← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 211

Sashe 93

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wanda ya zo gidan sai ya tambayi wacece Leesharh? Tun Abbie nacewa Allah ne ya kara mashi kyautar ƴa bayan Sharifat har ya gaji da basu amsa. Mahaifiyar mommar Gimbiya Zunaira wato uwar gidan King Badeen ce da ta samu labarin Leesharh ta ce a kawo mata ita zata riƙeta, dan ita a yanzu babu wata ƴa a gabanta, su Obaid and Omaid ne kawai suke gabanta, su kuma kunga suna school, sai an yi hutu suke dawowa, ko sun dawo kuma Tunisia suke tafiya yin hutunsu, basu wani zama da ita, dama tana neman yarinya mace dan su rinƙa zama a tare tana ɗebe mata kewa, idan baku manta ba Momma ce kawai yarta mace dama.

Nan fa Abbie ya ce shi dai a'a bai yarda ba, a barmashi ƴar marainiyarsa ya riƙe abarsa, ba yadda ba'ayi ba ya ce ina Leesharh shi zai riƙeta. Yadda ya kafe a kan babu in da zata je ne yasa Ummie ta ƙara tsananta zarginta a kansa, wani irin bakinciki ne ya rufeta, faɗi take wlh ko zata mutu sai ta san ta yadda zata yi Leesharh ta bar mata gidanta.

A takaice dai Leesharh ta yi tarin masoya, da alama tana da farinjini sosai, kowa son É—aukarta yake yi Abbie ya hana, Ummie ce dai kaÉ—ai bata sonta.

Kwana uku a jere family suna tururuwar zuwa duba jikin Ramish, a kwana na ukun ne ya tashi, dan ya ce kwanciya ta ishe shi, ya ɗan samu karfi ya tashi, yana tashi kuma ya fara shirin komawa bakin aiki, ba yadda basu yi da shi ba ya ce ina dole ya koma bakin aiki, dole a koma bakin rai bakin fama. In takaice maku dai dole suka haƙura suka kyalesa, dan sun san kome zasu ce sai fa ya koma kamar yadda ya yi niya.

Leesharh kuwa ta samu lafiya sosai, dan Bilal yasa Dr Raj ya bata kulawa sosai. Daga haka suka koma bakin aikinsu kamar yadda suka saba, batun zuwa ƙasar Tunisia dai sun shafeshi, sun ji labarin harin da aka kaiwa King, amma jin cewa daddyn nasu ya yi nasara sai suka ce to ai ba sai sun je ba, suka cigaba da abin da suka saba yi............✍️🔥

_________________________________🔥

KINGDOM OF POWER.💪🔥💘

Mu koma mu duba yadda aka yi Hoorain ya fita daga cikin gonar nan bayan an kai masu hari!!.

Fafatawa ya fara yi da mayakan nan, yana kashesu wasu suna shigowa, abin mamakin kuma duk wani warriors da zai shigo wajen Auta kawai yake hara, ita kaɗai suke son kamawa, abin tun bai dami Hoorain ɗin ba har ya fara ɗaure mashi kai, meyasa shi basu kawo mashi hari sai ita? Ya jefawa kansa tambaya. Wani mayaƙi ne da ya kusa cin galaba a kanta a in da ya zo datse mata wuya Hoorain ɗin ya kare mata da nasa takobin, amma duk da haka sai da wukar ta taɓata a saman shoulder ɗinta, ya yanketa sosai, hakan yasa ta kurma ihu mai sauti, kan kace me jininta ya fara bulbula daga wajen.

Haba idan ran Hoorain ya kai dubu to fa ya ɓaci a wannan lokaci, wani irin tafasa da zuciyarsa take yi mashi ne yasa a tsananin fusace ya ɗaga takobin nasa ya raba wannan warriors ɗin gida biyu, nan take ya fara yi masu yakin a haukace, kashe su kawai yake yi tamkar mai kashe karnika ba mutane ba, ransa ya kai kololuwan ɓacin rai.

Da suka ga ya haukace masu kisa kawai yake yi babu kama hannun yaro sai suka fara yin ta kansu, kowa ya fara gudun cetan ransa. Bai bi ta kan Autar ba ya raka warriors ɗin da gudu yana yi masu kisan ƙasƙanci da walaƙanci, pata pata ya rinƙa yi masu ɗaya bayan ɗaya sai da ya tabbatar ba mai shaƙar iskar numfashi a cikinsu, sannan ne hankalinsa ya dawo jikinsa.

Jefar da takobin nasa ya yi ya nufe ta da gudu, tana zube a saman gwiwowinta, ta riƙe in da aka yanketa ɗin tana kuka hawaye tamkar ruwa ya ɓalle hanya ya fita, kunsan a guje zai fita ai, haka hawaye ke tsere a saman face ɗinta. A guje ya taho, yana zuwa ya zube gwiwowinsa a ƙasa a gabanta tare da kai hannunsa ya riƙo hannun nata.

Yadda jininta ke zuba ba ƙaramin ɗaga mashi hankali ya yi ba, jikinsa har wani tsuma yake yi ya kai hannu zai rago rigar jikinta ya ɗaure mata hannun nata. Ai a ɗari ta riƙe rigarta da ɗayan hannun nata tana girgiza mashi kai a kan bata so kada ya yaga mata riga, dan an fara kirgan dangi kar ya kalle mata kayanta. Bai yi mata musu ba ya sake mata rigar tata tare da miƙewa ya ɗauketa cak suka nufi saman kujeran King, zaunar da ita ya yi, sannan ya kama sket ɗinta zai yaga, nan ma a hanzarce ta riƙe ta hana shi.

Miƙewa tsaye ya yi, ya shiga tashin hankalin da ta haifar mashi da ruɗu, ji yake ana caka mashi wuƙa mai kaifi a ƙawon zuciyarsa, ita aka yanka da wuƙar amma zuciyarsa tafi tata jin raɗaɗin hakan. Matsawa daga in da take ya yi, can gefe in da ba zata iya ganinsa ba ya nufa, yana jinta tana kuka tana faɗin. "Hoorain kada ka tafi ka barni, dan Allah ka dawo tsoro nake ji".

Sam bai kulata ba, ya tafi abinsa, zuciyarsa na ƙuna. Sai da ya tabbatar ya ƙurewa ganinta sannan ya dakata a bayan wata bishiya, cire rigar mayaka dake jikinsa ya yi ya ajiye a gefe, nan take wani farar single ta bayyana a kakkarfar kyakkyawar surar jikinsa, tamkar yanzu ya ɓare single ɗin daga ledarta, haka ya cirota ya ajiye a gefe, sannan ya ɗauki kayan yakinsa ya mai da jikinsa. Single ɗin ya ɗauka ya koma in da take.

Farar single tas haka ya sanya cikin wannan jini nata ya É—aure mata hannun, saboda zubar jinin ya yi yawa, sai kallonsa take yi tana kuka, sam yaki yarda ya É—ago su haÉ—a idanun, duk jikinsa jini shi ma, dan ya yi kisa ba karya.

Yana gama ɗaure mata ya miƙe ya nufi gate ɗin gonar, still dai a rufe. Haurawa ta saman katanga ya yi ya dira baya ya barota a ciki. Wani jibgegen dutse ya ɗauko, kwaɗon dake jikin gate ɗin ya zo ya fara duka da wannan dutse yana son ɓalleta. Duk wasu warriors a wannan lokacin suna harabar Kingdom ɗin, hakan yasa har ya ɓalle kwaɗon ba wanda ya gansa. Allah ma yasa kwaɗo guda ɗaya suka sanya, sauri yasa basu rufe gate ɗin da kyau ba, da kwaɗi 6 ake rufe gate ɗin da su, sannan a sanya mashi kuba, to tsabar sauri ko kubar ma basu sanya ba saboda sauri.

Ya yi sa'a yana ɓalle kwaɗon gate ɗin ta buɗe, godiya ya yi ga Allah, sannan ya nufi in da take. Yana zuwa bai yi magana ba ya saɓeta sai saman shoulder ɗinsa, da alama yana cikin matsanancin ɓacin rai, dan yadda yake taku ma zaka fahimci ran maza fa a ɓace yake.

A hanyarsa ta nufa cikin kingdom ɗin ma sai haɗuwa yake yi da warriors ɗin Queen Zarina, abin da ya kara kona mashi rai ya sanya shi fafata yaki cikin fushi kenan, duk mayakin da ya kama wani irin kisan walaƙanci yake yi mashi na ƙin karawa. Da kyar da suɗin goshi ya iya samun dama ya ƙariso kusa da cikin harabar kingdom ɗin da ita, a maimakon ya bi ta hanyar da zata sada shi da cikin harabar, sai ya kauce hanya, da yake kingdom ɗin tana da girma kuma tana da kofofin sirri sosai a cikinta, sannan a matsayinsa na assistant commander kuma wanda ya yi wasan kasansa a cikin kingdom ɗin ba wata hanya ta sirri da bai sani ba, dan haka sai ya ɓad da kafa.

Yau har cikin family part ya shiga da ita amma ta kofar baya. Yana shigowa ta kofar baya ya hango King Zuhair yana fita ta kofar gaba, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da yiwa Allah godiya da Allah yasa babu wanda ya kamashi ya taɓa jikin Gimbiya har ma ya ɗauketa, da sun yi katari da King ai shikenan kwanansa ta kare, dan da ya shiga ɗari uku ba uku ba.

Ciki ya shigar da ita, a dab kofar underground ɗin ya sauƙeta, sai shesshekar kuka take yi.

Hannu yasa ya kwance mata single É—insa da ya É—aure mata hannu da shi, sannan ya ce.

"Ranki ya daÉ—e ki je ciki su momma suna wajen, nan shi ne mazauninsu a duk lokacin da aka kawo mana hari irin haka". Ya faÉ—a cikin kunar rai, har wani huci yake yi, da kyar ma ya iya yin maganar.

Kura mashi idanu sosai ta yi, ya kawar da kallonsa bai san su haɗa idanu. Faɗawa saman faffaɗar kirjinsa ta yi tare da ce mashi. "Nagode sosai Hoorain, ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata, dan Allah kazo mu gudu wajensu momma tare kada ka je mutanen nan su kasheka ka ji?".

Hannu yasa ya cireta daga jikinsa, yana tsaye kyam cikin jarumta. "A'a ranki ya daÉ—e, ki je kawai kekam, nima zan je wajen Abbona, In Sha Allah babu abin da zai faru, amma dole na fita yaki kam!".

Kuka ta saka mashi mai sauti a kan ita ba zata yarda ya je yakin ba, dan kada a kashe shi a banza. Lallashinta dan dolensa ya fara yi, hankalinsa duk ya tafi wajen Abbonsa, da kyar ya samu ta yarda zata shiga ciki. Matsowa ya yi da kyar ya iya cire tiles dake wajen ya buÉ—e mata kofar sirrin da idan ba a cikin family kake ba ba zaka iya sanin wannan waje akwai kofa ba, shi ma dai kasancewarsa zakara abin alfaharin KINGDOM É—in ne yasa King ya yarda da shi sosai haka har yasan duk wasu kofofin sirrin dake masarautar.
Chapter 93 · 0% Book details