayen katafaren gida na alfarma a Abuja Naija, sannan dik kuɗaɗɗen suna tafiya ne wani asusu guda ɗaya, haka na nufin mallakin mutum ɗaya ne.

Akwai infinity sky villas, wasu box masu zubin gidaje ne masu shawagi a iska, haɗe da smart levitation technology, ba kamar gidajen zama bane, a'a, su na yawon shaƙatawa ne a sararin samaniya, idan kun gaji da zaman cikin gida kuna da damar fita ki yanki ticket ku shiga wannan karamun box zai yi sama daku kamar ƙaramin jirgi, sai dai a iya sararin samaniyar CRYSTAL yake tsayawa baya zuwa wani wajen.

Ga watsu rantsasstsun neon quantum roads, titunan da ke haske bisa tafiyar mutane da motocin zamani. Ga wasu magnetic highways, hanyoyin mota da ba sa buƙatar taya, sai fasahar levitation. A saman waɗan nan tituna akwai wasu jiga-jigan Guards madaka ƙarti dake kai komo suna shawagi dan tabbatar da tsaro, kuɗin da ake biyan waɗan nan Guards ɗin kawai arzikin wani kamshaƙi ne a Naija.

Sannan akwai hanyoyi a sama, sky walkways, hanya ce da ta fita daga wannan gini izuwa wannan amma ta sama, kowani hawa akwai hanyoyin da suka sada gine-ginen, ba sai ka sauƙo kasa ka sake hayewa sama idan zaka je wajen mutum ba.

Akwai ƙayatattun wuraren hutawa a ciki irinsu ethereal beach, wani nau'in teku da ke canza launi a bisa lokacin dare ko rana, ba kato sosai bane, an yisa ne dan mazauna CRYSTAL ɗin su mori kuɗin hayansu da kyau. Ba iya su aka tsaya ba, akwai cloud nine resort, wurin hutawa mai shawagi a saman gajimare! Amma shi ma a iya sararin samaniyar CRYSTAL ɗin ne. Lunar reflection park, wani kaɗaɗɗen lambun da ke hasken launin wata, saman lambun wasu kyawawan taurari ne aka yi kwalliya da su dake ƙarawa wajen kyau.

Akwai Crystal sphere arena, wajen taruka, wasanni, kallon cinima dan kallon film ko wani abin, da wajen nishaÉ—i da aka yi amfani da fasahar hologram.

Irin solar da ake amfani da shi a CRYSTAL yana bada wutar lantarki ba irin solar da aka sani bane, domin kuwa su haɗe yake da views ɗinsu, idan rana ta daki glasses na windows ɗin sai wutar lantarki ta samu, batiransu na chanji wanda yasa ko dare ce wuta bata taɓa ɗauke masu.

Babu ƴan aiki a CRYSTAL PALACE, domin kowani gida akwai robot dake aiki bisa umarnin mazauna wannan gida. Akwai SOLARIS CORE, wani katafaren gini ne wanda ya kasance cibiyar kasuwanci, a nan kasuwansu yake, super market kala daban-daban a ciki dan yin shopping ba sai sun fita waje ba. Dan a kara ƙawata CRYSTAL PALACE kawai sai aka yi wasu floating luxury malls a saman, idan kana so zaka iya zuwa can ka yi shopping ɗinka hankali kwance. KAI TURAWA FA SUN CI GABA, YANZU NASAN WASU SUNA NAN SUNA TINANIN ANYA AKWAI DIK ABIN DA NA KIRGAN NAN A GASKE KUWA? TO DIK AKWAISU SARAI, IN BAKU JE IN DA SUKE BA KUN KARANTA A NOVEL ƊINA, SHIYASA NA DAURE NIKE MAKU BAYANINSU DALLAH-DALLAH DAN KU GANE, NAIJA MA MUKE DA KANANAN GINE-GINE IRIN ESTATE BARE SU? AI SUN SHAHARA A GINE-GINE SHIGEN CRYSTAL PALACE TIN TINI.

Ga wani katafaren elysium cloud lounge, wajen cin abinci ne a sama mai balain kyau da ɗaukar hankalin wanda aka tsara shi sosai. Yanayin tsarin tsaron wajen, akwai irin drone security ɗin nan, ƙananan jirage dake kula da tsaro dare da rana, da zarar sun ga wani motsin da basu yarda da shi ba zasu hau kara take Guards su ɗauki matakin gano meke gudana ko wace barazana ke zuwa. Ga irin bio scanning entryways, babu wanda zai shiga yankin ba tare da kowa dake cikin gidansa ya gane waye ya shigo CRYSTAL PALACE a yau ba! Dan akwai tv da aka haɗa da bio scanning ɗin a kowani gida dake wajen.

Dik da haka akwai quantum shielding system, tsarin wall da aka kewaye wajen mai amfani ne da wutar lantarki dan kare yankin daga barazana ta waje, ko jingina daga waje ka yi da jikin bango sai ka ji shocking, kuma bulletproof ne wall É—in, ga wani katafaren CRYSTAL PALACE HOSPITAL a takaice mu ce CHP, hospital ne dan kula da lafiyarsu, asibiti ne wanda shi ne na huÉ—u a duniya wajen karfi da kayan aiki game da manyan jiga-jigan likitoci.

Gate guda biyar ne na shigowa CRYSTAL, wanda kuma dikka gate É—in suna da mahaukatan tsaro na ban mamaki, ba sai na faÉ—a maku haÉ—uwar gidajen dake cikin CRYSTAL ba, saboda makurar haÉ—uwa ne, dik wanda kuka gani cikin CRYSTAL babban kai ne, ya kai yadda ba'a tinani, wane karamin kai da iya kama haya a cikinsa.

To a duniya gabaɗaya irin CRYSTAL PALACE guda huɗu ne kawai, kun taɓa jin labarin THE LINE NA SAUDIYA AND THE CIRCLE NA DUBAI? to su ne guda biyun CRYSTAL cikon na uku sai kuma wani a nan cikin US ɗin shi ne na huɗu, sai dai THE LINE AND THE CIRCLE kunga mallakin gwamnatin kasashen ne, kuma bama a fiddasu ba, shi kuma CRYSTAL mallakin wani mutum ne wanda su kansu mazauna wajen basu san ainahin mai wajen ba, dan an ce ya fi shekaru 10 da mutuwa, wasu sun ce yana prison and ɗauresa life in prison, dan haka yanzu wajen tana karkashin kulawar wani ne daban, to koma dai menene mu je zuwa dan abin dayawa. A takaice yadda Crystal yake kenan. Gidajen cikin CRYSTAL ɗin nan dikka an kama hayansu, babu empty, kada ku manta gidaje ne guda 20, kuma dikkansu benaye ne masu hawa 30 zuwa 50, amma dik wasu manya dake jin kansu a ƙasar sun kama haya suna ciki da family ɗinsu, dan yanayin tsaruwar wajen da kuma karfin tsaronsu, dan ko tsuntsuwa bata isa wucewa ta sararin samaniyarsu ba na'ura zata harbota ko ta kaɗata wani waje, zallar basira da technology aka zuba wajen tsara wannan gini, shiyasa ya fita daban......... Wannan ma na takaita maku haɗuwar CRYSTAL PALACE wlh.

-----------------------

Kai tsaye mu wuce Crystal Palace Hospital, watau CPH. A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da suka yi mata mugun nauyi, tana son motsa jikinta amma ta gagara, da kyar ta yi karfin halin waro idanunta waje. Ya subhanallah, idanun nata sun yi jajir sun kumbura matuƙa, sun zama abin tsoro.

Zazzarosu sosai ta yi tana bin in da take da kallo, ganin bata gane ko'ina bane wajen yasa ta É—an motsa lips É—inta da suka yi mata nauyin tsiya, tongue É—inta tamkar an É—aÉ—É—auresa, da kyar ta iya cewa. "Mammy, mammy where are you?".

Shiru babu wanda ya amsa mata, hakan yasa ta yunkura zata miƙe, sai ta ƙasa, a nan ta ji alamar jikinta a ɗaure yake, ƙoƙarin sauƙo da kallonta izuwa jikin nata ta yi, a daidai lokacin aka turo kofar room ɗin wanda hakan yasa ta wurga eyes ɗinta can. Wani mutum ne ya shigo hannunsa rike da wasu ledojin drip guda biyu. Sanye yake da tail coat, kafafunsa na cikin wasu haɗaɗun cover shoes masu tsadar gaske, fuskansa a sanye da nose mark, kansa sanye da hat, gabaɗaya kayan jikinsa bakake ne harta socks dake kafafunsa.

Yana shigowa ya sauƙe kyawawan dara-daran eyes ɗinsa a kanta, while ita ma shi take kallo, dik da yana sanye da nose mask hakan ba zai hana ka gane cewa haɗaɗɗe bane. Yana da tsawo sosai, ga cikar halittar, dik in da ake neman namiji wannan ya kai.

Ganin idanunta biyu yasa intently ya iso gaban bed ɗin, a gefe ya ajiye drip ɗin kafin ya mai da kallonsa a kanta da kyau. Can ƙasa ya ce. "Had luck". Ya faɗa yana kai hannu zai riko nata hannun. Da sauri ta janye baya, da kyar ta iya sake cewa. "Who are you and where is my mammy?".

A maimakon ya amsa mata sai ya kai hannu ya kama nata, a natse ya zare mata drip da ya kare yana faman jan jininta. Bayan ya cire ne ya zauna saman sofar dake kusa da ita, bai sake yi mata magana ba, da ganin haka ita ma bata sake yi mashi magana ba, ta yi shiru tana tinanin ina mahaifiyarta take?!. Daga karshe ta yunkura, a hankali ta miƙe zaune a tsakiyar haɗaɗɗen bed ɗin da ba zaka taɓa cewa na majinyata bane.

Ƴan kafafunta ta yi ƙoƙarin zurowa ƙasa, sai dai ina, gadon yana da tudu bata iya taɓo ƙasa ba, ɗan shagwaɓe fuska ta ɗan yi, kamar zata yi kuka, kai kallonta a kansa ta yi, ya sunkuyar da kai shiru tamkar ba mutum a cikin ɗakin. Turo baki ta yi tare da gyarawa ta matsa bakin bed ɗin sosai. Dirowa ƙasa da karfi ta yi a in da ta tafi gabaɗaya zata faɗi ya miƙe kafansa ɗaya ya tareta, ashe dama yana kallonta, da ta faɗo forehead ɗinta zai bugu da tiles ɗin ne, sai ya tare kan nata ya bugu da kafarsa.

Slowly ya ɗago da kallonsa a kan face ɗinta, bai yi magana ba yasa hannu ya kama nata hannun, da hannu ɗaya ya ɗagata tare da miƙewa tsaye ya jefata kan gadon. A kan face ɗinta ya tsayar da idanunsa, still dai babu alamar zai yi magana. Yanayinsa yadda kuka san wani shahararren gangster haka.
Chapter 18 · 0% Book details