← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 211

Sashe 34

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai kawai ya gyaÉ—a mata alamar e yana lafiya ba tare da ya É—ago ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake cewa. "Tashi ka je ka yi wanka".
Nan ma girgiza mata kai ya yi alamar a'a ba yanzu ba. Wannan hali da yake yi mata na rashin magana sai dai girgiza kai yana matuƙar damunta, sannan halin da yake ciki yana matuƙar ɗaga mata hankali ba kaɗan ba, kawai dannewa take yi.

"Kamran meyasa kake mun haka ne? Kasan dai duk abin da zan yi a duniya ina yinsa ne domin kai ko? Domin farincikinka nake yin komai! A takaice ma dominka nake zaune a cikin wannan dajin na tsawon shekaru, meyasa ka kasa gane hakan? Meyasa ka kasa gane cewa uwa tana sadaukar da komai domin ƴaƴanta? Meyasa ka kasa gane cewa uwa ba zata taɓa cutar da ƴaƴan da ta haifa ba? Meyasa a yanzu zuciyarka take ƙoƙarin zaɓar wasu da ka haɗu da su daga baya ka manta da wadda ta haifeka ta sha wahala a kanka? Ni nasan da a ce in ka tafi babu wata haɗari to da ba wanda zai kai ni murnar da ɗaukin ganin cewa ka nemo Prettyn taka, amma ka kasa gane hakan, why my son, why?".
Ta dagata da maganar tana mayar da numfashi tare da kura mashi idanu.

Ba tare da ya ɗago kan nasa ba ƙasa ƙasa muryarsa bata fita sosai ya fara magana. "Mamma ki bar maganar su Pretty, saboda ke na hakura da su, saboda farincikinki na mance da su, ki sani Mamma kin fiye mun su, kin fiye mun komai a rayuwata, sai da kika kula da ni na girma na zama mutun sannan na haɗu da su, da baki kula da ni ba a ina zan girma har na san su na kaunace su, dan haka ki dai'na zancensu, ki manta da su kawai, ni ma na ciresu a raina....."

Kasa ƙarisa maganar ya yi sakamakon kuka da ya kubce mashi mai karfin gaske, Allah ya gani tilastawa zuciyarsa da yake yi a kan ya manta da su Pretty yana cutuwa sosai kuma ba abu bane da zai yiwu gaskiya, kawai dai mahaifiyarsa ta wuci wasa kuma ta wuci tunanin duk wani mai tunani a ransa ne yasa yake ƙoƙarin yi mata wannan sadaukarwan da in ya cigaba da matsawa yana iya rasa ransa.

Ita kuwa Mamma tana son ganin farincikin É—an nata É—aya tilo a duniya amma kuma fargabar rasa shi yasa ta gwammaci ganinsa a cikin bakinciki.

Wani irin tausayinsa ne ya kamata, ita tasan zafin so, kuma tabbas soyayya ta gaskiya kamran yake yi wa Pretty, taga hakan a cikin idanunsa tun ranar, tun da take bata taɓa jin zuciyarta ta karaya ko ta ji tausayin wani abin ba sai yau a kan ɗan nata, musamman yadda ya ce ya hakura da first love ɗinsa yarinyar da yake matuƙar kauna saboda farincikinta, tsabar zuciyarsa na son Prettyn ma da kuka ya kai karshen maganar ya hakura da ita, nan take zuciyarta ta ji in ta yi mashi haka ta rabasu magana ta gaskiya bata yi mashi adalci ba, ta cutar da shi sosai, in dai har zai iya sadaukar da soyayyarsa saboda farincikinta meyasa ita kuma ba zata so ta cika mashi burinsa dan ya yi farinciki ba? Abubuwa nawa ya yi ta sadaukarwa waɗan da yake kauna saboda ita? Ba zasu kirgu ba, ya sha hakura da abu saboda ita, ya sha danne zuciya ya yi mata biyayya koda baya so, meyasa ita yanzu ba zata hakura ta mashi abu ɗayan nan ba? Meyasa?. Haka ta rinƙa faɗa a cikin zuciyarta.

Shesshekar kukansa ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka. Matsowa kusa da shi ta yi cikin karayar zuciya tare da raunin murya ta fara magana. "Sam ba zaka hakura da Prettynka ba, ka je ka É—aukota a koma inane, ka dai'na kuka ya isa haka, yau ina maka izinin ka je ka É—aukota, nasara tana tare da kai my son". Ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka.

Sai a lokacin ya É—ago kansa, idanunsa a datse gam, hawaye sun wanke mashi fuska, gefe da gefen kunnensa dukka ya jike sharkaf da gumi, ga kuma wani zufar tana cigaba da tsasstsafo mashi, in ka gansa a haka sai ya baka tausayi sosai, mai saurin kuka ma sai ya zubar mashi da kwallah.

Girgiza kai ya shiga yi hawaye na cigaba da gangarowa da gudu daga idanunsa zuwa saman face É—insa, tamkar am buÉ—ewa ruwa hanya.

Saboda kuka da ya ci karfinsa da kyar ya iya buÉ—e baki zai yi magana.
"Bana da buƙata Mamma, no need, saboda nasan Pretty ta mutu, ta mutu Mamma, nima mutuwa kawai nake son yi a yanzu, dan nasan na rasa Pretty, babu wani amfanin fita nemanta". Yadda yake magana sai ya baka tausayi, yana maganar ne kawai amma babu wani kuzari ko sanyi a muryarsa, bawan Allah ya zama kaman zararre, ga idanu a datse yaki buɗe su.

Nisawa ta yi tare da furzar da iska mai zafi daga bakinta. "Bata mutu ba, kuma ba zata mutu ba, saboda bazaka taɓa faɗuwa ba my son, komai kasa a gaba sai ka yi nasara, kai ɗin jinin nasara ne yake gudu a jikinka, nasara a jininka yake, babu faɗuwa a jininka, mahaifinka bai taɓa faɗuwa ƙasa ba a komai da ya sanya a gaba, mahaifinka wuta ne mai balbali, jarumi ne, daga ni har mahaifinka nasara muka sani kuma a jininmu take, dan haka zaka yi nasara, ka dai'na tunanin faɗuwa, idan ka nuna sarewa da gazawa hakan yana nuni da cewa kai ba jinin damisa bane! Dan damisa bai san sarewa ba!".

Wani irin buÉ—e idanunsa ya yi a É—ari jin cewa yau da bakinta ta ambaci cewa yana da mahaifi! Abin ya ruÉ—ar da shi ya kuma bashi mamaki.

Cigaba da magana ta yi. "Ban so na sake yin magana a kan mahaifinka ba a rayuwata, amma yau kasa na yi magana a kansa saboda Pretty, ka je yarona, kaje zaka yi nasara dawo da Pretty, na yarjema kaje ka kawo mun ita nan".

Wani irin nisawa ya yi tare da furzar da iska, nan take hawayen dake zarya a saman face ɗinsa suka dakata cak, wani irin wasai ya ji a jikinsa, harshensa da yake ji ta yi mashi nauyi yin magana a ɗazun ne ya ji yanzu ta sake shi wasai, cikin tsantsar ƙaguwa da son jin wanenen mahaifinsa ya ce. "Mamma ki bani labarin babana, and please ki barni na je garesa ko da sau daya ne na gansa da idanuna kinji?".

ÆŠan daure fuska ta yi kafin ta ce. " kamran ba zan baka labarin babanka a yanzu ba, ni dai Pretty zaka je ka É—auko mana a yanzu".

A take ya riƙo hannayenta a cikin nasa, muryarsa har sarkewa yake yi saboda saurin magana ya furta. "Please Mamma na ji ba zaki bani labarinsa ba, to please ki gaya mun in da yake na je na gansa, na yi maki alkawarin ba zan yin mashi magana ba ganinsa kawai zan yi na dawo".

Wani irin canzawa fuskarta ya yi daga annuri izuwa zunzurutun baƙinciki, idanunta a take suka yi jajir, ji take kamar ta fashe da kuka. Amma sai ta danne ta ce. "Shikenan Kamran, zan barka ka je neman nasa, amma ba zan taɓa gaya maka in da yake ba, ka nemosa da kanka, idan har jinin damisa ce take gudu a jikinka to tabbas ba makawa zaka kai kanka in da yake, dan damisa baya sanya kai a waje bai cinma in da yake da burin zuwa ba, dan haka ka kaikanka gare shi".

Cike da zumuɗi ya ce. "Mamma ni kuma na yi maki alkawarin tabbas zan kai kaina gare shi, tabbas zan nemo babana". Ya yi maganar tare da sake fuskarsa kamar ba shi yake kuka a yanzu ba, farincikin jin cewa yana da uba kuma Mamma ta bashi izinin isa ga babban nasa yasa ya mance da duk wata ƙunci da yake ciki, Allah sarki iyaye kenan.

"Mamma in je in shirya in tafi?". Ya yi maganar yana kallon face É—inta.

Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a kafin ta ce. "Kamran ka nutsu, mahaifinka ba yadda kake tunani yake ba, ya wuci tunaninka, zan barka kaje neman nasa ne ma domin ka matsa mun kuma ina son farincikinka, tabbas nasan zaka iya isa garesa, sai dai kuma kafin na barka ka tafi ina da sharaÉ—i guda É—aya".

Da sauri ya ce. "Wani irin sharaÉ—i ne Mamma? Ki faÉ—i koma menene zan yi na yarda".

Nisawa ta yi kafin ta fara magana. "Sharaɗin shi ne zaka yi ɓaddakama, ba zaka tafi a haka ba, ba zaka tafi da kamanninka ba, dan bana son kowa ha ga face naka".

"Mamma why to?". Ya faÉ—a da alamar mamaki a saman face É—insa.

"Because duk wanda ya san babanka idan ya ganka zai gane cewa kai ɗin ɗansa ne, kuma kaga alkawari muka yi da kai a kan ba zaka bari kowa ya san kai ɗan damisa bane, sannan kuma kusantar hanyar in da babanka yake da ainahin kamanninka ba abu bane mai yiwuwa, dan kafin ma ka kai garesa za'a iya hallakaka, wannan dalilin yasa na ɓoye maka wanenen kai, kuma saboda haka yasa nake koya maka faɗa dan watarana ko bananan ka kwaci kanka a koma inane, nasan da cewa ko ba jima ko ba daɗe mutanen mahaifinka zasu cinmana, in ma su ganmu a tare ko kai ka ɗai, shiyasa na ke koya maka kare kanka da kuma kwatar kanka a koma inane, dan haka dole sai ka yi ɓat da kama idan kana son na yarda ka tafi neman babanka".

Shiru ya yi yana jinjina wannan al'amari, Mamma ta gindayar da shi ta kuma ruÉ—ar da shi, shi yarasa to wani irin family ne da shi........ gaskiya nima narasa wani irin rikitarwa ne wannan.

"Mamma na yarda da sharaɗinki, amma taya za'ayi na ɓoye kamaninna kuma?".
Chapter 34 · 0% Book details