← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 211

Sashe 132

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har zai rufe mashi fuska da rigar tata sai kuma wani tunani ya faÉ—o mashi, tunawa ya yi da idan ya kuskura ya rufe mashi fuska da rigarta fa to ba shakka zai gane cewa Autar tana wajen, dama ya yi niyar ya É—aure mashi fusa da rigar tata ne sosai sai su gudu, kunga kafin ya samu ya kwance face É—in nasa ya bisu ma sun kurewa ganinsa sun yi nisa, amma sai ya tuna to ai zai gane rigarta ce, in hakan kuma ya faru to fa tabbas yau ba zaman lafiya a wannan masarauta, tabbas sai hankalin kowa ya tashi.

Tuna hakan ne yasa ya fasa kudurin nasa, a hankali ya fara sanÉ—o da ita a bayansa suka bi ta bayan bishiyar, uncle Taheer yana ta gaba su kuma suka bi baya, cikin dabara ya samu ya bar arear wajen.

Suna fita kuma ya rasa ina zai yi da ita, ga ko'ina da haske tamkar rana, mayaƙa suna ta shawagi, idan aka gansu a tare kawai ma ya shiga uku bare kuma a ganta goye a bayansa.

Duk ya ruɗe hankalinsa a tashe bawan Allah, sam bai ma san lokacin da ya wuce room ɗinsa da ita ba, ba zai iya sauketa a wajen ya ce ta tafi ba, dan babu riga a jikinta, ɗan banzan kishi ba zai iya barinsa ya yi hakan ba, zai ga ai kowani mayaki idan zai wuce zai ganta kafin ta isa cikin part ɗinsu, idan kuma ya ce zai tsaya sanya mata rigarta to fa tabbas za'a iya ganinsu, dan mayaƙa masu gadi suna ta going up and down a cikin harabar kingdom ɗin dan tabbatar da tsaro.

Suna shiga ɗakin nasa ya banko kofa tare da murza key, a hanzarce ya sauko da ita daga bayan nasa, jikinsa har tsuma yake yi wajen miƙa mata rigarta dan tasa yasan ta yadda zai yi ya mayar da ita cikin gida.

Yana jiyowa da nufin ya miƙa mata rigar idanunsa suka sauƙa a kan haɗadɗen lallausan surar jikinta, fata kamar na jarirai.

Ai a dubu ya kawar da kallonsa while ita ma ta yi ƙasa da kai. Miƙa mata rigar tata ya yi ba tare da ya sake juyowa ba, da kyar ta iya karɓa ita ma saboda kunyarsa da ya kamata, ga shi vest ɗin jikin nata a dai'dai cibiyarta ya tsaya mata, ya kalle mata plat tummynta da sauran sassan jikinta.

Mayar da rigarta jikinta ta yi, wani irin yanayi na tsananin kunyarsa ta tsinci kanta a ciki.

"Muje na rakaki ko?". Ya faÉ—a ba tare da ya juyo gareta ba.

Ɗakin nasa ta fara bi da kallo tana mamakin irin tsabtarsa, komai nasa kamshi yake zubawa, ga ɗakin nasa ɗan dai'dai, sai dai akwai komai da duk wani ɗan adam zai buƙata a cikin bedroom dan more rayuwa, bed ɗinsa dake shinfiɗe da up white bedsheet ne ya yi matuƙar burgeta, ashe dai ya iya aikin mata.

Kallonta ta kai saman zabgegiyar takobinsa dake rataye a jikin bango, abin ya burgeta.

Can ta hango wani hoto dake saman bedside drawer ɗinsa cikin frame, an ƙawata shi sosai da kwalliyar flowers masu ɗaukar hankali.

Dawo da kallonta a kansa ta yi tana mamakin hali irin nasa, idan ka gansa a dake cikin jarimta kamar bashi da wani shaukin a kan soyayya, ashe É—akinsa harda kwalliyar flowers, ashe dai ya san love kawai dai jarumta ce ta fi soyayyar yawa a jinin jikinsa har ta rikiÉ—ar da shi har haka, da zai samu wadda zata farfaÉ—o mashi da soyayyar tuni zai taso da tasa, irinsu ne idan suka fara zuba love sai ka rasa ta ina suka koya.

Raɓawa gefensa ta yi zata wuce dan ta je ta ɗauki hoton taga su wanene? Ta dai hango har da ƙaramin yaro a cikin hoton, ga kuma mace da namiji wanda idan ba gizo idanunta suke yi mata ba sai taga kamar commander Zafar ne lokacin yana ɗan matashi matashinsa, to waye ƙaramin yaron kenan?. Ta jefawa kanta tambaya, taso amsar ya kasance Hoorain ɗin nata ne dai, hakan yasa ta nufi hoton da sauri dan ta tabbatar, sai dai bai bari ta ƙarisa wajen ba ya yi saurin riƙo hannunta.

A hanzarce ta juyo da kallonta a kansa, da sauri ya kawar da idanunsa daga kanta dan baya son su haÉ—a ido.

"Hoorain ka bari mana, hoton can zan je na kallah". Kamar zata yi kuka ta yi mashi maganar.

Jin ta ambaci hoto yasa ya yi saurin kai kallonsa kan hoton, ai kuwa a fujaje ya saki hannunya ya je ga ɗauke hotonsa da nufin ya ɓoye.

A hanzarce ta ƙariso wajensa tana yin ɗan kukan shagwaɓa a kan ya bata ta ga su wanene?.

Kin bata ya yi saboda baya son ta gansa yana yaro, ga shi a hoton mamarsa ta haÉ—a shi da nama a hannu ta kuma cusa mashi wani a baki bai gama haÉ—iyewa ba, duk dan ya yi shiru a É—aukesu hoto, kuka yake ta yi, hakan yasa kumatunsa suka kumburo a hoton, abin gwanin ban dariya, shiyasa baya son ta gani.

Kuka ta fara yi mashi tare da fara ƙoƙarin kwatar hoton daga hannunsa.

Hannun nasa ya É—aga sama kafin ya ce. "To ki kwata ki gani mu gani idan kina da tsawo".

Tsalle ta fara yi tana son kwata sai dai ina ta kasa, dan kuwa komai tsallen da zata yi bata kusa kamawa ma.

Dakatawa da yin tsallen ta yi tare da juya mashi baya ta harÉ—e hannayenta a saman kirjinta a dole ta yi fushi.

Ganin haka yasa ya sauke hoton, a hankali ya dawo ta gabanta ya zamana suna fuskantar juna. Hoton ya miƙo mata ba dan ya so ba sai dai fushin da ta yi bai so hakan ba, cikin sanyin murya da sigar rarrashi haɗe da tausasawa ya ce. "Am so so sorryyyyyyy ranki ya daɗe, tuba nake yi, ga hoton nan ki gani".

Yadda ya yi maganar da ka jita zaka san bata kai har cikin zuciyarsa ba, saboda baya son ta gani gaskiya.

Ba tare da ta ɗago da kallonta a kan hoton ba ta furta. "Dukkan abin da my hero zai ce baya so to nima bana buƙata, dan haka na fasa ganin hoton ka ajiye shi kawai".

Maimaita sunan my hero da ta faɗa ya yi a cikin zuciyarsa, haƙiƙa ba yau ta fara ce mashi jaruminta ba, amma na yau da ta faɗa sai ya ji sunan ya yi mashi wani irin daban.

"Da gaske nake yi ranki ya daɗe ki ƙarɓa ki gani kin ji? Dan Allah ki dai'na yin wannan fushi ko?".

Cool murmushi ta sakar mashi tare da dawo da kallonta a kansa, tamkar wata babbar mace tasa hannu ta karɓi hoton, ba tare da ta kallah ba ta nufi saman drawer ta ajiyeta, a hankali ta juyo garesa, murya mai cike da kulawa ta furta. "Wani lokaci idan na zo zan kalli hoton, yanzu dai bani rigar taka na tafi". Tana magana tana matsowa in da yake tsaye, kallonta kar a kan face ɗinsa.

Ajiyar zuciya ya sauke, yau jin kansa yake yi tamkar ba'a duniya yake ba, ya kasa yarda cewa yau Gimbiya Zunaira ce a cikin É—akinsa, abin ya tsaya mashi a rai, anya zai iya rintsawa yau kuwa? Ya jefawa kansa tambaya.

Ya shagala da tunani bai san lokacin da ya kafeta da kallo har cikin ba, sai dai jinta ya yi ta sanya tafukan hannunta cikin nasa tana faÉ—in. "Tunanin me kake yi kuma kallon me kake mun?".

Nisawa ya yi tare da buÉ—e baki zai yi magana kenan suka jiyo knocking na kofar É—akin da karfi.

A tare suka wani irin zaro idanu kamar kwayar idanun nasu zai faɗi ƙasa.

My people's wa kuke tunanin ya buga masu kofa? Me zai faru a wannan dare?.

A can cikin gida kuwa, nemanta King Zuhair yake ta faman yi a ɗakunan ƴan uwanta, dama kunsan yana zuwa yi mata addu'a a kowani dare, to ya je room nata zai yi mata addu'a ne bai sameta ba, ya je ɗakin Mommarta bata nan, ya leƙa na Chuchu bata nan, izuwa yanzu hankalinsa ya fara tashi, ga shi Guyson ma yana ɗakin Mommarsu bare ace suna tare, sarkin kwalafucin uwa ba, yaka manne da ita yaki matsawa.

Me kuke tunanin zai faru idan King bai ganta ba? Akwai cakwakiya gobe, ni dai suna yi ina shan Maltina mai sanyi, to me yafi rai'na?.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 6/11/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥

35

A tare suka dawo da kallonsu a kan juna, sun kasa motsawa daga in da suke, dukkaninsu faÉ—awa suka yi duniyar tunani.

Ita kanta Autar ta yi matuƙar tsorata, zuciya da iya shegen jefa mutum cikin mugayen tunani da saƙe saƙe, musamman idan mutum yana tsorace da abu to wlh zuciya ta rinƙa kara mashi tsoro ta hanyar jefa mashi munana tunane tunane.
Chapter 132 · 0% Book details