← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 211

Sashe 162

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin girmamawa ya ce. "Ka yi hakuri daddyna, tuba nake yi, kunyarka nake ji yasa na ɓoye, to amma ba ga shi yanzu na gaya maka ba?".

"Yanzun ma ai sai da na ritsaka ne ka gaya mun". Ya yi maganar yana wurga mashi hararar wasa.

"To daddy sorry, dan Allah a bani ita kada a wahalar da ni, kuma daddy kamar yadda ka ce ayi mana aure a satin nan ɗin na yarda ka ji my hero?". Yana magana yana ɗan turɓune fuska zai yi wa daddy shagwaɓa.

Hannu uncle Abbas É—in yasa a gefen cikin É—an nasa ya fara yi mashi cakulkuli yana faÉ—in. "Eyeee my son ya girma zai zama ango".

Dariya sosai ya fara yi yana faÉ—in. "Kai daddy ka bari mana, zaka sa cikina ya yi ciwo".

Cigaba da yi mashi ya yi yana ta dariya har da hawaye, da yaga ba zai dai'na yi mashi ba sai ya kwanto jikinsa ya rukunkume shi ta ko'ina ya hana shi yin wani motsi, dan dole ya dakata taga yi mashi cakulkulin ya rungumeshi suna ta dariya gwanin birgewa.

Sai da uncle Abbas ya tabbatar ɗan nasa ya yi farinciki sosai sannan ya miƙe ya nufi waje yana faɗin zai yi magana da King a kan batun kafin su sanar da Akka halin da ake ciki.

Cike da tsantsar farinciki babu ko kunya ya hau zubawa daddyn nasa godiya ba adadi, har tsokanarsa uncle Abbas ya yi a kan wato baya jin kunyarsa ko?.

Yana fita ya miƙe ya faɗa cikin toilet, dan an fara kiraye kirayen sallar mangariba. A gaban mirror dake kusa da wash hand base ya tsaya yana kara kallon zanen janbakin dake saman kumatun nasa, hannu ya kai ya shafa wajen yana jin matuƙar farinciki sosai.

Uncle Abbas kuwa yana fitowa ya nufi part É—in King, a hanya suka ci karo da Chuchu da ta fito daga part É—in ita ma zata je wajen Auta a É—akin momma ta bata labarin soyayyarta da Yah Jawad É—inta.

Tsabar sun samu tarbiya wajen momma har ƙasa ta tsugunna zata kwashi gaiwa kanta a ƙasa. Ai tsabar farincikin da uncle Abbas yake ciki na ganewa da ya yi suna soyayya da ɗansa bai san lokacin da ya ɗagota ya rungumeta yana murmushi ba. Ya sha rungumarsu sosai, amma sai ta ji na yau ya yi daban, dan wani irin rungumar farinciki ya yi mata, ji yake kamar ya mayar da su cikin jikinsa saboda farinciki, bai san lokacin da ya hau zuba mata ruwan albarkoki ba adadi ba, tun tana amsawa da amin har ta kwanta shiru a jikinsa tana mamakin meyasa yau ya tsawaita addu'arsa a gareta? Bata san ya san komai ba.

Ya ɗauki tsawon mintuna 5 yana zuba mata addu'a kafin ya saketa yana shafa kanta. Ƙasa ta yi da kai ta yi shiru kamar wata amaryar da ake yi wa nasiha.

Wucewa ya yi baki yaki rufuwa ya shiga part É—in King, ita kuma ta wuce ta nufi na Momma.

Momma kawai ta samu a ɗakin, zama ta yi kusa da ita suka ɗan yi hira kamar na 30 mins haka, sannan ta miƙe tare da cewa Mommar bari ta je ta duba Auta a part ɗin Akka, da okey momma ta amsa mata. A lokacin kuma Auta suna tare da Hoorain da uncle Taheer wajen da suka samu wancan miss understanding ɗin nan.

Part É—in Akka ta nufa, yau dai kaya marasa nauyi ne a jikinta, doguwar riga ce mai karamar hannu, bata da wata kwalliya sosai a jikinta, ta sanya malesian cap a kanta mai shegen kyau, irin waÉ—an nan Æ´an huluna marasa nauyin, masu mannewa da kan mutun.

Kai tsaye room É—in Akka ta nufa. Sai dai bata kai ga shiga room É—in ba ya rufe mata idanu ta baya tare da É—aukarta cak sai cikin room nata dake cikin part É—in.

A tsakiyar É—akin ya sauketa tare da zagowa ta gabanta. Ya yi wanka ya shirya cikin arab jallabiyar fara tas, da alama massalaci ya fito, sai tashin kamshi yake yi, ya yi kyau sosai.

A tare suka sauke ajiyar zuciya na ganin juna da suka yi. Ƙasa ƙasa ta ce. "Yah Jawad ina wuni".

A É—an takaice ya ce. "Ban wuni ba".

ÆŠan zaro idanu ta yi, kamar zata yi kuka ta ce. "Kai Yah Jawad me kuma na yi maka?".

ÆŠan rage tsawonsa kaÉ—an ya yi. "Mema baki mun ba?".

Turo baki ta yi. "Me na yi to?".

Hannunsa ɗaya ya ɗaura a bayanta tare da matso da ita jikinsa, ya kara rage tsawonsa ya rankwafo kanta kenan, ƙasa ƙasa ya ce. "Waye ya ce ki sumbaci kumatu na? Ga shi yanzu kinsa daddy ya gani kin sa na ji kunya ko?".

Zaro idanun ta yi tare da É—ago kallonta a kansa, kashe juna da kallon kauna suka yi.

"Yanzu Yah Jawad da gaske daddy ya gani? Kuma me ya ce maka?". Tana magana tana kara zaro ido ga shi tana kallonsa.

"In gaya maki abin da ya ce?".

Kai ta gyaÉ—a da sauri. Iskar bakinsa ya hura mata a face É—inta, hakan yasa ba shiri ta datse idanunta gam, matso da face É—insa daf da tata ya yi, ya haÉ—esu, kamar kai raÉ—a ya furta.

"Cewa ya yi sai na gaya mashi wacece mamallakiyar wannan jambakin?".

A É—ari ta waro idanunta waje. "Amma dai Yah Jawad baka ce mashi ni ce ba ko?...........".

Ƙasa ƙarisa maganar ta yi jin yadda ya sauke ɗan bakinsa a saman nata.

"Waye ya koya maki sumbtar mutun ma tukun nan?". Ya yi maganar lips É—insa suna saman tata.

"A wajenka na koya". Yadda ta yi maganar sai ka rantse da Allah battery aka sakawa yar tsana, idanunta a buɗe garau tana kallon nasa, kamar dai wadda ta yi suman tsaye kuma, ba zaka taɓa cewa ita ta yi maganar ba kamar wata Robbot ta koma.

"A yaushe na koya maki ni kuma? Ko yaushe kika taɓa ganin na sumbaci wani?".

Yana magana suna kallon cikin idon juna babu ko kyaftawa.

"Ba kai ne ranar da na yi barci a room naka ka dawo dani room nawa ka kwantar da ni kafin ka fita sai ka sumbaceni a goshi ba? Daga ranar na koya, shi ne nima na yi maka yau".

ÆŠan zaro idanu shi ma ya yi. "Kenan baki yi barci ba ranan?".

Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Okey bari in yi maganinki yanzun nan, wato idanunki biyu kina jina ko? Kin ga komai ko?A haka kuma kika wahalar da ni wajen nunawa kamar baki san ina sonki ba ko? Allah ba zan kyaleki ba".

Ɗan raba jikinta da nasa ta yi, ta sanya hannu ta riƙo waist ɗinta, tana jujjuya fararen idanunta ta ce.
"Ni dai babu yadda zaka yi dani! Kuma kai Yah Jawad dama so kake yi in ce na gane kana sona tun baka furta mun ba? To ai idan na yi haka ban cika mace mai aji ba! A'a ni ina da ajina dole na ja class, na san komai kawai wahalar da kai nake son yi kamar yadda ka yi ta bani punishment a baya". Tana magana tana É—an girgiza weist É—in nata.

Ai mutuwar tsaye ya yi, ta kwance mashi notikan ƙwaƙwalwa, iyee ashe ita ma tasan komai kawai tsiya ce irin tata.

Cigaba da jujjuya fararen idanun nan nata sama ta yi tana faÉ—in. "Allah Yah Jawad nima ai ka wahalar da ni da kaki bayyana mun soyayyarka da wuri, ka azabtar da zuciyata........".

Bata kai karshen maganar ba ta yunƙura zata kwasa a guje, sakamakon capka da ya kai hannunsa zai yi mata.

Ai kuwa ta gudu bata tsira ba, dan kuwa a dubu ya capkota tare da jawota jikinsa, yarinyar nan ta wahalar da shi, wato dama dik wasu take takensa tana sane da su, tsabar iyashege ne ta bar shi ya wahala wai ita tana jan aji, to wlh yau sai ya tsinke ajinan Æ´ar kaniya kawai, har da wani girgiza mashi weist da wani yin fari da ido, ta sanya ya faÉ—a cikin yanayi dan iyashege.

"Wayyo my melody ka yi hakuri ka ji? Na tuba ba zan sake na". Tana maganar da É—an ihu.

Mannata da jikinsa sosai ya yi, ya ƙanƙameta ƙasa ƙasa ya ce. "Nutsu in gaya maki wata magana".

Jin haka yasa ta nutsu tsit É—in.

"Meyasa kika wahalar da ni to?".

Hannunta É—aya ta É—aura a saman weist É—insa ta baya, ta rungumo shi da kyau, É—ayan hannun kuma ta É—aura saman kirjinsa, cike da so da kaunarsa, cikin salo mai É—aukar hankali ta ce. "Saboda na ja ajina mana Yah Jawad, yanzu kaga ai zaka soni sosai".

Murmushi ya sakar mata tare da kai hannunsa ya riƙo hannunta dake saman kirjin nasa, ya ɗan matse hannun nata kaɗan kafin ya rankwafo kanta.

"I really love Jannat, ke É—in ta daban ce a rayuwata, please ki so ni ko da rabin wanda nake yi maki ne kin ji?".

"Yah Jawad a gaskiya son da nake yi maka yafi wanda kake yi mun, kasan yadda nake sonka kuwa?".

Ƙasa sosai ya yi da murya. "Da gaske?". Yadda ya yi maganar zaka gane da kyar ya iya yinta, idanunsa a kan lips ɗinta.

Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e. Tana yi tana jujjuya idanun nan nata sama.

Ai kasa jurewa ya yi, yadda take magana a kusa da shi, yadda take juya waÉ—an nan fararen idanun nata sama tana rikita shi, yadda take motsa kyawawan lips É—in nan nata ya ji ba zai iya gani ya kawar da kai ba, ba zai iya hakura ba, ya zo har wuya yau

Shammatarta ya yi ba zato ba tsammani sai ji ta yi ya capki lips ɗinta na ƙasa ya fara bata hot kiss. Zaro idanu ta yi tamkar kwayar idanun nata zasu faɗi ƙasa, hannu yasa ya rufe mata idanun nata da shi saboda kada ma ya kallesu ya ji zai dai'na.

E Jawad ya fi karfina gaskiya, my people's ina zuwa🥱😂.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
Chapter 162 · 0% Book details