← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 208 OF 211

Sashe 208

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai wannan mai keken napep yake tsala gudu suna neman wannan mata, a hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauƙa gari yana kara duhu sosai, amma har e wannan lokaci Zee bata cire rai da samun nasaran ganin wannan mata ba, ta dafe kanta da yake barazanar tarwatsewa tana karanto dikkan addu'oin da suka zo bakinta, shi kansa mai mashin ɗin addu'a yake tayata da shi yana aikin tsinewa wancan mata albarka, shi ma bahaushe ne ɗan Kano, neman na halaliyarsa ya kawosa Abj.

Basu yi wani tafiya sosai tsakaninsu da asibitin ba suka tsinkayo hanyoyin biyu sun rabe a wajen, ɗaya ya yi ta cikin daji ɗayan kuma ya ƙarisa kutsawa cikin gari.

Shi kansa mai keken napep ɗin hankalinsa a tashe ta yadda baya gane me yakamata bare kuma ita Zee, sai dai dik da halin da take ciki bata bari kaifin ƙwaƙwalwarta ya dishashe ba, wannan guy ɗin zai wuce da su ta hanyar da ya kutsa cikin gari sosai ne ta ce mashi.

"A'a mu bi wannan hanyar da ta bi cikin dajin nan".

"Meyasa zamu bi nan?". Ya jefa mata tambayar yana É—an rage gudun mashin É—in dan kada su nisanta da wannan hanya.

"Saboda babu wani mai gaskiya da zai bi hanyar dajin nan a irin wannan lokaci, haka zakila babu wani mai hali irin na matar nan da zai saci yaro a irin wannan lokaci ya bi hanyar cikin gari da shi, bata da gaskiya, so ƙoƙarin ɓoye kanta zata yi, dan haka mu bi nan in da rabo sai kaga Allah ya haɗa mu".

Ya gamsu da maganganunta da hujojinta ya kuma jinjinawa kaifin tunaninta da hangen nesanta, dik da tana cikin damuwa bata bari hakan yasa ta rasa nutsuwar da zata fiddawa kanta mafita ba, haka ake son mumini mai zuciyar imani, a dik lokacin da wata ƙaddara ta faɗowa bawa so ake ya nutsu ya koma ga Allah dan gudun kada ya sake tabka asara a cikin asara.

A hanzarce ya juya kan mashin É—in suka bi wannan hanyar, a lokacin ruwan saman ya kara yawaita irin wannan ruwa wanda babu iska babu tsawa, sai dai ku ji yana zuba shaaaaaaa haka.

Basu yi nisa a kan wannan hanya ba tun daga nesa suka ga ansanya hannu a saman hanyar alamar ana son tare abin hawa.

Sam bai sanya alamar tsayawa ba ya yi niyar wucewa. Ita kuwa Zee idanunta suna a kan wadda ke ƙoƙarin tsaidasu ɗin dan taga wanene or wacece a cikin ruwan saman nan ga dare kuma take neman abin hawa.

Gab zasu wuce ba tare da sun tsaya ba Zee ta yi ihun cewa wlh wannan mata ce ya tsaya ita ce. Ai matar tana jin haka ta bar bakin hanyar a guje ta shiga ta cikin dogayen ciyayin dake gefe gefen wajen.

Wani irin mahaukacin birki mai mashin É—in ya ja, a miliyan ya fito ya bi bayan matar, haba Zee ma a miliyan ta bi bayansa tanata faÉ—in Alhdulillah babu iyaka.

Kun san ba zaku haÉ—a gudun mace da namiji ba, hakan yasa ya yi saurin cin mata, yana gab da zai kamata ta jefar masu da babyn a kasa ta kara karfin gudu da iya karfinta ta kutsa cikin daji, dan tasan me zai biyo baya idan asirinta ya tonu, a tunaninta gara ta rasa wannan jariri da ta tsaya su kamata su yi mata ihu jama'a su taru asirinta ya tonu.

Allah sarki bai bi bayanta ba ya dakata a miliyan ya ɗauki jaririn dake kuka kamar maƙoshinsa zai ɓalle, bawan Allah ya ji wuya, farkon zuwansa duniya ya fara da shiga ruwan sama mai sanyi, ga shi dan bakar mugunta matar ta jefar da shi a ƙasa, kila ya buge ne ko ya ji ciwo yasa yake ihu haka.

Dai'dai lokacin Zee ta ƙariso wajen tana haki sama sama. Jikinta har ɓari yake yi wajen kai hannu ta karɓi jaririn. Guy ɗin ne ya ce. "Ki yi sauri mu bar cikin ruwan nan da shi".

Ai tun bai ƙarisa magana ba ta wuce gaba da sauri ta, tana zuwa ta afaka cikin napep ɗin da sauri.

Yana zuwa shi ma ya shiga da gudun gaske ya ja mashin É—in, basu zame ko'ina ba sai asibiti in da Khadija take.

Suna isa yana kashe mashin É—in Zee ta fito da sauri ta koma cikin hospital É—in, bayanta ya bi shi ma domin ya ce mata ta zo su canza asibiti kada wani matsalar ta sake faruwa.

ÆŠakin da Khadija take ta koma, har lokacin Khadija bata motsa ba kamar dai da gaske babu rai a jikinta.

Mai napep yana zuwa bai ɓata lokaci wajen shiga cikin ɗakin ba. A gefen Khadija ta kwantar da babyn, zanin da matar ta kudundune shi a ciki ya jike, yaron ma ya dai'na kuka sam, kamar dai ya yi barci ne ko ya suma.

A gaggauce ta janyo akwatin kayansu dake a cikin ɗakin. Sauri sauri ta buɗe akwatin ta ciro zanin Khadija, jikinta har rawa yake yi wajen miƙewa ta karisa wajen babyn.

Sauri sauri ta cirosa daga cikin wannan jikakken zanin ta sanya na Khadijah da ta ciro ta kudundunesa a ciki.

Guy ɗin yana ƙoƙarin yi mata magana suka ga anturo kofar ɗakin an shigo. Wata nurse ce ta shigo, sai a lokacin Zee ta lura ashe ba'a labour room aka kawo Khadija ba, wani ɗaki ne na daban.

Ƙarisowa ciki nurse ɗin ta yi, tana ƙoƙarin yin magana guy ɗin nan ya rigata da cewa. "Madan muna da buƙatar canza hospital".

Kallonsa ta yi kafin ta ce. "Anyi maku laifi a nan ne?".

"Ko anyi mana laifi ko ba'ayi mana ba mu dai canza hospital zamu yi, ko bamu da ra'ayin zaɓar asibitin da dik muke so ne?". Yana magana yana buɗe mata ido irin ta san shi fa ba da wasa yake yi ba kuma ba zai ɗauki wani iskanci ba!!.

Ɗan siririn harara ta wurga mashi kafin ta ce. "To umma ta gaida A'isha, kufi ruwa tafiya in kunga dama, amma ai sai kun biyamu kuɗin aikin da muka yi maku da gado, haihuwa da muka karɓa da sauran abubuwa".

"Nawa ne kuÉ—in naku?". Ya faÉ—a shi ma yana harararta. Guy É—in idanunsa a buÉ—e suke, da alama wayayyene sosai.

Zee dai ba ta su take yi ba, bata ma ko jinsu, hankalinta yana kan yadda zata kudundune wannan baby ya ji dumi, shi ne a gabanta, bama ta bi ta kan Khadija ba tukun nan, sai a yanzu kuma idanunta suka ciko da kwallah tab.

"Dubu shabiyar ne kuÉ—inmu". Ta faÉ—a a gadarance.

Bawan Allahn nan da yake yana da zuciyar kirki sai ya ciro atm card daga aljihunsa ya ce da Zee yana zuwa bari ya je waje ya nemi mai pos ya cire masu kuɗinsu su basu sai su karɓi sallama su tafi wani hospital ɗin.

Zee da hankalinta baya jikinta ai ko amsa mashi bata iya yi ba, sai da ta sanya zannuwa har uku ta kudundune yaron nan da kyau, sannan ta mayar da sauran kayan nasu cikin akwati, ta matso kusa da Khadija tana cigaba da ambatar sunanta.

Shiru bata motsa ba, shi ma babynta bai motsa ba har wannan mai keken napep ya je ya ciro kuɗi ya dawo, nurse ta yi mashi jagoranci zuwa in da zai biya kuɗi ya karɓi sallama su zo su haɗa kayansu su tafi.

Sosai Zee ta zauna a gefen gado tana ruwan hawaye, wani na bin wani zafafa da su, har wa lokacin jikinta kerma yake yi. Baiwar Allah taga wahala taga bone!!.

Ba ƙaramin tausaya masu wannan mai napep ɗin ya yi ba, wannan ma bai san ainahin labarinsu ba, bai san tashin hankalin da suka shiga a baya ya wuci na yanzu ba.

"Baiwar Allah ki ta shi Æ´ar uwar taki mu je na kaiku wani asibitin mai kyau da tsaro wan da ya fi wanna, dan kada makamancin abin da ya faru sake faruwa da ku". A tunaninsa Khadija barci take yi.

Cikin kuka murya a marairaice ta ce. "Ai taki tashi, tun da nazo nike ta ƙoƙarin tashinta amma taki".

Matsowa kusa da su ya yi dan ya gani ko dai suma ta yi. Da yake dai ya fi Zee shekaru kuma namiji ne shi É—an gwagwarmaya, anga jiya anga yau yana ganinta sai ya gane ba barci take yi ba suma ta yi ko kuma mutuwa.

Hakan yasa ya ce bari ya nemo ruwa a waje ko pure water ne su zuba mata su gani suma ne ko dai rai ne ya yi halinsa.

Zee dai bata ce ko uppan ba ta bishi da kallo tana tunanin ko dai shi ma cutar da su zai yi ne, dan ita a yanzu dik wanda ya nuna zai taimaka masu gani take yi shi ma kawai wani abin ya biyo a tattare da su, kwata kwata yanzu babu yarda da ko leda ce bare dabba bare mutun a zuciyar Zee, sai dai ta bi kowa kawai da ido.

A hankali baby ya fara motsawa. Da sauri Zee ta kai kallonta a kansa. Cikin gaggawa ta sa hannu ta ɗaukesa tana ƙoƙarin ɗan buɗe mashi fuska ya shaki iska, dan ita da taga kamar yana jin sanyi over sai ta kudundunesa har da rufe mashi fuska ta bar iya yadda numfashinsa zata iya fita kawai.

Tana buɗe fuskar tasa miƙa babyn ya yi tare da zabga hamma sannan ya waro idanunsa waje. Ya subhanallah, idan baka sani ba ko kwana za'ayi ana gaya maka Khadija chocolate colorn nan ce ta haifo wannan babyn ba zaka taɓa yarda ba, saboda yadda ya fito a bature sak babu mix, fari tas da shi, yanayin skin ɗinsa ma ya fi kama da Koreans ne ba ainahin turawa ba, gashin kan nan nasa golden white ne irin na Sweetie, ga lips ɗinsa dark purple, gashin kansa ya sauko mashi har gaban goshi yana rufe mashi idanu, ɗan fuskar nan dan daidai, kai kace bashi da baki saboda kankantarsa, idanunsa manya manya a waje, ga su launin ash colar mai haske hakan yasa suke kyalli sosai.
Chapter 208 · 0% Book details