Sashe 196
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zan iya Bilal". Shi ne abin da ya furta yana É—an É—aga kansa sama kamar mai tunanin wani abin.
Tun da Bilal ya ji ya furta kalmar zai iya sai ya yi shiru, dan dik san da kuka ji Ramish ya ce zai iya to fa sai dai ayi shiru, dan kuwa komai wahalarta sai ya yi ta ko da kuwa zata iya yin barazana da rayuwarsa sai ya aikata.
"Amma ka yi tunani a kan wanda ya turo mana wannan sakon kuwa?". Cewar Bilal.
Kai ya girgiza alamar a'a ba tare da ya furta uppan ba.
Dr Raj dake aikin latsa waya ne ya ce. "But the guy is very very smart and talented wlh, na sha madarar mamakin ganin Yah Ramish ya jinjina mashi, koma wanenen ya turo sakon nan shegen kwaro ne, ya kware a aiki over".
Sirrin tsaki Bilal ya ja kafin ya ce. "Shirmen banza, ni ba shi nake magana a kai ba, so nake mu yi tracking ɗinsa ta koma wace hanya mukamashi, daga nan ya gaya mana ya akayi ya sanmu ya kuma san komai da ya shafe mu da har yake ƙoƙarin taimaka mana! For what reason?".
Juyowa garesa Dr Raj ya yi tare da dai'na latsa wayar tasa ya ce. "Yah Bilal kai dai akwai saurin hawa wlh, kawai ku kyalesa tun da ya taimaka mana ba cutar da mu ya yi ba".
Miƙewar da Ramish ya yi tsaye ne yasa suka yi shiru tare da mayar da kallonsu a kansa dan su ji me zai ce.
Hannaye ya zura cikin aljihun wandon sleeping dress É—in jikinsa, calmly ya furta. "Akwai wanda nake zargi, but kada ku tara mun aiki a brain É—ina, let me finish what I started first, zan kama koma wanene". Ya kai karshen maganar tare da hayewa saman bed É—in.
"Wai me kuke yi a room É—in nan ne? Kowa ya wuce nasa mana, i want to sleep". Cewar Ramish again.
Harara Bilal ya wurga mashi kafin ya gyara kwanciyarsa yana faÉ—in. "Dr idan ka fita ka rufo mana kofa ni kum maga kwanciyata good night". Alamar ba zai bar É—akin ba kenan.
Wani harara na musamman Ramish ya wurga mashi da idanunsa da suka koma sleeping eyes sosai saboda barci da yake ji. Bai ce ko uppan ba ya kwanta tare da janyo bargo.
Cikin zolaya Dr ya ce. "Ko aure kuka yi ai ni ina tsakaninku da matan naku babu mai rabani daku, dan haka bari ma na kashe mana wuta ku gani sai da safe".
Ko sannu Ramish bai ce masu ba ya kara gudun Ac tare da janyo bargon har kansa ya rufe. Dr Raj ya kashe wuta tare da juya masu baya ya cigaba da latsa wayarsa, shi ma Bilal bargon ya ja kawai ya rufe jikinsa. Ba'afi 10 mins Ramish and Bilal suka yi barci, shi kuwa Dr ya jima yana taɓa waya kafin barci ta kwashesa. Asuba ta gari zakunan King Zuhair.
_______________🌹💘______________
AUTA ZUNAIRA.
A hankali ta lallaɓa ta fita ta kofar baya, da yake gidan nasu yanzu a cike yake da manyan baki saboda bikin nan sai ya zamana busy ya kara yi wa iyayen nasu yawa, kowa hankalinsa yana kan ɓangaren da ya riƙe, ita dai Momma an barta da dik wasu bakin da zasu zo alhakin kula da su yana a kanta, so kowa da abin da yake yi, su Auta kuma an barsu a hannun Aunty MieMie.
Kai tsaye part of warriors ta nufa ko tsoro bata ji ba, sai dai tana tafiya tana ɓuya idan ta ga warriors zasu gifta, bata bari kowa ya ganta ba, da yake yanzu ta san room nasa sai kai tsaye ta nufi wajen.
Sai dai bata kai ga ƙarisawa wajen ba ta tsinkayo muryan Ansar a ɗan jefe can wajen wasu wishbone chairs da aka ƙawata kewayayyen wajen da su, ga wasu flowers masu kamshi cike a wajen, sannan akwai dogayen bishiyoyi da suka kewaye wajen, kamar small garden haka, yawancin lokuta Hoorain da Ansar suna yawan zama a wajen.
Lallaɓawa ta yi ta matsa kusa domin ta ji me suke faɗa, dik da bata ji voice ɗinsa a wajen ba hakika tasan yana a wajen, dan ta ji zuciyarta ta amsa sunansa a kisa.
Su uku ne a wajen yau kam, zaune suke saman kujerun suna hira cike da shaƙuwa da juna. Cike da zolaya Anwar ya ce. "Hoorain ina gimbiyarka take?".
ÆŠago kai ya yi cike da mamaki ya ce. "Wacece kuma Gimbiya?".
Wato dai kowa ya gane cewa Hoorain yana son Auta fa, saboda ba so ne na wasa yake yi mata ba, hakan yasa dik abokan da suke tare suka ganosa.
Kallon Ansar Anwar ya yi kafin ya ce. "Ansar ka ji mum mutumin wai ni yake tambaya wace gimbiya kuma?". Yana magana yana murmushi kyakkyawan balarabe da shi.
Kara matsowa kusa ta yi dan ta ji me suke faɗa da kyau sosai. Ganin Hoorain ba kayan mayakan bane a jikinsa ba ƙaramin mamaki ya bata ba, sai dai kuma daga in da yake zaune ya bata baya ta yadda ba zata iya kallon face ɗinsa ba, tunani ta fara yi a kan wato dama yana cire holar yakin nan a cikin mutane? Kenan su Ansar sun san ainahin face ɗinsa? To meyasa ita yake ɓoye mata fuskarsa? Anya ba wani dalili mai karfi kuwa?. Ta jefawa kanta waɗan nan tambayoyin wanda a wajensa ne kawai zata samesu.
Sosai ta ƙagu da son ta ga face ɗinsa, ga shi tana son jin hiran da suke yi, ya zamar mata dole ta laɓe ta gama jin hiran nasu sannan ta shiga wajen taga face ɗinsa, dan tana son ta ji me zasu ce a kanta tun da zancenta suke yi. Zubawa halittar jikinsa ido cikin shigar wandon jeans milk milk color and t-shirt ash ta yi, hakika kayan warriors sun fi yi mashi kyau matuƙa.
__________________________
"Kai Anwar ka dai'na ɓata bakinka a kansa, dan ko me zaka ce mashi sai dai ma ya ce maka bai santa ba". Cewar Ansar.
ÆŠan zaro idanu Anwar ya yi tare da cewa. "Kai Ansar yama isa ya ce bai san gimbiya ba? Mun fa san komai shiru kawai muke yi, kawai malam ka gaya mana ya take?".
Shiru bai tanka masu ba, hannunsa riƙe da wayarsa yana latsawa, hasken kwayayen fitillun dake wajen sun haska face ɗinsa dake sanye da face mask da kyau. Ya fake da iska mai sanyi ya yi yawa ya sanya face mask a face ɗinsa.
Sake maimaita mashi tambayar ina gimbiya Zunairansa take Anwar ya yi cikin zolaya.
A kule ya ce. "Anwar kada ka sake mun maganar wata a nan, na ce maka ni ban san wacece wata Zunaira ba, dan haka kada ku ɓata mata daɗin hiran da muke yi da hiran wata can daban, in hiran ƴan'matanku ma zaku yi ni bari na shige ciki sai da safe kawai". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye.
Wani irin faÉ—uwar gaban da ya ji ne yasa shi fara É—an waige waige kamar mai neman wani abin. Kallo suka bishi da shi Ansar yana faÉ—in. "Kai our Lion matsalata da kai saurin hasala da fusata, wai a haka kuma zaka yi aure? An gaya maka mata zasu iya É—aukar wannan uban saurin fushin naka ne? Daga maga sai ka wani fusata kace zaka tafi ciki?".
Ko kallon in da suke bai yi ba, bai ma ji me suke faÉ—e ba, saboda hankalinsa ya yi wani wajen, zuciyarsa ta buga ta amsa da sunanta, tabbas ya ji a zuciyarsa tana kusa da su, shiyasa ya fara waige waige, lallai ya tabbata ba son wasa yake yi mata ba tun da har in ta matso kusa da shi sai ya ji hakan a cikin zuciyarsa koda bai ganta ba, sonsa na daban ne wlh.
Ita kuwa idan ranta ya kai miliyan to ya ɓaci, bata ji daɗin yadda ya furta da bakinsa cewa bai santa ba, har da wani bai san wata Zunaira ba, wato itace ma wata, abin ya bakanta mata rai da har wayarta dake hannunta ya zame ya faɗi kasa ba tare da ta farga ba, abin da taɓa zuciya ace wanda kake mutuwar so ne zai tsaya a gaban abokansa yana cewa bai ma sanka ba, abin da ciwo gaskiya, zuciya bata da kashi!!.
Ganin yana nufo ta in da take yana waige waige kamar mai neman wani abi ne yasa ta bar wajen da sauri domin ta koma cikin gida, ta fasa haɗuwa da shi ɗin ma dan ya bakanta mata. Wucewa ta yi ta bar wayarta a ƙasa a wajen ba tare da ta sani ba.
Tana barin wajen ba jimawa ya iso daidai in da ta bar wayar tata, dik ta in da take da ya matso zuciyarsa take kara amsa mashi da tana wajen, shiyasa ya nufo wajen kai tsaye, ya yi mamakin meya fito da ita a daren nan?.
Yana ƙoƙarin bin hanyar da ta bi ne ya hango waya a ƙasa, da farko bai san wayarta bane har sai da ya ɗauko tukun nan ya gane nata ne, dan ya saba gani a hannunta. Wannan waya ta kara sawa ya tabbatar da zarginsa a kan tana kusa da shi, sai dai kuma ya ji zuciyarsa ta sosu sosai, dan yana da yakinin ta ji maganganunsu ne yasa ta gudu, dik sai ya ji babu daɗi, a ransa ya ce lallai yakamata su haɗu tun kafin ta koma cikin gida domin ya bata hakuri, yasan halinta sama da kowa, yasan zata iya kwana yin kuka a kan hakan, idan hakan ya faru kuma ba zai taɓa samun nutsuwa ba shi.
Cikin zafi ya fara takun jarumta yabi bayanta dan ya cin mata. Dik ƙaguwa da son ganin face ɗinsa da take yi a yau ta samu dama amma ya ɓata mata rai yasa ta ji bata da buƙatar hakan.