← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 211

Sashe 78

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sannan ga dukkan alamu Leesharh bata taso da uwa kusa ba, saboda yanayin yadda take gudanar da rayuwarta zai tabbatar maku da cewa ba shakka ta jima bata a tare da mahaifiyarta, duk macen da ta taso a tare da uwa ba zata yi irin shirmen da take yi ba, ga ƙwaƙwalwar dai tana da shi, amma an rasa wanda zai sarrafata ta hanya mai kyau har ƙwaƙwalwar tata ta amfaneta, kuna gani dai yadda take ta fama a kan tunanin masu nikaf, sai ta yi kamar zata ɗago gaskiyarsu sai kuma ta sake komawa ruwa, sai ta yi tamkar ta gane gaskiya, sai kuma ta sake faɗuwa, gabaɗaya gata gatan nan kawai, tana da buƙata uwa ko kuma mai irin zuciyar uwa wanda zai cike wancan gurbin.

Shi kansa Abbie yanzu da ya jawota a jikinsa sosai ya fara lura da cewa da wuya idan wannan yarinya ta kammala secondary, sannan yanzu ya ga ƙanƙantar shekarunta a yanayinta da ta matso kusa da shi, sai dai bai wani ɗauki wannan tunani nasa da mahimmanci ba, daga karshe ma ya watsar da tunanin a in da ya umarce Dr Raj ya tsaya mata ya yi mata duk abin da ya dace!!.

Yah Rizwan and Omar wato Guyson sun shirya komawa ƙasar Tunisia a yau, shi Yah Rizwan batun aurensa da Gimbiya Chuchu zai kaisa sai kuma Akka da ta ce lallai lallai ya zo, dan tana zargin Jaish ko Jawad ne suka yi mata wancan tsiyar, shiyasa ta ce Rizwan ɗin ma ya zo, a cewarta shi ne uwarsu ɗaya da Jawad, dan haka kome za'a yanke a gabansa za'ayi,
Su King basu taɓa rabe ƴaƴansu ba shi da uncle Abbas, amma Akka tsab take rabasu, ba wani haɗesu da take yi da sunan family, wani lokaci idan gigin tsufan ma ya bugota sai ta kira Yah Jawad da Abbas ɗin ma mai gabaɗaya, wannan tsohuwa dai sai dai muce Masha Allah, rigimamma ce number ɗaya.

A ɓangaren Yah Ramish kuwa, Dr Raj ya sha matuƙar wahala a kansa, Bilal ma ba'a magana, har rama bawan Allahn nan ya yi, ya shiga matsanancin damuwa sosai, baya fita office, baya samun ishasshen barci, haka zalika baya nutsuwa ya sanyawa cikinsa wani abin kirki, sai gayyar coffee or cappuccino, idan ya ɗan gaji da su ne sai ku ga ya sha cold brew, aikin kenan kullum, ya rasa ina zai sanya ransa ya ji sanyi, suna kaunar junansu ne, in short Ramish ɗin dake kwance yana jinya ma ya fisu kumari da kyan gani, sai jigila suko suke yi suna going up and down a kansa.

Idan baku manta ba dama harbi biyu aka yi mashi, dukka biyun kuma sun ɗan taɓa yi sosai, ɗayan kam ma a gefen cikinsa ne bullet ɗin ta fasa, ɗayan kuma a hannunsa wajen damatsansa, na hannun nasa kam Alhamdulillah ba laifi an shawo kan wannan matsala, na cikin ne dai aka samu matsala saboda abin da ya sha kafin harbin ɓille ɗin. A iya binciken da Dr Raj ya yi a cikin jininsa ya gano an bashi wata magani ne mai suna arm bars an kwaɓa shi da joins locks da wani shegen magani mai karfin iya ɓacewa a cikin jini wanda ya ƙasa iya gane wanenen, duk iya binciken da ya yi ya kasa ciro maganin, shegen magani ne mai wuyar ganewa idan ya ratsa jini, da ace ba Ramish aka haɗawa wannan ba, kai ace ba wani na jikin Dr Raj ɗin aka yi wa hakan ba tsab zai iya bincika ya gane wani irin magani ne.

Amma ɗan uwansa da suka shaƙu aka yi wa hakan, baya cikin ishasshen nutsuwa da zai iya yin wani dogon bincike, yana tafiya ma tamkar zai kifa saboda tashin hankali, aikin nan yinta kawai yake yi dan tabbatar da ɗan uwansa ya kuɓuta daga haɗari, amma a wahalce yake bawan Allah.

A ɓangaren Leesharh tun ranar da masu nikaf suka katse mata kira a kan ta ce su haɗa ta da babanta, to tun ranar basu sake kiranta ba, ba wai kuma basu nemanta ɗin ba ne, nemanta ma suke yi kamar hauka dan su tambayeta shin Ramish ya mutu ne ko kuwa harbin bata same shi a in da ya kamata ba? Kun san idan ba ita da take cikin gidan kuma hawan da su Ramish ɗin suke ba da wuya masu nikaf ɗin su san halin da ake ciki ta wajen wasu, dole sai ta wajenta, dan idan baku manta ba a baya sun faɗi cewa suna da ma'aikata a gidan, amma ba'a can ciki ba, har suka kara da cewa Leesharh yarinya ce za'a barta ta yi aiki a can ciki, to shiyasa suke nemanta dan su samu rahoton meke gudana a cikin gidan.

Sai dai kash a yanzu ko sun kirata wayar baya shiga, ba komai yasa hakan ba kuma face sun koma kwana É—aki É—aya da Sharifat, gudun kada asirinta ya tonu yasa ta kashe wayar mai gabaÉ—aya ta cusata cikin wani aljihun wandonta ta danna a can kasar echolac É—inta, ta yadda hankalin Sharifat ba zai kai wajen ba.

Abin da Leesharh bata sani dan gane da masu nikaf a nan ba shi ne, a wannan rana da ta zubawa Ramish wannan maganin da suka bata, da Ramish ya mutu tamkar yadda suka shirya ko sun kamashi sun tafi da shi kamar yadda suke so, to da ba shakka ba zasu sake nemanta a waya ba, aikinsu da ita ya ƙare, zasu san ta yadda zasu yi ne a cikin gidan su tona mata asiri ta yadda Abbie zai binneta da ranta, ko kuma su Yah Bilal su kasheta su miƙawa karnika namarta, sannan su kuma su kashe babanta dake hannunsu, kunga sun rufe babinta kenan, a tunaninsu asirinsu a rufe hankalinsu a kwance dan sun san bata san komai dan gane da su ba bare ta tona masu asiri.

Da Allah yasa bata da hakkinsu, Allah ba azzalumin bawansa bane, sai Allah ya nufa burinsu bai cika ba, Allah ya aiko Bilal ya ceci ran ɗan uwan nasa, Ramish bai mutu ba!! Wannan dalilin yasa yanzu suke neman Leesharh ɗin kamar hauka, dan kuwa kunga idan ya kasance Ramish bai mutu ba dole su nemota ta koma bakin aiki, dan su fa sun kwallafa rai a kan sai sun ga bayansa, ba gudu ba ja da baya, wannan abinfa ba iya masu nikaf bane kawai, akwai manyan jiga jigai daga sama waɗan da su suka ƙaddamar da contract ɗin, dan haka Leesharh rayuwarta yana cikin gagarumin haɗari, tabbas idan ta yi sanadiyar mutuwar Ramish kamar yadda suka tsara, to su ba zasu fitar da ita daga gidan Abu Abdussalam ba, a nan zasu tona mata asiri su Bilal su ji da ita, su kuwa kunga a tunaninsu dama bata san face ɗinsu ba bare idan suka tona mata asiri ita ma ta ce zata tona masu.

Gaskiya akwai gagarumin cakwakiya zallarta, dan kuwa Leesharh tana tsaka mai wuya ne, saboda wannan aiki da aka bata jiga jigai manyan kai a ƙasar ne suka ƙaddamar da shi........ Ni dai fatana a nan shi ne kada Leesharh ta sake ta kunna wayarta, dan dole ta nan zasu sameta, idan bata kunna ba ai shikenan, Allah yasa kamar yadda ta kashe wayar ta manta da ita shikenan a tafi a hakan kawai mugayen mutane kawai, zasu zalinci marainiyar Allah!.

Yau ta kama Friday sai murna Sharifat take yi idan aka sauko masallacin sallar jumma'a Abbie ya aminta za'a kaita gidan King Badeen ta wuni sai dare a dawo da ita, ba yadda bata yi ba a kan Leesharh ta zo su je, amma ina ta ce wlh ba zata je ba, kuma tun farko Sharifat ɗin ce ta ja ta ce ba zata je ba, dan tana zaune a tsakiyar gado daga ita sai kayan barci, basu jima da tashi daga barci ba, Sharifat ta tafi gaishe da Abbie, a nan ta tambayesa zata je gidan kakan nasu, ya ce idan an sauƙo daga jumma'a za'a kaita, shi ne ta shigo room ɗinsu da gudu tana murna ta ce. "Leesharh ki shirya Abbie ya yarda za'a kaimu gidansu abokan faɗarki wato su Omaid sarakan zuciya".

Ai daga jin sunan su Omaid ta ce wlh har ta mutu ba zata je wannan gida ba, sai godiya ga Allah dama take yi da Allah yasa ba'a gidan nan suke da zama ba, sun tafi nasu gidan, kawai rana tsaka Sharifat ta wani ce mata tazo su je gidansu? A kan wani dalili? Ai ba wannan magana, shi ne ta ce ba zata je ba.

Magiya sosai Sharifat ɗin ta rinƙa yi mata tana gaya mata ai basa nan suna school, ina ai taki yarda, ta ce wlh ba wannan zance. Daga karshe dai Sharifat ta haƙura ta shirya ita kaɗai. Gidan Abu Abdussalam a manne yake da katafaren masallacinsa da ya gina a waje, a nan suke yin sallar jumma'a, amma fa saboda girman gidan sai sun shiga mota daga cikin gida izuwa mallacin.
Chapter 78 · 0% Book details