Sashe 192
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ta É—ebo ruwa a hannunta ta shafa mashi a fuska, wani daddaÉ—ar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanu, da alama kauna tana ratsa shi, giyar soyayyarta na É—ebansa.
Cikin nutsuwa tasa sabulun a face É—insa, a hankali hankali ta fara goge mashi tana wanke dik baki da jan tana kuma latse mashi lallausan kumatunsa.
Ita kuwa Mahreen da ta je ta ce wa bappan gata nan Hamma ya ce yana kiranta, sai bai musa ba ya ce e tazo ta taya shi hira, dan yasan takura masu ta je tana yi yasa suka yi mata hakan.
Taso ki ta ce wa bappa ita dai bata son yin hira da shi wajensu hamma zata koma, da kyar ya shawo kanta ta hanyar ce mata tazo su yi hira zuwa anjuma kaÉ—an zata raka shi wani wajen. Jin za'a je yawo ne yasa ta yarda ta zauna.
Luv bird kuwa, tas ta wanke mashi face ɗinsa, shi ma ya karɓi sabulun ya wanke mata jaja jajan janbakin da ya goga mata. Bayan ya gama wanke mata ne ya ɗabo ruwa a hannunsa ya watsa mata a kirji saman tula tulanta.
Da sauri ta kalli wajen, sai kuma ta ji kunya ya kamata, zata yi kasa da kai ya yi saurin yallabo haɓarta. Ɗago ido ta yi suka kalli juna. Girgiza mata kai ya yi alamar bai yarda ta sunkuyar da kai ba.
Murmushi ta sakar mashi ba tare da ta furta uppan ba. Sake haɓar tata ya yi yana kallonta.
Hannunta tasa cikin ruwan tana É—an wasa da shi. Matsowa ya fara yi da face É—insa izuwa saitin tata, dan ya jika mata fuska lips É—inta sun yi pink sun tafi da imaninsa, ya ji ba zai iya hakura ba sai ya É—an shasu.
Sai da ta bari ya iso dab da ita sai ta watsa mashi ruwa a fuska ta miƙe da gudu zata bar wajen. A miliyan ya miƙe ya riƙota, dama kamar yasan zata yi mashi hakan, shiyasa ya yi timing ɗin kamata.
Sama ya É—agata sai saman shoulder É—insa. Bubbuga bayansa ta fara yi tana faÉ—in. "Hamma dan Allah ka saukeni kada bappa ya ganmu, Allah ba zan sake ba".
Ina bai kulata ba ya haura sama da ita, dan yasan bappa dai ba zai zo ba. Cikin daji ya kutsa da ita, da alama cikin gonar shinkafa zasu tafi, dan fa soyayyarsu a wajen bishiyar gwaivar nan tana muguwar tafiya da imaninsa, wannan shi ne akuya ta ji daɗin manda, Mahnoor na Hamma hamma na Mahnoor, suna sha'aninsu nima ina nawa sha'anin da Maltina ta mai sanyi....😂
To kuzo mu je mu leƙo su Khadija bayin Allah, watakila kafin mu dawo Hamma ya isa in da yake da nufin zuwa, sai muga me za'ayi kuma tun da shi baya gajiya da................
________________🌹💘___________
ABUJA.🌹
Zee ta kara samun lafiya sosai masha Allah, kullum na Allah sai sun ari wayar wannan Auntyn tasu sun gwada kiran number Sadiq, amma ina bata shiga, kullm magana É—aya dai tana a kashe, tun suna damuwa da hakan har suka daina bayin Allah.
Wai ina Sadiq ne my people's, kun dai san haka kawai wlh ba zai yi shiru bai nemi Æ´aÆ´an nan nasa ba, dan yasan halin da ya barosu, dole dai akwai wani dalili bawan Allah.
Zee tana taya wannan mata aiki sosai, matar yanzu bata hanata, dan ta samu lafiya. Sun ki su gaya mata labarinsu, dan a cewasu gara masu zama a wajenta da su koma gidansu wajen Hauwa hakan yasa suka ɓoye mata asalinsu, Allah sarki basu san Hauwa kam bata nan bama, bata kasar ma, dan kuwa Kasar Brazil suka wuce da ita, sun ce dai sai ta faɗi in da su Khadija suke ko kuma ayi ta azabtar da ita har sai ta faɗa, Allah sarki ba turanci hakan yasa ta yi shiru ba magana, su kuma sun ɗauka taurin kai take yi masu ba zata buɗi baki ta yi magana ba, shiyasa shi gogan ya ce a wahalar da ita har sai bakinta ya buɗe.
Ni kuma sai ihu nake yi ina gaya masu bata jin turanci ne yasa ta yi shiru ba taurin kai bane, amma ina sunki saurarona dan nima da Hausa na gaya masu........😂
Cikin Khadija a yanzu ya shiga watansa tara, daga yanzu zuwa kowani lokaci zata iya haihuwa, saboda haka lafiyarta dai sai a hankali, yau zazzaɓi gobe ciwon kai jibi ciwon baya, haka take ta fama baiwar Allah, fatarta ya ɗan kara duhu yanzu.
Zee tana iya bakin kokarinta wajen taimakawa yar uwar tata, ita ma wannan mata tana iya kokarinta wajen taimakawa Khadija ɗin, dan ta ce tausayi suke bata, sai dai Khadijah ta ki gaya mata cikin jikinta bashi da uba, bata sheganta shi ba, sun ɓoye suka ce mata ai ɓarayi sun kashe baban nasa, hakan yasa ta kara tausaya masu.
Amma Khadija tana da iya shege wlh, wai ɓarayi sun kashe baban, wato dai tasan shi ɗin ɓarawo mutane ne yana zuwa yana yi masu ciki shi ne aka ce masu aiki irin nasa ne suka kashe shi, to baban cikin ina kake? Da ranka da lafiyarka kana ji da mulki isa da izzar zuwa ka ɗauki dik ƴar da ka ga dama ka yi mata ciki amma Khadija ta ce ka mutu.
Zee ta ɗan mayar da jikinta kaɗan, ta ɗan murmure saboda tana samun kulawa, kullun fuskarta a ɗaure tamau, ko baki sun zo cin abinci bata ɗaga idanu ta kalli mutun, zata kai masu abincin amma fuska kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa.
Yaran aikin da suke taya Hajiyar aiki tun kafin zuwansu Zee wajen, yanzu suna mugun respect ɗin Zee, dan kuwa ta riƙe mutuncinta basu ga fuskar wasa ba, ta ja ajinta, dama ita Khadija ba fitowa take yi ba, tana kwance a ɗaki, idan ta gaji da kwanciya ne sai ta fito ta koma ta baya ba ta idanun mutane ba, ta zauna ta buga uban tagumi tana tunanin duniya, kullum aikin kenan.
Kun san halin Zee dama bata É—aukar raini ko wargi, shiyasa a dik in da take take kama mutuncinta take kuma girmama kanta.
Yau Sunday babu kasuwa sosai, jama'a É—aiÉ—ai ne suke shige da fice a wajen, hayaniya ya ragu saboda weekend kowa yana gida.
Zee ta yi wankarta tana sanye cikin doguwar rigarta, daga cikin kayan da suka zo da shi ne. Wajen Khadijah ta nufa, tana zaune saman stool tana cin yalo da Auntyn tasu ta saya mata a kasuwa da ta je cefene............. Na ce anya kuwa kirkin wannan mata haka kawai take yi masu kuwa? My people's ku duba fa ku gani, mun san na Allah basa karewa, amma a irin wannan yanayi da duniyarmu ta lalace anya kuwa? Har da saya masu tsaraba fa take yi idan ta je kasuwa, anya bata buƙatar wani abin daga garesu kuwa? Haka kawai kam akwai dai wahala gaskiya, ni dai na ɗiga ayar tuhuma a kanta gaskiya, mugu bashi da kama, su Khadijah ku kula dan Allah, kada dai ku saki jiki.
Plastic chair Zee ta ɗauko ta zo ta zauna a kusa da ita, miƙo mata yalon ta yi tana faɗin. "Tun ɗasun ina kika shiga? Na san dai yau babu aiki sosai".
Ɗan turɓune fuska ta kara yi. "Ina wajen Aunty ne mana tana bani labarin rayuwarta na baya, ni bama wannan ba, wai Aunty Khadijah yaushe zamu bar gidan nan ne? Dan wlh ni banson zama a nan".
Ɗan zaro idanu Khadija ta yi. "Zee mu bar nan fa kika ce?". Tana magana tana miƙo mata plate ɗin yalon.
Kai ta gyaÉ—a mata alamar e hakan yake nufi, sannan ta É—aura da cewa. "Ni ba zanci yalon ba".
"To idan muka bar nan ina kike son mu je?". Tana magana tana gutsiran yalon nata, bayan ta mayar da plate É—in saman laps É—inta.
"Wajen kawu Sadiq mana". A takaice ta bada amsa tana kara turɓune fuska.
"To ai sai ki bari mu cigaba da gwada number tasa sai randa Allah ya yi muka samu wayarsa sai ya yi mana kwantance mu je ko kuma ya zo ya É—aukemu ko?".
Shiru ta É—an yi kamar mai wani tunani, tasan dai ba zasu iya komawa gidan babansu ba, dan idan akwai in da suka tsani zama a duniya bai wuce wannan gida ba, idan suna ciki kullum a cikin kunci suke suna tuna rayuwarsu ta baya, ba zasu samu farinciki da walwala ba, so ba zasu koma can ba, gidan su Sadiq kuma tasan dole sai sun same shi a waya ya gaya masu in da zasu je su samesa ko ya zo ya É—aukesu dan gudun kada su sake faÉ—awa irin wancan tsautsayin da suka faÉ—a.
"Zee ki rinƙa ɗan sakin fuskar taki mana, aka ko saurayi ai kya samu, amma yadda kike kamar wata basawan nan yaushe zaki samu saurayi? Baki san razana masu kallonki kike yi bane? Wasu fa zaki tarar ba abinci suka zo ci ba, ke suke son samun damar gani, amma sai ki rinƙa ɗaure fuska haka?". Cewar Khadija, cikin zolaya ta yi maganar.
Kara cukule fuska ta yi. "Ni Aunty Khadijah bana so, ce maki aka yi ina neman saurayi ko kuma zan yi aure ne?".
Zaro idanu ta yi. "Ba zaki yi aure ba ya zan yi dake to?".
"Ki yi yadda kike so dani, amma ni da aure kam babu wannan zancen".
"Meyasa to?". Tana magana tana cin yalo.
"Saboda yawancin maza mugayene, azzalumai kuma mayaudara, ki kalli irin zaluntarki da aka yi mana, amma kike cewa na yi aure?". Cike da damuwa sosai ta yi maganar.
"A'a Zee, kada ki kafa hujja dani wajen faɗar ra'ayinki, ke dai kawai ki roƙi Allah da ya baki na gari". A sanyaye ta yi maganar.
"Ni fa Aunty Khadijah wlh babu aure a tsarina, kuma banga namijin da ya isa in sake mashi fuskata ba, ke ni in takaice maki ma na tsani maza". Tana kai karshen maganar ta miƙe da alama ranta ya ɓaci, bata son batun maza ne tun da namiji ya cutar mata da ƴar uwa.