← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 211

Sashe 113

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yauwa ashe kin gane, yanzu kinga mu shirya mu sa ranar tafiya Kadunar nan, dan na gaji da zaluncin Hauwa, banda RAWANIN ZALINCI da mugunta babu wani abin da yake kanta, gara mu tafi wajen kawu sai ya fi mana, kinga ba iyawa da ita zamu yi ba, ni bani da karfi a halin yanzu, ke kuma baki da lafiya, ba zamu iya da ita ba, gara kawai mu bar mata gidan.

Na'am da zancen nata Zee ta yi. "To amma Aunty khadina kuÉ—in motar zuwa fa? Sannan a ina zamu ga su kawun?". Tana magana tana É—an zaro idanu alamar ta shiga ruÉ—ani.

"KuÉ—in mota kam zan É—auka mana a cikin kuÉ—in da na zo da shi, su kuma su kawu In Sha Allah zamu gansu". Ta kai karshen maganar tare da karkatawa ta kwanta a saman gadon ta tada kai da laps É—in Zee.

Duk waɗan nan maganganun da suke yi a kan kunnuwar Hauwa suke yinsa, ta yi masu laɓe tana jinsu, burinta kawai ta ji sun faɗi a in da suka ajiye kuɗin, dan ta sha alwashin sace kuɗin nan ko ana ha maza ha mata, Allah Allah take yi wani tsautsayi ya ja su fita daga cikin ɗakin ta shigo ta kwashi kuɗin abinta. Bakar mugu ba, to ta Allah ba taki ba, In Sha Allah ba zaki gansu ba bare har kwashe.

Shafa kan Khadijah ɗin ta farayi suka cigaba da yin hira a in da Zee take ta yi mata magiya a kan idan mace ta haifa dan Allah ta yi mata takwara. Alkawari ta yi mata a kan za'ayi haka, koda ta mutu idan yarinyar ta zo da rai to ta rinƙa kiranta da Zainab.

Girgiza kai ta yi tare da cewa ba zata mutu ba, In Sha Allah ita zata shayar da Æ´ar tata. Amin kawai ta amsa da shi, amma ita a jikinta bata jin zata cigaba da rayuwa mai tsawo...........

__________________________🔥

DUBAI🛬

Leesharh, kwance take a saman bed ɗinsu tana fuskantar saman celling, ta yi shiru da alama duniyar tunani ta luluƙa, wayarta ce ta fara ringing, ba wayar da masu nikaf suka bata ba, a'a, wayar da Bilal ya saya mata ita da Sharifat iri ɗaya, jiya ya sayo masu wayar ya kawo masu, akwai sim card da komai a ciki.

Ganin sunan my brat ne yasa ta yi saurin picking. Sharifat ce.

"Hllo Bloody". Daga ɗayan ɓangaren Sharifat ɗin ta faɗa. "Naam Brat". Ta masa mata tana miƙewa zaune, ta kara kyau sosai, har ɗan cika ta yi, ta yi kumari saboda kwana biyun nan ta rabu da su annoba wato masu nikaf, tun da ta jefa wayarta a cikin echolac bata sake bi ta kansa ba.

"Bloody ki zo É—akin Abbie yanzu". Cewar Sharifat É—in.

Da okey ta amsa tare da miƙewa zaune tana katse kira , wandon jeans fari ne a jikinta, daga ta sama kuma riga ce black color mai karamar hannu iya daidai shoulder ɗinta, kanta babu ɗan'kwali, ta saki gashinta da yake shan gyara sosai a hannun Sharifat, sai kyalli yake yi.

Kasa ta sako, mayafinta mai É—an girma ta É—auko, yafawa ta yi tare da É—aukar wayar tata, ta sanya parlourn sillpers masu kyau da laushi a kafafunta, sannan ta fito.

Kai tsaye part ɗinsa ta nufa, tana kan tafiya ne massage ya shigo cikin wayar tata, ƴar kara wayar ta yi, haka yasa ta kunna wutar screen ɗin dan ta duba saƙon wanene?.

Tana yi tana cigaba da tafiya, bata ankaraba dab zata shiga parlon Abbie shi kuma yana fitowa, karo suka ci a in da dukkansu wayoyinsu suka faɗi ƙasa, shi ma yana tafiya ne yana latsa waya kamar dai ita, shiyasa suka ci karo ba tare da sun farga ba.

Wani irin tsoro ne ya kamata, tsoron ɗagowa ta kalli wanenen ma ta ji, ƙasa motsawa daga in da take ta yi. Hakan ba ƙaramin haushi ya bashi ba, ta buge mashi waya kuma ta ƙasa tsugunnawa ta ɗauko ta bashi hakuri? Lallai yarintar nan da me take taƙama? Ya jefawa kansa tambaya.

Ai ko da wuta take tafiya a bakinta sai ta san yau ta haɗu da Ramish ya faɗa a ransa. Wani irin marin da ya dalla mata a kumatu ne yasa ta dai'na gane komai, ji ta yi kamar ba a duniya take ba, duk da take chocolate color sai da yatsun hannunsa suka fito a saman face ɗinta, alamar ta maru kenan, har wani jiri ne ta ji yana ƙoƙarin ɗibarta, hankalinta sai da ya gushe na wucin gadin.

Bilal da yake bayansa da suka fito a tare ne ya ce. "Ramish yau kai ne da sanya hannunka a jikin mace? Abin da mamaki, what kind of sadness did you feel da har ka mareta?". Yana magana yana kallon ta ta yi mutuwar tsaye, ko motsawa ta kasa yi.

Dr Raj dake bayan Bilal ɗin ne ya amsa da. "Dole ya mareta mana, kana gani ta buge mashi waya amma taki tsugunnawa ta ɗauko ta bashi hakuri!"............ Aka ce so so ne amma sonkai ya fi, karo fa suka yi, ba ita ta buge shi ba, duk suna kan latsa wayar ne suka bugi juna, amma sun ɗaura mata laifi sun bi bayan ɗan uwansu, sun haƙiƙance itace ta buge mashi waya.

A tare suka fito daga É—akin Abbien nasu, gaishesa suka je suka yi.

Tsugunawa Bilal ya yi ya ɗauko wayoyin dukka biyu, ya damƙa mata nata a hannunta tare da kama hannun nata ya turata cikin parlourn, sannan ya miƙawa Ramish ɗin ma nasa yana faɗin. "Sorry bro".

ÆŠan binsa da kallon mamaki Dr Raj ya yi. "Amma Yah Bilal ni kam me haÉ—inka da wannan aljanar yarinyar ne?". Kasa hakura ya yi sai da ya tambaya, dan abin yana bashi mamaki yadda Bilal É—in yake yi mata mugu mugun saukin kai, ko Sharifat baya yi mata irin hakan.

Wucewa Ramish ya yi ba tare da ya karɓi wayar tasa ba, bayansa suka bi Bilal yana faɗin. "Dr tausayi take bani kawai". Ya faɗa yana cusa wayar Ramish ɗin a cikin aljihunsa, dukkansu shigar Arabs jallabiyas ne a jikkunansu.

Ta jima a tsaye a bakin kofar parlourn ta gaza motsawa daga in da take, raɗaɗin marin nasa ne yake ratsa tsoka da jijiya har izuwa ɓargon kashin jikinta, bata taɓa jin mari mai zafin wannan ba, kai ko marin gandurobobin gidan yarin AAJ bai kai ko rabin nasa a zafi ba, ko marin su Omaid da suke twins bai kai nashi zafi ba, har ta ji duniya ya canza mata.

Sautin muryar Ummie da ya daki dodan kunnuwanta ne yasa ta farga ta dawo cikin hankalinta, firgita ta yi tare da zaro idanun, ba komai Ummien ta ce mata ba face me ya kawota part É—in mijinta?.

Murya na rawa ta ce. "Sharifat ce ta kirani wai na zo".
Da hannu ta nuna mata hanyar barin parlourn ba tare da ta yi magana ba. Da sauri ta juya har tana haɗawa da ɗan gudu gudu. Tamkar zata kifa ƙasa, a haka ta wuce ta koma ɗakinsu.

A saman gado ta kwanta tare da kunna wutar screen ɗin wayar tata. Ajiyar zuciya ta sauke ta sanya hannunta guda ɗaya a saman kumatunta in da ya mareta, ƙasa ƙasa ta ce.

"Mugu azzalumi Allah zai saka mun, ashe haka kake bakin mugu, ai dole ne ma jama'a su nemi kashe ka, daga gani ka zalunci mutane dayawa ne, sai Allah ya saka masu, idan ka yi wasa ma makiya ne zasu kasheka a kan titi, daga É—an yi karo da kai kawai ka sauke mun wannan hannun naka kamar na samudawa, Allah ya isa na". Tana surutan tana cire password na wayar dan ta duba massages É—in da ya shigo cikin wayar tata É—azun kafin su yi karo da shi.

A wani irin zabure ta miƙe zaune, wani irin razana ce ta bayyana a saman face ɗinta lokacin da ta ɗaura idanunta a kan saƙo. A ruɗe kuma a fili ta furta. "Who give them my number? A iya sanina only Sharifat ce kawai take da numberta, ko shi Yah Bilal da ya saya mana wayoyin bana tunanin yana da number.

Mamaki ne ya kusa kasheta, har ta kasa karanta sakon, wani irin fargabar abin da zata ji dangane da sakon ne ya kamata, yau kuma dame suka zo? Infact a ina suka samu contact ɗinta?...... Idan kun fahimci wani abu my people's, masu nikaf fa basu da wani zaɓi ne da ya wuce dole su sake nemanta, dan itace kawai ta samu damar da babu wata da taɓa samun makamancinsa a gidan, babu yar aikin da aka taɓa yantawa sai ita, sun san yanzu ta zama yar gida zata ƙara kutsawa cikin family sosai, ta samu wajen zama, yanzu ne ma aikinsu zai tafi yadda suke so cikin farinciki, dole su nemota su lallaɓata, shiyasa suka sake yi mata text a kan zasu sanyata aiki na karshe wanda ba mai wahala ba ne, amsa kiran waya ce kawai zata yi idan lokaci ya yi, daga wannan aikin amsa call ɗin da zata yi shikenan zasu bata babanta su kuma mayar da ita kasarsu.

Jin hakan yasa ta miƙe zaune, wani irin gumi ne ya fara tsastsafo mata daga gefe fuskarta. Tunani ta fara yi a kan in dai amsa call ne kawai ai gara ta yi masu su bata babanta.
Chapter 113 · 0% Book details