← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 211

Sashe 56

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan ran Ronnie ya yi dubu a kan wannan marin to ran nasa ya ɓaci, cikin fusata ya tako ya ƙariso in da suke, daga ganin yadda yake tafiya kai kasan ba rago bane, jarumin gaske ne.

Dai'dai lokacin da ya ƙariso wajen ita kuma Delisha ta ɗagota da dogon gashin kanta tana ƙoƙarin dalla mata wani marin a karo na biyu, ga shi ta damke mata gashi tana ja da karfi. Yana zuwa ya riƙe hannunta ta baya, a fusace ta juyo dan taga wanene? Ai kuwa tana juyowa ya ɗauketa da nasa marin mai doɗar da jin bawa.

Wani irin jiri ta gani ya ɗebeta da karfi, ta ji hannun maza, dan fa marin Ronnie ba wasa, wurgi da hannunta da ya riƙe ya yi da nufin ya kama Sweetien dake ƙoƙarin zubewa ƙasa saboda marin da ya ɗauke Delisha ɗin da shi yasa Delishan ta saki gashin kan Sweetien da ta riƙe ba shiri. Tana sakinta kuma ta tafi zata faɗi ƙasa, shi ne ya yi wurgi da hannun nata zai taro Sweetien.

Yana ƙoƙarin kama Sweetien Delisha da ta dawo dai'dai ta cire hannu zata dallah mashi mari ita ma ko tsoro babu, ta fa san wanene shi sarai, amma take ƙoƙarin rama marin da ya yi mata dan nemanwa kai rugugin balai. Ai kuwa cap ya capke hannun nata da hannunsa ɗaya tare da ƙara dallah mata wani gigitattacen marin mai karfin gaske da ɗayan hannunsa, sannan ya riƙo Sweetie da hannun da ya mareta ɗin, cikin ɓacin rai ya kwashe kafafunta ta zube ƙasa, abin da yasa ya yi mata hakan kuma ba komai bane face renin da take ƙoƙarin kawowa a tsakaninsu, a iya saninsa yasan cewa ko master Devil ya mara bai isa ya ce zai rama ba bare ita, saboda shi ɗin kowa yana girmamasa kamar yadda suke girmama Black Tiger, sanin Black Tiger ɗin ya fifita shi sama da kowa a cikin birnin, dan dole ake yi mashi biyayya, da yara da manya waɗan da suka fisa, kai har dattawa suna yi mashi biyayya, dan ya mareta shi ne ita sarkin bala'i zata rama? Tab dan ma ta samu hankalinsa na kan Sweetie ne, ai da ya yi mata one blow seven die.

A fusace ta miƙe tsaye, kansa ta yi da iya karfinta a dole ba zata kyalesa ba, gani take yi yanzu ta kawo karfi ita ma, ji take kamar zata iya dukansa, mutumin da tun yana ɗan shekara biyar ya fara koyan Wrestling shi ne wai take tunanin zata iya dukansa.

Ai kuwa sake Sweetien ya yi ya juya kanta kamar wani zaki, kan kace me suka fara gwabza faɗa kamar wasu zakuna. Ronnie yana da karfi sosai, wani irin damƙa ya yi mata a gashin kanta wanda sai da yasa ta yi ihu, da karfi ya ja gashin kan nata tare da ce mata ta ji yadda Sweetien ma ta ji lokacin da ta ja mata nata gashin, ashe ba daɗi? Ashe da zafi?, yana yi mata magana yana ƙara fisgar gashin nata da karfin gaske.

Azaban da ta ji ne yasa cikin dabara ta juya tare da damko dogon wuyar nan nasa da karfi ita ma, hakan yasa ya saki gashin kan nata da sauri, yana sakinta ta juyo da kyau tare da shake mashi wuya da karfin gaske. Sweetie kam kara tsorara sosai ta yi, musamman yadda taga suna faɗa cikin rashin tausayin juna, kamar basu taɓa sanin juna ba, duka sosai Ronnie ya yi mata tamkar bai taɓa saninta ba, duk da hakan kuma ta kasa daddara a cewarta ba zata barshi ya sha a banza ba, kenan ya daketa ya daki banza? Ba zai yiwu ba, ga shi sai kara cin jibga take yi.

Da dai yaga dan yana yi mata a hankali ne take ƙara zaƙewa, sai ya cire duk wata sanaiya ya kama hannunta dake wuyarsa ya ɓanɓarota, da karfi ya murɗe hannun nata ta baya, ji kake ƙad ya ɓalle mata ƙashin hannu. Bai barta ta yi ihun hannun ba ya jajumota sama cikin fusata zai yi wurgi da ita saman glass table dake kusa da su.

Ihun da Sweetie ta kurma tare da rufe idanu ne yasa ya farga da kisan kai da yake son yi, dan kuwa in dai ya yi wurgi da ita a wajen sai dai wata ba ita ba, ba zata yi saura ba, dan babu abin da zai hana ƙashin bayanta ballewa sai dai wani ikon Allahn. Jin ihun Sweetien yasa ya wurgata saman sofa tare da matsowa ya riƙo hannun Sweetien wanda ta ɗaura a saman face ɗinta ta rufe idanunta da shi dan kada taga yadda zai yi kisan kai.

Yana riƙe hannunta ya miƙar da ita tsaye kenan kwatsam sai ji ya yi Delisha ɗin ta buka mashi wani abin saka flowers a ciki, wadda ya kasance shi ma da gold aka yi shi, haka ta daddage ta ɗaga shi da hannunta ɗaya ta buga mashi a bayan ƙeyansa, tana buga mashi kuma ta fara layi kamar zata faɗi ƙasa, ga bakin azaba da hannunta da ya karya mata yake yi mata.

Ai kuwa sakin hannun Sweetien ya yi tare da juyowa ya capki wuyarta, da karfi ya shaƙeta, ga kansa in da ta buga mashi abin zafi yake yi mashi over, kamar yadda yake jin raɗaɗin wajen haka yake ƙara shake mata wuya da karfin gaske, nan take idanunta suka firfito waje ta fara ƙoƙarin faɗa tsakanin rai da mutuwa, ƙoƙarin shakar numfashi take yi, amma ina ta kasa, dan ba riƙon wasa ya yi mata ba. Ta kasa iya kwatar kanta.

Sai da ya tabbatar ta dai'na numfashi, sannan ne ya hankaɗata da karfi da kuma hannun ɗaya, gabaɗaya ta tafi ta kifa a ƙasa kamar gawa, ko motsi bata yi kamar ta mutu.

ÆŠaga idanunsa ya yi yana kallon É—an siririn gold stair case dake cikin gold parlourn kusa da dining room, stairs case ne mai design of indomie É—an siriri na wucewar mutun É—aya, na haurawa ne sama in da ainahin room É—in Black Tiger yake. Ajiyar zuciya ya sauke, dan yasan duk abin da suke yi tsab Black Tiger yana kallonsu, yasan komai, kawai dai bai tanka masu bane, ya barsu suka gwabza abinsu.

Stair case É—in ya nufa kai tsaye, babu ko tsoro bare shakka, haka ya bar Sweetie a wajen tana zaune ta rasa madafa, ga dukkan alamu ya saba haurawa wajen.

A can wajen wasa kuwa, sai raƙashewa suke yi, an saki sauti sai rawa suke yi, master Devil ma fa ashe ya iya taka rawa over, Floris ma rawa ta taka sosai kamar babu ƙashi a jikinta yarinyar nan, suna chashewa son ransu, sharholiya iya sharholiya, dama haka suke yi duk idan aka gudanar da gasa.

Makudan kyauta masu tsada Black Tiger ya aikowa Oxil da shi kamar yadda yake a dokar gasar, ba'a karya doka sam sam, ko ma waye ya ci ko ya faÉ—i a gasar doka zata hau kansa.

Almost 1 hour Ronnie ya ɗauka a saman kafin ya sauƙo, yadda ya shiga ba'a haka ya sauƙo ba, daga ganin yadda face ɗinsa take a yanzu zaka san yana cikin tashin hankali da damuwa, idanunsa sun yi jajir sosai, alamar ran maza ya ɓaci. Ga dukkan alamu ya yi katari da abin da bata yi mashi daɗi ba a saman!!.

Kai tsaye waje ya nufa bai sake bin ta kan Sweetien ba, yadda yake tafiya cikin jarumta zaka fahimci lallai ransa a ɓace, ya fusata sosai.

Da kallo Sweetien ta bishi har ya kurewa ganinta. Zama ta yi a ƙasa a wajen gwanin ban tausayi, kallon Delisha dake baje a ƙasa kamar gawa ta yi kafin ta mayar da kanta ta kifa a saman gwiwowinta, shiru ta yi tana tunanin yadda za'ayi ta gudu ta bar wannan Daula. A hankali voice ɗin mummynta ya fara ratsa kunnuwanta, tana tunano zantukan da suka yi kafin mum ɗin ta ɓace masu.

"Sweetie duk wuya duk daɗi kada ki yarda ki bawa wani mahaluki wannan abin, ki kasance mai dauriya a duk halin da zaki shiga, in dai kika bada wannan abin to tamkar ki sadaukar da ran mahaifinki ne, ni nasan ba zan taɓa kai labari ba, shiyasa na zaɓi na baku shi ɗin, dan ba kowa zai yi zaton abin yana hannunku ba, ki kula da Pretty sosai, magana ta karshe a nan shi ne ki sani wannan abin yana da matuƙar haɗari sosai, manya manyan sarakuna na sama da masarautu biyar ne suke neman wannan abin idanu a rufe, zasu iya aikata komai dan su same shi, nasan rayuwarku zata iya shiga haɗari a dalilin wannan abin, amma bani da wani zaɓin da ya wuce in damka maku shi kamar yadda mahaifinku ya bani shi amana, ki sani wannan makulli ne na rayuwa ko mutuwa na mahaifinku".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da sake waigawa ta fara tunanin yadda suka yi da Pretty a kan Spender ɗin bayan ɓatar mum ɗinsu.

"Pretty kin san yadda zamu yi da wannan abin da mummy ta bamu É—in?".

Pretty dake zaune saman gado ta buga uban tagumi ta amsa mata da a'a bata sani ba. "To ni dai wannan abin ni zan baki ki riƙesa, saboda ke kina da ido ni bani da shi, dan haka ke zaki fi kula da shi, sannan ki kula sosai kin dai ji abin da mum ta ce a kansa ko?".
Chapter 56 · 0% Book details