← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 211

Sashe 176

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kada kuso ku ji wani irin ajiyar zuciya mai shegen daÉ—in da ya sauke jin ta kwanto a jikinsa, hakan yasa ya juyo gareta tare da amsa kiransa da ta sake yi.

"Kayi hakuri hamma". Ta faÉ—a kamar mai tsoron yin magana.

Shiru bai iya amsa mata ba saboda wani irin daɗi da yake ji, ya kasa yin magana, sai dai ya rungumeta tare da kai hannunsa saman ƙugunta, ya cigaba da wasa da beat ɗin idanunsa a lumshe.

Biye mashi ta yi ta hanyar kwamciya shiru a jikinsa tana sauraro dik abin da yake yi mata.

My people's nasan kuma zaku so ganin yadda za'a kalli juna da safe ko? Mata kunya miji kunya, wlh suna bani joy, to bari dai mu je wani ɓangaren mu dawo, watakila kafin mu dawo garinsu ya waye.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A..✍️🔥🕊️

ABUJA.

Bayan wasu lokuta!!.

Wani É—an madaidaicin restaurant ne irin wanda matafiya suke tsayawa su ci abinci a wajen, daga ta cikin restaurant É—in akwai É—akin mamallakiyar wajen, wato in da take kwana kenan, jama'a sai hada hada suke yi, suna shiga suna kuma sake fita, masu cin abinci suna ci masu aikin suna yi.

A ta bakin hanya restaurant É—in yake.

ÆŠauke take da tray mai É—auke da plate É—in abinci har kala uku take ta nufi teburin abinci dake fuskantar kofar shigowa, daga ganin yanayin yadda take tafiya zaka iya fahimtar tana cikin tsananin damuwa da rashin lafiya.

Maza biyu da mace guda É—aya ne a zaune a saman teburin, su tazo ta zubewa abincin, kamar zata kifa a kansu ma haka ta ji.

Daga bayanta wata yar lukutar mata gajeriya kakkarfa ta ce. "Zainab amma nace ki bar aikin nan sai kin samu karin lafiya ko? Ki je wajen Æ´ar uwarki ku kwanta ku huta".

Juyowa ta yi idanunta jajir da su. "Ai na samu lafiya Aunty". Ta yi maganar tana tinkarar matar.

"Dik da haka ni dai ki je ki huta". Da to ta amsa mata tare da wucewa can cikin É—akin matar.

A nan ta isko Khadija tana kwance saman Æ´ar katifar dake a É—akin, ta tada kai da jakar kayansu, ta tasa wani hoto da kallo, rike take da hoton a hannunta.

Zee tana zuwa ta leƙa hoton ai bata san lokacin da ta ce. "Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Hasbunallahu wani'imal wakil, Aunty Khadijah a ina kika samo hoton Balarabe ne ko Bature ne wannan? Kai kin gansa kaman shi ya yi kansa saboda kyau, kamar na san face ɗin nan nasa kuma, sai dai na manta a ina na taɓa ganinsa".

Tun da ta shigo ɗakin Khadija bata lura da ita ba har ta yi wannan maganar dikka bata jita ba, ta luluƙa duniyar tunanin wanda take gani a jikin hoton, tana ganinsa tana hawaye, ko daga ina ta samo hoton? Allah masani sai kuma alkalamina.

"Yauwa Aunty Khadijah kaman wannan shi ne wannan Jahiz ɗan kwallo da baba yake kallon wasansu kullum har yasa nima na fara supporting guy ɗin, kamar sun yi kama fa, anya ba shi bane kuwa? Kai dik da kullum cikin kayan ƴan kwallo nake ganinsa hakan ba zai sa na gaza ganesa dan yana cikin wasu shiga na daban ba, Allah ni dai nasan fuskarsa a cikin ƴan kwallon da baba yake gani, Allah yasa Jahiz ɗin ne, ina son guy ɗin nan over". Ta kai karshen maganar tana taɓa Khadija da ta yi nisa a wata duniya ta daban.

Tun tasowansu suka san babansu da kallon kwallo, yana mugu mugun kaunar uncle Jahiz namu dai nasu King Zuhair, saboda tsabar kaunarsa da yake yi yasa yake da tarin jaridu masu É—auke da sunansa, ko ban maimaita ba nasan kun san baban Zee dai yafi yawan kasancewa a tare da Zee, hakan yasa ita ma ta kamu da kaunar guy É—in, idan baku manta ba a baya nace maku tana son kallon kingdom of power ko a tv ne, to saboda uncle Jahiz take son kallon su King Zuhair.

Ta kaunacesa sosai kamar yadda babanta yake sonsa, kullum in dai wasansu ne sai sun kallah a tare da baban nata.

Wani irin firgita Khadija ta yi, a miliyan ta yunkura zata ɓoye hoton wai dan kada Zee ta gani, bata san ma ta riga ta gani har ta gama surutan da zata yi a kansa ba.

"Aunty khadina me kuma abin ɓoyewa? Dan Allah ki gaya mun kin san shi ne? A ina kika samu real hotonsa ba'a jarida ba kuma ba sanye da kayan kwallo ba? Wlh ya yi kama da Jahiz namu ni da baba". Tashin hankali uncle Jahiz namu kuma?.

Rai a É—an dakile ta ce. "Wannan ba Jahiz bane".

Shiru Zee ta ɗan yi tana ƙoƙarin tunano fuskar Jahiz ɗinsu ita da babanta, sai kuma tunanin baban nata ya faɗo mata, nan take idanunta suka ciko da kwallah.

Ita kuma Khadija ta yi maza ta ɓoye hotonta a cikin jakar da ta tada kai da shi. Wai shin mema ya kawo su Khadija Abuja? Ya aka yi suka kuɓuta daga hannun waɗan can mutanen, da gaske uncle Jahiz ɗinmu ne a jikin hoton dake hannun Khadija ko dai mai kama da shi ne? Hmmm akwai tashe tashen hankula fa. To sai mun haɗo gobe idan mai dukka ya kaimu ma ji dikka waɗan nan amsoshin, love u all guy's 💘

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️ 🕊️

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

45

ABUJA.

"Kai Aunty Khadijah wlh ya yi mun kama fa da Jahiz ɗinmu ni da baba, dan Allah ki gaya mun idan shi ne! Na yi iya tunanin da zan yi a kan kamanin Jahiz ni dai wlh ban ga wani canji ba, kaman shi ne". Ta yi maganar cikin ƙaguwa da son jin shin da gaske shi ɗin ne ko dai Khadijah ta fita gaskiya ba shi bane kama ce kawai?.

"Zee wannan ba Jahiz bane ba, ki daina wahalar da kanki, kuma ni ban ga kamanin Jahiz a tattare da wannan guy ɗin ba, kece dai kika gani". Da kyar ta idasa maganar, saboda wani irin kululum bakinciki da ya tokare mata maƙoshinta, ta tuna da abubuwan da suka faru da ita a baya.

"Shikenan Aunty Khadijah na yarda, amma meyasa kike ɓoye mun abubuwanki? Shin ni ba yar uwarki bace? Ko kina tunanin zan iya cutar dake kamar yadda Hauwa ta yi wa mama ne?".
Tun da ta fara magana idanunta suka karo kwallah.

Shiru Khadijah ta ɗan yi, dik jikinta sai ta ji ya yi mata mugun sanyi, tunani ta fara yi a kan idan ta cigaba da ɓoyewa Zee gaskiya to fa za'a iya samun matsala sosai a tsakaninsu, bata da biyun Zee yanzu a duniya, idan ta sa ƴar uwar tata ta fara zargin bata sonta ko bata ɗauketa da mahimmanci ba hakan zai sa ita ma ta fara ɓoye mata nata sirrin, ta kuma ja baya da ita sosai, sanadin hakan za'a iya samun rabuwar kai a tsakaninsu, a gaskiya ko zata ɓoyewa kowa bai kamata ta ɓoyewa Zee ba, yana da kyau ta gaya mata gaskiyar abin da yake faruwa.

"Aunty Khadijah ki yi hakuri da abin da na faɗa idan ya ɓata maki rai, amma ni a nawa tunanin tun da ke kika tashi na kwanta, ke kika sha kika sake na kama, ke kike fara sa kaya idan sun yi maki kaɗan ki cire na saka, komai kace a gaba ina biye dake, dik in da kika saka kafa kika cire next nawa kafan ne a wajen, sai nake ganin kamar na wuci ki ɓoye mun wani abin da ya shafi rayuwarki, amma tun da baki son na sani ba zan sake tambayarki komai ba". Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka, har ga Allah tana matukar jin ciwon ɓoye mata da Khadijah take yi...... Amma fa a nan wajen wlh Zee ta yi magana mai ma'ana, wato ita ta kwanta a ciki da ta fito sai ita kuma ta kwanta, ita ta sha nono ta sake ta kama, gaskiya ta yi magana a wannan waje, dik mai hankali kuma zai san tana da nutsuwa da iya magana.

Tun da ta fara magana Khadijah take binta da kallon tausayi da kuma so da kauna, har ta idasa zata miƙe ta fita ne Khadijah ta riƙo hannunta.

"Zauna mu yi magana". Ta faÉ—i hakan ita ma kamar zata yi kuka.

Ba musu ta koma ta zauna kanta a ƙasa, yau ta tuna da rayuwarsu ta baya, Jahiz yasa ta tuna da babanta, dik jikinta ya yi la'asar.

"Zee ina son ki sani ba wai ina ɓoye maki abu bane dan bana kaunarki ko ba ki kaina faɗa maki ba, zancen bana kaunarki ma ai bata taso ba, kin fi kowa sanin kece farinciki na, kuma idan da babu ke kin san da shaiɗan ya jima da cin galaba a kaina wajen zugani na hallaka kaina da kaina..............".

Dakatawa da yin maganar tayi tana ƙoƙarin share kwallar da take zubo mata, ta kuma sauke ajiyar zuciya.

"Kiyi hakuri, ni dama ina ɓoye maki wasu abubuwa ne dan ina ganin kamar baki yi girman da zaki iya rike wasu maganganu ba, amma ki yi hakuri, na miki alkawarin zan faɗa maki komai, kuma daga yau ba zan sake ɓoye maki komai da ya shafeni ba".

Tun da ta fara magana idanun Zee yake a kanta, ta ma kasa iya rarrashinta, so kawai take yi ta faÉ—a mata gaskiyar al'amari.
Chapter 176 · 0% Book details