← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 211

Sashe 84

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Commander ba zai kamun masu da hannu ba, dan shi É—in bujumin zaki ne a cikin zakuna, namijin gaske ne.

Ko da suka kama shi mayaƙa shidda ne suka riƙosa, sannan mayaƙa biyu suka cire mashi ragar da suka sanya suka kama shi ɗin. Ƙoƙarin azabtar da shi su kashesa suka fara yi, bawan Allah ya jigata ya wahala. Wani warriors maras imani ne ya ciro takwabinsa zai datsewa commandern kai.

Yana ƙarisawa ya ɗaga takobin kenan tamkar daga sama suka ga an fille mashi wuya. Yana datse mashi wuyar kuma dokin da Hoorain ɗin yake kai ta ɗaga kafafunta sama tare da yin haniniya da karfin gaske........ Tab ta ina Hoorain ya bi ya fito har yazo cetan babansa?.

Kafin sauran warriors dake riƙa da commandern su yi wani yunkuri tuni Hoorain ɗin ya datsewa uku daga cikinsu kai, cikin zafa ya diro ƙasa daga saman dokin nasa, fafatawa suka fara yi da su, duk ya kashe banza, sannan ya rungumi Abbon nasa yana mai bashi hakuri.

Uban tulin mayakan da suke bayansa Abbon yake gani. Kasa iya hakura ya yi har sai da ya ce. "Hoorain waÉ—an nan warriors É—in fa? Kai ka jagorancesu kuka fito ne?".

A takaice ya ce. "Abbo ba lokacin yin magana bane a yanzu". Ya kai karshen maganar tare da juyo da kallonsa a kan mayakan da ya fito tare dasu daga cikin kingdom ɗin, fafata yaki suka yi, ya gwabza da mayakan da suka yi masu kwantan ɓauna suka shiga cikin, da ya shigo cikin kingdom ɗin bayan ya fito daga cikin gonar ne, da yaga abin da yake faruwa na galaba a kansu da ake ƙoƙari yi, ransa idan ya kai dubu saba'in to ya ɓaci a lokacin, shi ne ya ɗaga murya a in da ya fara yi wa mayaƙansu faɗa a kan ta ya za'ayi su bar hakan ya faru? Daga nan ya ƙara masu kwarin gwiwa a in da suka ji sabon jarunta ya diro masu, suka ji jinin jikinsu na tafarfasa tamkar an ɗaura dalma a saman wuta, hakan yasa suka ji wani irin karfi ya zo masu, gadan gadan suka miƙe suka tunkari mayaƙan, Allah ya basu nasara suka cinmasu, kisan walaƙanci suka rinƙa yi masu bisa umarnin Hoorain ɗin, a tare aka gwabza da shi, kafin wani lokaci sai ga mayakan suna gudu suna ihu ancisu da yaki, kaf suka bisu suka kashe shegu, shi ne Hoorain ɗin ya yi masu umarni a kan su fito waje su taya su comments.

Ko da suka fito da yanayin buÉ—aÉ—É—iyar jikin Abbon nasa ya iya ganesa, ba dan haka ba da ba zai ganesa ba, dan na gaya maku jini ya wanke ko'ina na jikinsa, baka iya ganesa, shi kansa Hoorain É—in jini ne ta ko'ina a jikinsa, ya yi wanka har face É—insa dukka, ya gwabza ba kaÉ—an ba, amma har yanzu jininsa a tafashe yake, ji yake yi tamkar yanzu zasu fara yakin ma, tsabar taurin zuciyar irin nasa sam bai ji kamar ma ya fara yakin ba, sai tsuma jikinsa yake yi, jarumin jarumai ba!!.

Haƙiƙa commander ya ji matuƙar daɗin ganin ɗan nasa, rungumesa ya yi tamkar zai mayar da shi cikin cikinsa, wani irin annashuwa na musamman ne ya bayyana a saman face ɗinsa, haka suka cigaba da gwabza yaki a tare kamar wasu yaya da kani.

Cikin ikon Allah, Allah ya basu nasara suka kashe mayaƙa da dama, sauran da suka ga abin ya juyo ta kansu ne sai suka fara artawa a guje, da gudun gaske warrios na kingdom of power suka rakasu. Hoorain ya kama babansa suka nufi ciki, mayakan da suka saura a cikin kingdom ɗin ne suka firfito domin kwasan waɗan da suka jigata izuwa ciki........... To fah a nan ne kuma matsalar take, ina Yah Jawad da chuchu? Ina King Zuhair da ya fito domin jama'arsa? Ina Auta? Hoorain ta yaya ya iya fitowa daga cikin gonar har ya zo ya taimakawa mahaifinsa? Wacece Queen Zarina?. Amsoshinku suna cikin alƙalamina, mu dai je zuwa.

______________________ 🔥🔥🔥
----------------------------------🔥🔥🔥
______________________✍️🔥🔥

DARK WORLD🔥💘

Ko da Ronnie ya je ɗaukarta Black Tiger ya hana shi, bai ɓata rai ba ya dawo wajen rawar tasu. A daren ranar dai sun cashe iya cashewarsu, anci an sha, anyi rawa sosai, masu buguwa sun bugu matuƙa, abin dai ba'a magana.

Sai around karfe ɗaya da rabi na dare kowa ya watse, room ɗinsa Ronnie ya nufa. Wanka ya je ya tsala tare da shiri cikin kayan barcinsa masu tsada, riga mai kajeran hannu ne sai dogon wando black color, saboda hasken fatarsa sai ya yi wa kayan kyau matuƙa, sai zuba haɗaɗɗen kamshi yake yi, handout ɗinsa ya kwasa tare da pen and phone ɗinsa mai shegiyar tsada ya nufi waje.

Babu kowa a parlour, Floris ma ta yi barci. Dining room ya nufa, abinci ya É—eba daidai yadda yake ganin zai ishesu, da kansa ya zuba abincin ma tare da É—auka ya fito. Kai tsaye É—akin Sweetie ya nufa, fuskarsa sai kyalli take yi alamar yana cikin annashuwa.

Tana zaune a tsakiyar gado, sam babu alamar barci a tattare da ita, tana dai zaune shiru ta buga uban tagumi, da alama tunani take yi, ga kuma tarin damuwa a saman face É—inta!. Turo kofar ya yi tare da shigowa. Su fa da alama basu san cewa dare mahutar bawa bane, dan wani lokaci sai su kai asuba suna party abinsu, kamar wasu Æ´aÆ´an aljanu basa barci.

Ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da fara binsa da kallo, ya yi matuƙar yi mata kyau sosai. Ita tana ganin shi ne karshen haɗuwa a kyau tsabta da komai, shi ma kuma yana ganin itace karshen haɗuwa, magana ta gaskiya shi Ronnie kyanta ne yake ruɗarsa, bai taɓa yin soyayya bama, bai ma santa ba, shi dai duk macen da ta burgeshi sai ya sanya a ɗauko mashi ita ya kawota cikin empeir ɗin su yi rayuwa a tare, misali kamar Floris kenan, so a zuciyarsa babu banbancin a tsakanin Floris da Sweetie face kyanta, tsantsar kyan Sweetien kawai ya ja sa har yasa ya fara bawa ta hankalinsa da komai da komai nasa fiye da Floris, idan har akwai wani abin dan gane da ita ma a zuciyarsa to bai wuce sha'awar surar jikinta haɗe da kyanta ba, sai kuma batun Spender, bayan wannan babu komai.

And one thing about him, shi fa bai taɓa yin zina ba, amma su master Devil suna yi, kun san waje idan ba addini ba abin da ba zaku samu a wajen ba, to bai taɓa yin zina ba gaskiya, shi dai yana son ganin ƴan'matan kyawawan fararen tattabaru a kusa da shi, ya yi ta rungumarsu yana gaya masu kalamai masu daɗi suna murmushi yana ɗaukarsu hoto, shi ne kawai buƙatarsa, amma ko da sunan wasa bai taɓa kwatanta zina ba, haka zalika ko kiss bai taɓa yi wa mace ba, a kyaleshi dai idan ta yi mashi kyau ya bata sumbata, yana son yawo da kyawawan mata a gefensa, shiyasa zaku gansa tare da Floris and Delisha kullum, dan kyawawane suma, yanzu kuma ya samu Sweetie da ta ninnikasu a kyau, da alama ya fara mancewa da su, ba wanda yake gani yanzu sai Sweetie............. Ni kam nace Allah ya kamaka yasa sonta na gaskiya ya shigeka in ga ta tsiya, yaro sai iyashege kala kala, kawai kai ka tattaro kyawawan ƴaƴan mutane ka tarasu a gefenka dan ka yi ta kallonsu kawai? Wlh ana tsiya a Dark world, Ronnie ɗan duniya ne, wato shi baya son munana sai kyawawa, justice for kyan Sweetie!!. A gaskiya yana kaunar kyau ne sosai!!.

Sai ka rasa ganewa guy ɗin nan, komai nashi sai shi kaɗai, shi kaɗai yasan me a cikin ƙarƙashin zuciyarsa.

A gefen bed É—in ya zauna tare da É—aura kayan abincin a saman side drawers. Cool murmushi ya sakar mata kafin ya ce. "What are you thinking queen of beauty?".

Ƙara ruɗewa ta yi da ya yi murmushi, dan kuwa wani irin sihirtatcen kyau ne ya sake bayyana, ga dimples ɗin nan nasa masha Allah.

Jin bata amsa mashi bane yasa ya ɗan kwanto da kansa kaɗan ya leƙa face ɗinta. "Ko dai barci kike yi a zaune ne?".
Ajiyar zuciya ta sauke. "A'a idanuna biyu, kawai ina ganinka ne?".

"Na yi maki kyau ne?". Cikin wani irin murya ya yi maganar tamkar mai jin barci, bayan kuma yanzu ya gama tikar rawansa. Kai ta gyaɗa mashi tare da cewa. "Sosai ma, kana da kyau matuƙa". Ɗan matsowa kusa da ita sosai ya yi. "Na kai ki kyau ne?". Kamar mai raɗa ya yi maganar.

"Har ma ka fini". Siririn murmushi mai ƙayatar da mai kallonsa ya saki. "To taso ki bani abinci a baki, daga nan sai na gaya maki gaskiyar cewa kin fini kyau na kuma tabbatar maki da hakan".
ÆŠan zaro idanu ta yi. "Abinci a baki kuma? Ka zama Pretty ne? Ni gaskiya ba zan iya baka abincin a baki ba ka yi girma, kawai ka ci da kanka".

Maƙe mata shoulder ɗinsa ya yi tare da shogwaɓe fuska sosai, kamar zai sa mata kuka ya ce. "Ni bana iya cin abinci har sai idan ƴan'matan kyawawa kamar kece suka bani a baki"........... Wlh Ronnie yana iyashegensa son ransa, sai kyawawan tattabaru ne zasu bashi abinci ya ci.

Aikuwa sake baki ta yi tana binsa da kallom mamaki, wani irin kyau na musamman ya yi mata da ya yi shagwaɓar nan, ashe ya iya shagwaɓa kamar Pretty?....... Ni kam na ce menene ma Ronnie bai iya ba, ai wannan ku gansa ne kawai ku barsa.

Sai ya tuna mata da Pretty sarkin shiririta da shagwaɓar, nan take face ɗinta ya sauya na tuna ƴar uwar tata da ta yi.

"Haba mana queen of beauty, ba zaki bani a baki ba? Ko kina son na zauna da yunwa ne?". Ya faɗa a shagwaɓe har da turo baki....... "Idan fa ina jin yunwa bana iya yin komai, kuma kuka nake yi, idan na yi kuka kuma Floris ba zata barki ba, dan kin saka mata beb ɗinta kuka! Sai ta zaneki, yaya ma ba zai barki ba". Omg yadda ya yi maganar sai wanda ya gani!!.
Chapter 84 · 0% Book details