Sashe 50
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alqur'aninsu da bappa ya saya masu time da ya je Niger suka ɗauka suka nufi ɗakin bappa, a bakin kofa Mahnoor ta tsaya taki shiga, Mahreen kam tuni ta afka cikin da sauri ta je ta fara taɓa kumatun Jaish, wlh har ja kumatun nasa suka yi saboda taɓasu da Mahreen take yi, sun yi jajir da su, Bappa yana tsoron hanata kada ta tsayar mashi da kukan da ba karewa, rufin asirinsa ya rabu da ita, Mahreen ba kowa yake taɓata ya zauna lafiya ba.
Gaishe da bappa Mahnoor ta yi sannan ta É—aura da cewa. "Bappa zamu tafi karatu".
"To Mahnoor ku kula sosai, sai kun dawo". Cewar bappan.
"To bappa, Mahreen zo ki wuce mu tafi". Da kyar ta fito daga cikin ɗakin, wai ita a dole a barta ta zauna tare da aljaninta....... (Wayyo Jaish yana ganin rayuwa wai aljaninta kai jama'a maman Yasmin Mahreen bata da kirki sam sam😂)
Suna fitowa Nenne na fitowa daga nata É—akin, nan ta fara surfa masifa a kan ina awakin ta? Ai Mahnoor bata isa ta bar gidan nan ba idan bata je ta kamo awakin nan ta zo ta É—auresu a cikin walden dake kusa da kitchen wanda aka É—an kewayesa da É—an gajeran matanga sannan aka yi runfa da zana daga ta sama, sai tirken awakai da aka kafa a wajen.
Miƙawa Mahreen Alqur'anin hannunta ta yi tare da cewa. "Mahreen ki je karatun kada ki yi lattin bari na kamo awakan nasan suna cikin awakan bappa ne, bari na kamosu na dawo da su sai in sameki a karatun".
Karɓar Alqur'anin ta yi ta shige ɗakunsu ta ajiye ta fito. "Muje mu kamosu tare, ke kaɗai zasu wahalar dake, kuma zasu sanya ki watsa awakin bappa su baki aiki, muje in tare maki".
"Wuce ki É—auki littafinki ki wuce karatu ba zaki tayata É—in ba". Cewar Nennen.
Ai a take ta turɓune fuska zata saka kuka, ganin haka yasa Nennen ta ce. "Sai ki wuce ki bita ɗin ai chewing gum". Wannan shi ne biyayyar dole, idan aka ki yi mata biyayya taja asiri ya tonu wajen bappa, kai Mahreen duniya ce, yanzu zata yi wa Nenne hauka mai lasisi, rufin asirinta kawai ta barsu su tafi tare.
Bappa kuwa yana fama da Jaish da ya É—an motsa kaÉ—an, sam hankalinsa baya a kansu bare ya jiyo hayaniyar da suke yi.
A tare suka fita, suna fita Mahreen ta ce. "Baga irinta nan ba, ai dama nace maki ki rabu da Nennen nan ta yi ta zama a gidan ArÉ—o, amma ke gaki mai tsoron Allah, to wlh Nenne ba zata barmu mu zauna lafiya ba da batun shegun awakin nan nata, ni watarana sai na kashesu dukka ma mu huta da masifar safe".
Ita dai Mahnoor shiru bata ce ko uppan ba, cikin garken awakin bappa suka nufa. Wata yarinya ce ta zo wucewa ta ce. "Ku ba zaku tafi karatu bako? Lokaci ya yi, sai Inna Rabi ta yi maku shegen duka ai, ku kullum baku gajiya da zuwa a makare, ko da yake baku gajiya da shan duka ne shiyasa".
Dakatawa Mahreen ta yi da tafiya tare da riƙe west ɗinta, cikin tsiwa da masifa ta ce. "Ke Abu da su waye kike yi?". Ganin Mahreen ce ta amsa mata yasa a hanzarce ta ce. "Ni ba daku nake yi ba". A tsorace ta yi maganar, da alama tun farko bata lura da Mahreen ɗin a wajen bane, yarinya ƴar karama ta zama zakanya a cikin kauyen, duk ƴan mata tsoron masifar ta dana Nennenta suke yi.
"Da mu kike yi nafikijo (munafuka) ai mune kawai a nan wajen, zo nan munafuka!!". Cewar zakanya Mahreen, cikin tsawa ta yi maganar, irin ba wasa a tattare da itan nan.
Ai a ɗari da hamshin Abu ta watsa, gudu take yi da iya karfinta. Ɗage rigarta sama Mahreen ɗin ta yi zata rufa mata baya. Da sauri Mahnoor ta riƙota tana faɗin. "To Allah ya yi dare gari ya waye, rikicin duniya dukka sun tashi, wuce mu tafi ki rabu da ita, ke kowace safiyarki da faɗa take farawa, haba Mahreen yakamata ace yanzu kam kin rage jibgar ƴaƴan mutane".
Sai wani cija laɓɓa take yi, taso ne ta bi yarinyar ta lallasa mata jiki, har da wani ɗage riga zata yi gudu dan iya balai. Kwafa ta yi tare da cewa. "Wlh idan muka haɗu da ita a karatu sai na cire mata hakwaran bakinta na gaba, gobe ba zata sake kulamu ba, ɗan banza duka zan yi mata sai dai Inna Rabi yau ma ta dakeni, amma sai na gwada mata na fita rashin ji".
"To na dai ji, zo ki wuce mu kama awakin nan mu mayar da su mu wuce karatun". Da kyar ta jata suka shiga cikin garken awakin. Awakin Nennen ƙanana ne guda biyar da take kiwatasu a cikin gida, ita sune arzikinta, ji da su take yi, da daddare tana kwamcesu su sha iska, su shiga gidan mutane su yi ta ɓarna a kitchen suna kalitan ƙanzo a tukunya, idan sun gama ne sai su shiga cikin awakan bappa su kwanta, da safe kullum sai Mahnoor ta kamosu ta zo ta ɗaure mata su. Ita kuma Nennen idan ta tashi ko sallar asuba ne taga awakin wasu a kitchen ɗinta ta rinƙa surfa masifa kenan ba ɗaga kafa, ta kama akuya ta yi ta jibga dan ba nata bane....... Allah dai ya shiri Nenne, amma akwaita da son zuciya kam.
ÆŠaure awakin suka dawo suka yi kafin su É—auki Alqur'aninsu suka wuce makaranta.
Bayin Allan da suka je sai da suka sha bilala bibbiyu na latti. Ana tashi karatun kuma Mahreen ta capke Abu da duka kamar an aikota, kafin Inna Rabi ta zo ta rabasu faÉ—ar Abu ta sha É—an banza duka da cizo haÉ—e da yagushi, ta ji mata ciwo a fuska da yagushi. Ai Inna Rabi na dososu ta saki Abu ta watsa a É—ari sai hanyar gida, wlh duk iya shegen Mahreen bata tsayawa a daketa, kaunar lafiyar jikinta take yi amma ta iya jibgar jikin wasu ta yagushesu.
Hanyar gida ta nufa sai taga ai Inna Rabi zata iya biyota gida, dan haka sai ta nufi hanyar wajen kiwonsu, saboda izuwa yanzu tasan bappa ya tafi kiwo, a wajen kiwo kuma ko Inna Rabi ta zo hakuri bappa zai bata ta tafi, ba zai taɓa bari a dakar mashi autarsa ba, kafin zuwa gobe su je karatun kuma bappa ya je ya bada hakuri haka ake fama da ita kullum.
Ai kuwa hasashenta gaskiya ne, a can ta isko bappa yana zaune ƙasan bishiya. Ita kuwa Mahnoor gida ta nufa dan ta mayar da qur'anansu kafin ta wuce wajen kiwon nasu. Inna Rabi kuma ta ɗauko bayafi tare da riƙo hannun Abu suka bi bayan Mahreen dan ta je ta haɗesu ta ji me ya haɗasu faɗa, bata yanke hukunci ba tare da ta ji ta bakin kowa ba, sai ta haɗesu ma take tambayarsu ta yadda ɗaya na zai cuci ɗaya ba.
Ko da Mahnoor ta shigo gidan babu kowa, Nennensu ta shiga maƙota, kun san fulanin daji da shegen iya zuwa maƙota, suna ɗaukar kamar gida ɗaya suke, yanzu yanzu zakaga wannan ta shiga maƙota wannan ma ta shiga nan, rayuwarsu dai akwai ban sha'awa yadda suke kamar ahali ɗaya. Ganin Nenne bata nan ne yasa ta wuce ɗakinsu ta ajiye Alqur'anan, tana fitowa shi ma Jaish yana fitowa daga ɗakin bappa, ya dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi da hannu ɗaya, jiri ne yake ɗebarsa, ya dafe jikin kofar fitowa
Ai a É—ari ta..............
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI â¤ï¸ðŸ”¥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 7/10/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
💘ZANGO NA BIYU....âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
E_________17
Ai a ɗari ta kurma ihu tare da nufar waje da gudu. Ko kallon in da take ma bai yi ba, shi gidan ma yake bi da kallon kyama da ƙaskanci, daga sama har ƙasa yake karewa gidan kallo, har wa yau idanunsa suna nan jajir kamar jini, da alama akwai abin da ya sami idanun nasa.
Mahnoor kuwa bata zame ko'ina ba sai wajen bappa, tana zuwa ta iskosa ya gama case da su Inna Rabi na jibgar Abu da Mahreen ta yi, ya shiga cikin dabbobinsa yana raba wasu shanu guda biyu faÉ—a.
Da kyar ta iya ƙarisawa wajensa a cikin tsakiyar dabbobin, sai haki take yi tana numfashi sama sama. Sam bai lura da ita ta zo da gudu ba, hankalinsa yana kan dabbobin, ita kuma Mahreen tana zaune tana cin gwaiva da bappa ya tsinko mata dan ya yi mata nasiha. Idan kana son zaman lafiya ka yi mata nasiha kuma ku zauna lafiya sai ka bata wani abin.
Haka bappa yake yi mata, sai ya bata gwaiva ko rake ta nutsu tana sha sai ya yi mata nasiha a nutse, a haka sai kuga ta É—auki maganarsa in ta yi niyya, tafa san daidai yarinyar nan, kawai dai idan anyi mata ba daidai bane take mantawa da wani daidai ta rama abinta, amma sarai ta san me take yi.
Ganin ta ƙariso wajensa tana ta zuba uban haki ga numfashinta na fita sama sama ne yasa ya yi saurin riƙota yana faɗin. "Mahnoor lafiya kuwa?".
Kasa amsa mashi ta yi, saboda uban gudun da ta sha, numfashinta bai dai'dai ta ba bare ta iya yin magana. Hannunta ya riƙo suka fito daga cikin dabbobin, in da Mahreen ke zaune suka nufa. Gorar ruwansa dake wajen ya ɗauko ya bata tare da zaunar da ita a kan ta zauna ta nutsu ta sha.