← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 227

Sashe 13

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe 11 daidai suka hallara a katafaren class É—insu, class É—in ya tsaru sosai, tamkar secondary set haka, suna da Ac, tables É—insu mai shegen kyau da loca, chairs É—insu mai kyau, kowa da kujerarsa. Captain Onbish ne ya hallara a gaban class É—in nasu hannunsa rike da wata katuwar littafi. Fuskansa babu alamar annuri ko wasa, a saman table dake kusa da smartboard ya ajiye takardan hannunsa, yana sanye da kaki a jikinsa.

Rubutu ya É—an yi a smartboard É—in da makar kamar haka FIREARMS kafin ya juyo ya kallesu, while dik shi suke kallo. Dikkansu sun fitar da note books É—insu, a natse cikin kakkaifar voice ya fara da faÉ—in.

"Firearms, watau rabe-raben makamai, yau zamu fara ne da rabe-raben makamai kafin ku san menene makaman na gaske". Ya ɗan dakata yana rarraba idanu a kansu kafin ya cigaba da cewa. "Bindigogi sun rabu rukuni 5 ne, na farko akwai pistols, watau ƙananan bindigogi waɗan da za'a iya rikewa da hannu ɗaya, sannan ana amfani da su ne daga kusa. Misalan pistols akwai glock 17, beretta M9, colt m1911, SIG sauer P226, jimilla nau'ikan kala 10 na pistols gun".

Dafe kai Noor ya yi, a ransa ya ce. "Da sunan waÉ—an nan makamai kawai idan aka barka sai su kasheka ko ka shiga doguwar suma, kana jin wasu sunaye tamkar na horori wai bindigu, ni dai na shiga uku tin da na shigo aikin soja!".

A fili kuwa ya mayar da hankalinsa kan sauraron Captain Onbish da abin da yake faɗe. Leo, Zaynash and Unays sun natsu sosai karatun yana shiga kansu, saboda sun sanya a ransu zasu zama manyan sojoji masu ji da lafiya dan bawa duniya gabaɗaya tsaro su kori ƴan ta'adda, sun yi alkawarin a dik ranar da suka sanya kaki mai ƴanci, ma'ana suka tsallake horo suka zama sojoji, to tabbas ba za'a sake samun wani ɗan ta'adda a duniya ba kasarsu kawai ba, wannan alƙawari ne suka ɗaukarwa kansu. SHIN WANNAN ALKAWARI NASU ZAI CIKA? ZASU YI NASARAR TSALLAKE HORO SU ZAMA SOJOJI?.

Cigaba Captain ya yi da cewa. "Na biyu akwai rifles, bindigogi masu dogon murfi, ana amfani da su daga nesa, kuma suna da ƙarfi da daidaito sosai. Suna da nau'ika kamar haka, bolt-Action rifles, kamar mosin-nagant, kar98k, sai semi-automatic rifles, kamar m1 garand, SKS, da kuma assault rifles, kamar AK-47, M16, FN SCAR, G36, F2000, suna da nau'ikandai fiye da 30, amma ana koyar da nau'i 10 zuwa 12 a wannan Barrack ɗin, ba'a cika amfani da sauran nau'ikan ba". (Sai ga jami'ai na musamman ake koya sauran nau'ikan, misali idan suka gama karɓar horo, yanzu haka manyansu suna nan suna kula da dik wani motsinsu, idan suka kammala aiki za'a zaƙulo jarumai kuma ƴan baiwa, sai a sake basu horon da a nan ne zasu zama manyan jami'ai na sirri dana ambata maku a farko, za'a koya masu harbi na musamman wanda ko a ina ne a faɗin duniya komai nisan da suke zasu iya saita mutum su yi harbi kai tsaye.)

Ya É—an dakata ya basu 2 mins suka rubuta abin da yake karanta masu, dan shi ma yana bayani yana É—an kara rubutawa ne.

"Na uku muna da machine guns, bindigogi masu harbi da yawa a lokaci guda, ana amfani da su wajen mamaye wuri, suna harba bullets da yawa a lokaci É—aya. Sannan suna da nau'ika kamar haka, akwai light machine guns (LMG) RPK, M249 SAW sai general purpose MGs PKM, FN MAG, akwai heavy MGs DShK, browning M2 .50 Cal, suma sun kai kala 10". Nan ma ya É—an dakata ya basu damar rubuta wannan karatun kafin ya cigaba da cewa.

"Na huɗu muna da shotguns, watau bindiga mai fashewar bullets, suna amfani da pellets ko slug, masu amfani daga kusa. Misali remington 870, mossberg 500, benelli M4, winchester model 1897, a taƙaice irinsu 6 zuwa 10 ne kawai da aka fi sani".

"A karshe muna da sniper rifles, bindigar kwantena masu harbin nesa, suna da tsawo da ƙwarewar harbi daga nesa sosai, misalinsu akwai dragunov SVD, barrett M82 .50 cal, M24 sniper weapon system, L96A1, cheyTac M200, su 8 ne zuwa 12 da aka fi amfani da su".

"Amma akwai sauran makamai masu harbi irinsu submachine guns SMG kamar MP5, Uzi, PPSh-41, grenade launchers, kamar M203, GP-25, Rocket launchers, RPG-7, AT4, anti-material rifles, NTW-20, denel mechem, flamethrowers, kaɗan ake amfani da su yanzu, kamar M2. nau'ukan bindigogin, a taƙaice gasu kamar haka pistols 10, rifles duk nau'i 30, machine guns 10, shotguns 8, snipers10, gabaɗaya sama da 80 zuwa100 na nau'i bindigogi ake koyarwa a aji na nan GIDAN SOJA, amma ana mayar da hankali kan 25–30 na asali ne wanda kuma shi ne kuma zaku fi mayar da hankali, yau ku rike na'ikan da na faɗa maku, gobe zamu fara duba ne daga kan menene pistols gun da yadda suke, yadda ake amfani da su!". Ya dakata yana sauke numfashi a hankali.

Shi dai Noor gabaɗaya sunan makaman ma kawai sun hargitsa mashi lissafin ƙwaƙwalwa ne, wai sunan makaman kawai ma ai sai su sa mutum ya mutu da ransa, dan haka shi wlh ragonta zai dinga nuna masu har a gama horon ya fito bai samu result ba ko za'a barshi ya koma gida. Cike da wannan tinani a ransa har suka kammala class, suka tashi around 1 na rana, a nan ne kuma musulman cikinsu suka nufi masallaci dan yin sallah.

Bayan sun fito daga sallah suka wuce hall ɗin cin abinci dan yin lunch. Kamar dai ɗazu group-group suka zauna kowane da ƴan ɗakinsu suka ci abincin su, sannan aka basu hutun 30 minutes kamar ɗazu. Dik wani motsin matasan sojojin nan a kan idanun manyansu suke yi, kun san meyasa ake saka masu ido sosai?. Saboda a yanzu ne ake zaƙulo sojijin ɓangare na musamman, a yanzu ne ake ciro sojoji masu kaifin barisa, suna lura da su ne dan su ga su waye suka fi kaifin basira ta yadda ko sun kammala horo za'a sake basu horo na musamman na sirri dan zama zakwaƙuran kuma su kasance masu iya gano mai laifi da kallo ɗaya, shiyasa ake saka masu ido sosai a wannan lokaci.

Karfe 2:30 Captain ya umarcesu da su tsaya bisa tsari, sannan su yi tafiya a kan tsari izuwa wani katafaren fili mai girman gaske wanda shi ma a cikin GIDAN SOJAN yake.

Bayan sun isa wajen a nan Captain ya fara karantar da su me ake nufi da discipline da ladabi, yadda zasu kasance masu ladabi da girmama manyansu, bin umarni ba tare da gardama ba, tsabtace kaya da gyaran É—akunansu, tsari a rayuwa, da tsarkin jiki. Ai ya zame masu dole su yi ladabi da tsabta ne ma, idan ba haka ba su gwammaci mutuwa!!.

Sun yi wannan horo na discipline har zuwa karfe 4 na yamma, sannan suka wuce masallaci. Bayan sun yi sallah sun dawo suka ɗaura da horon gwajin ƙarfin hannu, ana koya musu yadda ake riƙe makami da ɗagawa ba tare da gajiya ba, amma ba kai tsaye shi aka koya masu ba, domin yau ne ranar farkonsu ko makaman basu gani da ido ba, kawai gwada karfin hannayen nasu aka fara yi ta hanyar haɗa mutane biyu, zasu rike hannun juna, dik wanda ya kwantar da hannun ɗan uwansa shi ya yi nasara, kai da baka yi kokarin ba za'a sake haɗaka da wasu har sau uku, idan baka yi ba yau za'a ɗaga maka kafa tin da ranar farko ce, daga gobe ka sake aka yi winning a kanka zaka karɓi wani horon ne na daban!.

Sun yi wannan horo zuwa karfe 5 na yamma, daga nan aka basu hutun 30min, bayan sun huta suka ɗaura da horon daidaito, aka koya musu yadda za su tsaya da ƙafafunsu ba tare da fargaba ba a lokacin harbi ko farmaki.

Dik horon da suka yi yau Noor shi yake cariying last, kwata-kwata babu alamar zai yi abin arziki a rayuwarsu na matasan sojoji, shi fata ma yake yi a koresa daga school É—in shiyasa yaki mayar da hankali.

Sarai Captain ya lura da shi, kuma da daddynsa ya karɓa mashi Form ɗin ya kawosa ya faɗawa G.A.T a bashi horo na musamman, dan haka shi kuma ya sanar da Captain cewa ya saka ido kan Noor ya tabbatar da cewa horo na musamman ya bashi, daddyn Noor suna da kyakkyawar alaƙa da GAT, Dan haka ya ce kada ya barsa ya yi lalaci dan renon mata ne shi.

Da misalin ƙarfe 6 aka basu horon zuciya, karatu da darussa kan jarumta, sadaukarwa, da ƙaunar ƙasa, aka zafafa masu kan batun kaunar kasa da yin komai a kan ƙasa da aikinsu, aka nuna masu cewa rai ba'a bakin komai yake ba, su kashe ko a kashesu, Captain ya zafafa masu cewa karaya ba halin namiji bane, tsoro ba dabi'a bace, jajircewa ita ce mutum, su tsaya tsayin daka dan kare kasa, ko sun mutu ƙasa zata yi alfahari da su. Sosai zafafan kalaman Captain suka fasa zuƙatan dayawa daga ciki, shi kansa Noor ya ɗan ji kamar zai yi aikin, amma idan ya tuna wannan ɗan banzan wahalar da suka sha yau, kuma a haka ma wai ranarsu ta farko ce, yana tuna wannan zai ce kai shi ina, sai ya ji zafafan kalaman Captain sun goge a kansa. Karfe 7 daidai suka tashi daga horon jarumta, Captain ya basu 5mins su yi alwala zuwa masallacin soji.

Haka kuwa aka yi, bayan sun yi sallar mangariba da ishai karfe 8 suka haÉ—u a dinner hall suka yi dinner, karfe 8:30 suka kammala, a nan ne Captain ya umarcesu da kowa ya wuce room É—insu, suna da damar yin wanka su kwanta, kada su manta gobe 4:30 na asuba zasu tashi. Daga nan ya hura usir kowa ya nufi room É—insa.
Chapter 13 · 0% Book details