Sashe 99
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kallo ya bita yana jiran yaga me zata yi. Aikuwa tana zuwa bata yi wata wata ba ta daka tsalle ta afka cikin ruwan abinta. Tana afkawa ta lume ƙasa tare da toshe hancinta da bakinta wanda hakan ya yi sanadiyar dan dole Jaish ɗin ya bita cikin ruwan, dan a tunaninsa ruwan ya tafi da ita ya kuma fi karfinta ne, bai san cewa ita ɗin gwanace wajen shiga ruwa ba, ta saba, ruwan kuma ta can tsakiya tsakiya akwai zurfi sosai, ta baki baki in da suke wanki ne babu zurfi, amma can ta tsakiya ya kai tsawon Jaish ɗin a zurfi. Ku kanku kun san ruwan da zai kawo Jaish wannan gari ba karamar ruwa bace ba.
Wani irin dariya ne ya so kubcewa Mahnoor lokacin da ta ga Jaish ya tsorata ya bi bayan Mahreen a dubu dan kada ta mutu. A zuciyarta ta furta. "Ai in dai Mahreeh ce watarana sai ta sanyaka shiga cikin wuta ma ba tare da ka sani ba, kaÉ—an daga aikin wannan yarinya Æ´ar albarka".
Shi kuwa bawan Allah haka ya zunduma tsulumdum cikin ruwan ba shiri, tana jin alamar ya tsundumo cikin ruwan ta ɗago kai a ɗari tana fitar da numfashi sama sama kamar zata mutu ƴar ƙaniya. Ƴan sakanni ta ɗauka tana jawo numfashinta da kyar da kyar, sai da ta dawo dai'dai ne ta daka tapi da ƴan tafukan hannayenta tana faɗin. "Na yi nasarar sanya Hamma shiga cikin ruwan nan".
Ƙatsake ya tsaya yana kallon ikon Allah, Mahreen zata iya mayar da mutum ana yi mashi kallon mahaukaci bayan yasan shi mai hankali ne, ita dai Mahnoor ta ɓoye fuska ne tana yi masu dariya, shi ma bappa da tun kafin Mahreen ta faɗa cikin ruwan yake tsaye a bayansu yana kallonsu dariya ya shiga yi masu, Mahreen da karfi da yaji tana son mayar da Jaish irinta, in dai zai cigaba da biye mata tsab watara za'a kirasa da abin da ya fi maye a wannan ƙauye.
Haka nan ya fito tsamo tsamo daga cikin ruwan ya yi sharkaf yana zuban ruwa, sai dariya bappa yake yi mashi, ita ma Mahnoor ta ɓoye fuska dan kada su haɗa idanu ko ya ganta tana yi mashi dariya, ita kuwa hajiya Mahreen tamu a bayyana take yi mashi dariyar tana murna tare da faɗin ta yi nasarar sanya shi shiga cikin ruwan.
Yana fitowa gida ya nufa ba tare da ya yi wajen bappan ba, dakatawa da yin dariyar da yake yi bappa ya yi, dan ya lura kamar ran Jaish ɗin ya ɓaci, sai dai kafin ya yi mashi wani magana tuni ya sa kai ya wuce.............
Abin da baku sani ba my people's, Jaish É—in nan fa ba Jaish da kuka sani bane, yes hakance kamar yadda kuka ji hakan dai na faÉ—a, ku kanku kun san Jaish na King Zuhair dai ba zai yi irin wannan abin da su Mahreen yana cikin hayyacinsa ba, to ya abin yake ne?.
Wannan Jaish ɗin dai ga shi nan ne, shi kansa bai san wanene shi ba, rayuwa dai yake a tsakanin mutane da kuma mutuwa, a halin yanzu dai iya cema ku zan yi bai san wanene shi ba, baya iya buɗe baki ya yi magana, ga dai shi nan babu wanda ya san hakikanin abin da yake damunsa, saboda babu wata asibitin da aka kaisa bare a san damuwar da take cikin kwakwalwarsa, kawai dai yana rayuwa ne. Sai dai kuma akwai ɗabiunsa da dama wanda har yau har gobe suna a tare da shi, which means da su aka haifesa kenan, irinsu kyamar abu, rashin son magana, shariya, halin ko in kula, izza, isa da taƙama, da dai sauransu, bayan su duk wasu dabi'un da ya ɗaurawa kansa daga baya ya watsar da su.
To me ya sameshi? Meyasa baya magana? Meyasa har yau har gobe idanunsa da suka kasance fararetas kamar madara an lalatasu izuwa jajir kamar wuta? Meyasa suka ki washewa idanun? To mu je dai zuwa, alkalamina zai warware maku komai, amma wannan littafin akwai cakwakiyar da ni kai'na suna sanya ƙwaƙwalwata ɗaukar zafi, sai na yi da gaske wlh, amma idan ba haka ba kowani ɓangare da rikicinsa mai zafin gaske, mai kuma bala'in ɗaure kai.
Bayansa bappa ya bi, dan ya lura sam bai ji daɗin abin ba, sau da dama idan Jaish ɗin ya yi wani abin bappa yana yi mashi kallon kamar jinin sarauta ne shi ɗin, saboda su basa ɓuya, a jininsu izza take, hakan yasa bappa yake yi mashi kallo duk yadda aka yi ya haɗa alaƙa ta jini da sarauta, ba'a haka ɗai watarana idan izzansa suka motsa yake zuba masu mulki ba, bappan baya hana shi ko ya ce mashi ya rinƙa sassautawa, dan yasan su fa a jininsu abin yake, ko ya yi mashi magana ba dai'nawa zai yi ba, sai dai ya wahalar da kansa a banza kawai..............
Dama da ni da ku kam my people's ai mun san halin Jaish namu na gaskiya, watakila laluran da yake ciki ne ma yasa ya yiwa su bappan saukin kai wallahu ahlam, amma dai mu je zuwa koma menene zamu sani ai.
Dap bappa zai shigo gida ita ma Nenne tana shigowa, da mamaki cike a ransa yake kallonta, da bakkwan kayanta da komai ta tattaro ta dawo, sai dai da ganin face É—inta zaka iya fahimtar akwai abin da take tafe da shi, da alama akwai zantuka a bakinta.
Sannu da dawowa kawai bappan ya yi mata, tsabar makirci irin na mace har da tsugunnawa ta yi ta kwashi gaisuwa haɗe da bada hakuri. Kai mata duniya ne, muna shagalinmu wlh, mu dai ɗuwawune dole a zauna damu ko anki ko anso..........💃🤸
Mamaki ne ya kara kama shi, amma bai kawo komai a ransa ba, bawan Allah ya karɓi kayan hannun nata da take tafe da su suka shiga ciki yana ta yi mata sannu da dawowa.
Haƙiƙa bappa ya kaunaci maman Mahnoor a rayuwarsa fiye da tubaninku, su bama haɗasu aure aka yi ba, soyayya suka yi har zancen ya kai ga iyaye, Nenne ba ita ce zaɓinsa ba, amma rashin maman Mahnoor ɗin yasa ya hakura ya karɓi Nenne, dan gara mashi ita a kan bare, yana kaunar Mahnoor sosai, dan idan ya ganta tana ɗebe mashi kewar mamarta, hakan yasa ya yarda ya karɓi auren Nennen, dan a tunaninsa zata kula mashi da ita tunda ƴar ƴar uwarta ce, bai san ya makaro ba, dan kuwa kamar yadda iyayensu wato su gwaggo basa shiri basa zaman lafiya haka su ma Nenne da maman Mahnoor ɗin ma basa shiri, dan kowacce tana taya mahaifiyarta kishi, tun suna ƴan'mata ake buga gaba, kunga kuwa Nenne zata iya sauke haushin mamarta da take ji a kanta, matsalar ta samo asaline daga irin zaman kishin da ake yi a gidan Arɗo, shi ne yasa babban kuskure ne ku yi zaman kishi a gaban ƴaƴanku suna gani, hakan ba ƙaramin gurɓata masu tunani da tarbiya zai yi ba, zaku zo ku aurar dasu da nufin hankulanku da nasu ya kwanta ku samu nutsuwa, amma sai ku gaza samun hakan, saboda irin zaman da kuke yi ya gurɓata masu tunani, to dan Allah ku rinƙa sassautawa a gaban yara ko dan gobensu ya yi kyau, ku aurar da su ku samu kwanciyar hankali da nutsuwa, suma su ɗauki duniya da sauki, yanzu dai kunga aya illar yin irin wannan zama a kan Nenne da mahaifiyar Mahnoor, aka ce idan gemun ɗan uwanka ya kama da wuta sai ka yi maza ka shafawa taka ruwa, Allah yasa mu dace!!.
Suna shigowa ɗakinta ta wuce, da alama dai har yau har gobe akwai tsoron Jaish a ranta. Ɗaki bappa ya bita da kayan, bayan ya ajiye mata ya wuce nasa ɗakin izuwa wajen Jaish ɗin, ko sannu bata sake ce mashi ba bare ta tambayi ina zai je, dan magana ta gaskiya ita ma bappan ba shi ne zaɓinta ba, tana da nata saurayin, suna tsaka da soyayya aka rabasu wai dan ta auri bappa ta kula da Mahnoor, kunga kuwa ko dan haushin rabata da saurayinta ma ba zata bar Mahnoor ɗin ba, ta dinga azabtar da ita kenan dan ta huce, kun san shi fa so mugun abu ne wani lokaci, sai ya iya saka ka yi kisa a kan abin da kake so ba tare da ka sani ba.
Da kallo ta fara bin É—akin nata da shi.
Duk tsawon lokacin nan da É—auka bata nan wlh kullum sai baiwar Allah Mahnoor ta share mata É—akin ta gyara shi fes, abin har É—an mamaki ya bata, amma da yake kishi da bakar zuciya sun rufe mata ido da kuma zugin gwaggonta, ga É—an banza jahilci a cike da kai, dan ita ko karatun addinin ma bata samu ba, gwaggonta mayyar son kuÉ—i ce, tun tana yarinya bata barta ta samu ilimin addini ba, yara rabi duk su tafi islamiyya amma ita kuma da sauran yaran da iyayensu ke son kuÉ—i sai a É—aura masu tallar nono su tafi, haka ta taso kan fanko babu komai sai shirme da wauta, shiyasa da zarar gwaggon nata ta kitsa mata wani abin tsab zai shiga kunnenta ya yi kane kane ya yi tasiri.
Ba abin da take tunani face kudirin da ya dawo da ita gidan, a burinsu na son suga sun ƙuntatawa Inna kakar Mahnoor ɗin zasu je su jefa kansu ga halaka.
Shi kuwa bappa nasa É—akin ya shiga, kwance ya isko Jaish a saman gado ya yi flat tare da É—aura hannu É—aya a saman face É—insa tamkar mai yin barci, sai dai idanunsa biyu, ya canza kaya ne ya kwanta.
Kusa da shi bappa ya zo ya zauna tare da fara ambatar sunansa da Hamma Hamma kamar yadda su Mahreen ke kiransa. Kada ku manta shi kansa bai san wanenen shi ba bare har ya sanar da su sunansa, so sai kawai suka sanya mashi Hamma!.