← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 211

Sashe 32

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

HaÉ—a ido kawai suka yi wajen kallon juna, basu furta ko uppan wa junansu ba, amma haka suka sake juyo da kallonsu izuwa kan jami'an, a tare suka kai wa criminal É—in mutun É—aya wani irin bahagon naushi a baki, Obaid ta gefen hagu ya naushi shi, shi kuma Omaid ta gefen dama kamar an aikosu.

Nan take bakinsa ya fashe hakwara biyu suka fita, da alama hakwaran a mace suke, sun ji busar sigari har sun gaji. Sake kaiwa É—ayan ma naushi suka yi a tare. Tsabar iya mugunta har da naÉ—e jallabiyar jikinsu zuwa gwigwa zasu fara labta masu duka kamar su aka kawowa su basu horo.

Ƙoƙarin janye criminals ɗin jami'an suka yi, aikuwa Obaid ya ce. "Kai ku dakata mu basu a jikinsu tukun nan, yau saboda su ma a gidan nan zamu sake kwana, da safe zanzo in ɗan yi Wrestling a jikinsu ko na 30 mins ne haka, naga sun ruɓe da shaye shaye, ba su da kuzarin da zasu iya jurar azabata na 1h".

(Ni kam na ce ko ba su ruɓe bama yaushe zasu juri azabanku? Ai ku wlh ko mai lafiya kuka kama sai abin da hali ya yi, Hmmmm jikokin Akka waye ya ce ba ku ba? Yanzu duk rikicin da kuka rinƙa yi a cikin gida bai isheku ba sai kun karawa wasu ma? Kai my twin's sai shiriyar Allah.)

Omaid ne ya amsa da. "Sure, ni ma da safe ina zuwa, kune kuka harbi yayanmu ko? To ku shirya karɓar azabanmu".

Wucewa da su jami'an suka yi, amma sai da Obaid ya kara masu naushi ɗaya a ciki. Juyawa suka yi tare da cewa ƴan rakiyan nasu su koma bakin aikinsu su sun fasa komawa yau, sai gobe da sassafe zasu koma bayan sun ci ƙaniyar waɗan can criminals ɗin, daga haka suka wuce cikin gida abinsu, abin nema ya samu, dama ba'a taɓasu ba ma sun iya mugunta bare kuma Allah ya kawo masu mai laifi? Ai shikenan kuma.

Tun daren jiya Dr Raj yake fama a kan Ramish amma har yanzu shiru, waya ya yi wa hospital ɗinsa a in da ya ɓuƙaci da a kwararrun Dr's guda biyu and nurses uku su zo gida dan su taya shi aiki, ya dai yi nasarar cire bullet ɗin dukka biyu, amma dai har yanzu bai iya shawo kan matsalar ba, basu ma ta tabbacin Ramish ɗin yana raye ko ya mutu. Tun jiya Dr yake ƙoƙarin gano wani abu, yana zargin kamar a cikin jinin Ramish ɗin da akwai wata kwaya ta ruwa da ya sha kafin faruwar abin, dan tabbas alamu sun nuna jinin jikinsa a gauraye take, hakan tana ɗaya daga cikin dalilan da yasa Dr Raj ɗin ya kasa shawo kan matsalar, dan jinin jikin Ramish ɗin akwai matsala a tattare da ita kuma jinin tayi sanyi over ta yadda Dr ya kasa iya aikinsa, duk wani allura da ya yi mashi jinin taki ƙarɓa sai ta fara ƙoƙarin canza mashi position na aikinsa, kamar jinin matatce.... Tashin sense.

Nasan kun ƙagu ku ji me ya faru, to ku saurara, bayan fitansa gida da nufin ya halarci meeting da zai yi shi da ƴan cikin team ɗinsa. Shi da wani jami'in swat mai tuƙa motar tasa kawai suka fita, bai ɗauki wasu jami'ai ba, ya fita shi kaɗai, dan yana tunanin meeting ne na sirrin, a ganinsa babu wanda ya san da batun, kuma kunga babu wanda ya san da batun sai Leesharh da ta yi mashi laɓe sai kuma ƴan uwansa.

Yana kan hanyar tafiya ne Bilal ya kirasa a waya, a nan ne yake sanar da Bilal ɗin yana hanyar zuwa guest house ɗinsa domin yin meeting da yaransa kafin su wuce ƙasar Tunisia gobe. Okey Bilal ya amsa mashi da shi tare da ce mashi gashi nan biyo bayansa, daga haka suka yi sallama.

Sun É—an yi tafiya mai nisa tsakaninsa da kiran da Bilal ya yi mashi, kwatsam ba zato ba tsammani wata mota ta tari gaban motarsu, da kyar driver nasa ya iya taka birki, saura kaÉ—an su yi karo da motan da ta shiga gaban nasu.

Jin cewa Ramish ɗin bai yi magana bane yasa drivern bayan ya dai'dai ta nutsuwarsa ya juyo tare da cewa. "Sorry sir". Ya yi saurin ce mashi sorryn ne kuma saboda sun san halin Ramish ɗin yana da zafi, yanzu zai iya hukuntasa a kan haka, dan zai ce tuƙin ganganci ne, ba zai yi la'akari da cewa wata mota ce ta sha gabansu ba, zai hukunta shi ne kawai, shiyasa ya yi saurin cewa sorry.

Sai dai ga mamakinsa Ramish É—in bai amsa mashi ba, yasan cewa dama ba wani amsa masu magana yake yi ba, amma abin ya É—aure mashi kai yadda suka kusa yin accident kuma bai yi magana ba. Juyowa ga Ramish É—in da kyau ya yi da nufin ya sake yin magana, sai ji ya yi anyi knocking na glass É—in motar.

Zuge glass ɗin ƙasa ya yi da nufin ya yi magana, dama so yake yi ya gama da Ramish ɗin kafin ya fita ya ci uban koma waye mai wannan mota da ya shiga gabansu, sai ga mai motan ma ya kawo kansa yana yi masu knocking na glass ɗin.

A fusace ya zuge glass ɗin, har da ɗaure fuska sosai irin ba wasan nan, dan kudirin cin uban komawaye mai motan ya yi a ransa. Bai kai ga buɗe baki ba sai ganin ya yi mai motan ya sanya mashi bindigar silent gun a kai, cike da bada umarni ya ce ya yi maza ya yi waje. Ramish kuwa yana zaune kaman gunki, yadda kuka san an sassaƙasa a wajen, idanunsa kuma a buɗe garau yana ganin komai, sai dai ko yatsa daga jikinsa ba zai iya motsawa ba, tamkar ba shi ya yi waya da Bilal ba jimawa ba, in short bayan idanun babu wani abin da yake amfani a jikinsa a halin yanzu, sai kallo kawai, ga kuma wayarsa a hannunsa yana kame kam.

Ba musu wannan jami'in ya fito, saboda babu bindiga a hannunsa, ita kuma bindiga fa kunsan idan tana waje to umarninta ake bi, dan haka wannan jami'in ya bi umarnin bindigar dake kansa dan dole ya fito daga cikin motar. Sai dai akwai kudirin in ya fito ya samu sarari ya ci uban mai motar ya kwaci bindigar a ransa.

Yana fitowa mai motan dake sanye da mask baka a face ɗinsa, ga hand gloves ita ma baka, takalmar kafarsa Booth ce baka, a takaice baka iya ganin komai na jikinsa face ido, ƙara sanya mashi bindigar da kyau ya yi a kai, da alama ya san halin jami'ai zasu yi ƙoƙarin kwatar kansu, sai ya kara sanya mashi bincigar da kyau, abinku da babban gari kuma cikin yankin manyan kai na ƙasar ko'ina shiru tsit, dan dare ne kowa ya wuce gida, dama su manyan nan ba wani fita suke yi ba, suna cikin gida abinsu, to me zasu fita su nema?.

Wani irin fito mai motar ya yi sai ga wasu maza guda uku masu irin shigarsa sun fito daga cikin motar tasa. Kai tsaye gidan baya na motar su Ramish ɗin suka buɗe, kamar sun san ba zai iya taɓuka komai ba, da zafinsu suka ɓalle kofar motar. Janyo shi suka yi suka fito da shi, har lokacin idanunsa a buɗe suna kallon komai ba zai dai iya motsawa ba.

Fito da shi suka yi da nufin su sanya shi a cikin motarsu su tafi da shi, a dai'dai lokacin Bilal ya iso tare da motar sojoji guda É—aya, shi baya kasada da rayuwarsa wajen tafiya shi kaÉ—ai, duk in da zai je da Æ´an rakiya dan tsaro ba dan tsoro ba, inma sojoji or Æ´an'sanda ko kuma jami'ansa wato air force su take mashi baya, baya dai fita shi kaÉ—ai, shi da ma ba farautar rayuwarsa ake yi ba yana kula sosai, amma shi Ramish yasan nemansa ake kamar hauka, yasan da cewa yana da tarin makiya gaba da baya amma sai kuga ya yi fitowansa shi kaÉ—ai, wani lokaci ma da kansa yake jan motar shi kaÉ—ai, ba ya wani damuwa da Æ´an rakiya, yana kasada da rayuwansa, sai ya ce shi ba rago bane, zai iya kwatar kansa a koma inane.

Isowar su Bilal wajen yasa mutanen suka yi azama tare da kara zafin nama wajen ganin sun tura Ramish ɗin cikin motarsu sun gudu da shi. Ai kuwa drivernsa ya ɗaga murya wajen gayawa su Bilal ɗin abin da yake faruwa. Da farkoma wucewa motocin su Bilal ɗin zasu yi, sai kuma yaga kamar ba gaskiya ake ƙullawa a wajen ba, a matsayinsa na Jami'i sai ya ce su dakata su ga menene yake faruwa a wajen?. Suna dakawata ne mutanen suka fara saurin tura Ramish cikin mota su gudu da shi dan sun ga wasu sun dakata a wajen ga jiniya.

Shi kuwa drivern Ramish da yake yasan cewa motar gidansu ne sai ya yi saurin sanar da su da su yi sauri su zo kar waÉ—an can su tafi da Ramish, Allah sarki bai gama ihun gaya masu ba mai motan da ya sha gaban nasu ya ciro bindiga ya harbesa. Ganin haka yasa Bilal ya É—auko nasa bindigar tare da fitowa da sauri.

Kan kace me sauran da suka ɗauki Ramish ɗin suka sauke shi ƙasa suka ciro nasu bindigar. Musayan wuta suka fara yi Bilal ya harbi ɗaya saura suka gudu, sojojin suka rufa masu baya. Ƙarisowa wajen Bilal ɗin ya yi yana bin Ramish da kallo.
Chapter 32 · 0% Book details