← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 211

Sashe 25

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka ta je ta yi ita ma, ta zo ta yi zaman ƴan bori a tsakiyar katifa ta hau yin wannan mahaukaciyar kwalliyar tata, shiyasa fa kwata kwata powder baya jima masu idan bappa ya sayo masu, saboda Mahreen ke karar da shi a face ɗinta, damɓarashi take yi kamar an aikota, ga power irin jajayen powder nan ne, wlh sai fuskarta ya tashi daga farar fata izuwa jan ƙoshe, abin dai sai wanda ya gani, kuma a haka take hauka da faɗa idan aka yi wa kwalliyar tata dariya, wannan yarinya ni dai in ce sai shirin Allah.

Yau dai sai sauri take yi tana son ta gama da wuri ta je ta cigaba da taɓa kumatun aljanin nan da bappa ya kawo, tana son ta je ta yi ta mulmula mashi ne kafin Mahnoor ta gama kwashe tuwo su tafi.

Kaya irin na jikin Mahnoor É—in ta sanya a jikinta, da alama bappansu É—inki iri É—aya yake yi masu, duk abin da Mahnoor take da shi ita ma Mahreen tana da shi.

A hankali ta gama ta miƙe tare da tattare komai ta mayar mazauninsa, ba karya suna da tsabta kam, basu son datti, komai nasu tsab tsab. A ɗari ta fito ta afka cikin ɗakin bappa dan ta fara aikin mulmula mashi kumatu..... Ni kam na ce su Mahreen an samu sabon business, Allah ya fitar da kai Our Jaish.

A gabansa ta zauna, ta kura mashi idanu kamar mai nazarin wani abin, yadda kuka san itace likita an kawo mata mai jinya tana nazarin yanayin jikin nasa, haka ta nutsu tana kare mashi kallo, ita dai a duniya Jaish ya yi mata, bata ki a barta ta mayar da shi Tv ta yi ta kallo ba.

Ta É—auki tsawo lokaci a haka tana ta kallonsa, jin sautin muryar Mahnoor na kiranta tazo su tafi ne yasa ta yi saurin kai hannunta saman jajir É—in lallausan kumatun nasa ta fara shafasa a hankali kafin daga baya ta fara mulmula mashi kamar wadda take mulmula gullinsuwa.

"Wai Mahreen ba zaki fito mu tafiya ba?". Mahnoor ta faÉ—a daga waje, tsoro ya hanata shigowa ta janyo Mahreen É—in.

"Ni fa Adda Mahnoor ban fa gaji da taɓa kumatunsa ba, kizo kema ki taɓa jiki akwai daɗi".

"Allah ki fito daga cikin É—akin nan tun kafin in shigo".

Da yake kwararriya ce a iyashege sai ta ce. "Idan kina son na fito muje gidan ArÉ—o to fa sai kin shigo kin kama hannuna, idan ba haka ba ni babu in da zan je".

"Ayya gajin Bappanmu kin ga ina jin tsoron aljaninnan, dan Allah ki fito, wlh ba zan iya shigowa ba, ki zo kinji ko? Idan muka je kiwo gobe zan ciro maki kanya".

Kin fitowa ta yi, ta kafe sai Mahnoor É—in ta shigo in dai tana son su je. Tana surutu tana É—an murguÉ—a baki, gashin idanunta kam ba'a magana, suna tsaitsaye zara zara dasu na rashin kunya.

Cigaba da yi mata magiya daga waje ta yi, amma ta ki fir, sai cigaba da mulmulawa bawan Allah kumatun nasa take yi. Ai kuwa kamar daga sama ba zato ba tsammani kwatsam ya wani irin zaro idanu waje, ga idanun nasa sun yi jajir tamkar wadda aka watsawa barkono a cikinsu.

Subhanallah wani irin ihu da Mahreen ta zunduma mai sautin toshe jin mutun, ta yi wani mahaukacin razana, dan bata yi excepting zai buɗe idanunsa ba, sam bata kawo hakan a ranta ba. A dubu ɗari ta miƙe ta fasa waje tana ihu.

Ai kuwa tun da ta zunduma ihu farko Mahnoor ta arta waje a guje, dan a tunaninta aljanin ne ya tashi ya kama Mahreen É—in yasa take ihu, a maimakon ta shiga ciki ta kai kama agaji idan ma hakan ne, ina ai sai ta yi ta kanta a É—ari, dama kamar a kan kaya take, tana jin tak ta arta waje a dubu abinta.

Haba wa hajiya Mahreen ana firowa sai kofar gida, ihu take har da cire takalma da É—an'kwalin kamar su ne suka sanya Jaish ya buÉ—e idanu, yau har da karanta suratul fatiha a cikin ihun nata. Bata zame ko'ina ba sai gidan kakansu ArÉ—o, duk ta zubar da takalma and É—an'kwali a hanya.

Can ta isko Mahnoor har ta isa gidan sarkin tsoro, tuni har ma ta shige cikin ɗakin kakarta mace tana kuka da hawayenta duk da ita bata ga abin da Mahreen ta gani ba, ihu kawai ta ji amma har da kukanta. Kakar su dake cikin madafa bata san da zuwan Mahnoor ba dan ita bata yi ihu ba sai hawaye gudowa kawai ta yi, sai da Mahreen ta shigo a haukace tana ihu ne duk wata halitta mai rai dage gidan har da magensu sai da suka fito, manyan mata an shigo waje ai dole a fito a tarbeta, Mahreen manyan ƙasa.

Mata uku ne a cikin gidan, so bukkoki huÉ—u ne da na Malam ArÉ—o biyar kenan a cikin gidan. Harta ArÉ—o sai da ya fito a hanzarce jin irin ihun da ta afko masu cikin gida da shi.

Da sauri kakarta ta yi ƙoƙarin kamata tana kiran sunanta, ina kin basu haɗin kai wajen riƙota da suke yi ta yi, faɗi take. "Hande mi woni, ina Nennenmu? Ashe da gaske ne aljani Bappa ya kawo gida, wlh aljani ne idonsa ba irin na mutane bane, kamar wuta idanunsa suke, na shiga uku, ga idanunsa wlh sun kai ukun na Adda Mahnoor a girma, kato kato da su, yau kam mutuwa zan yi na kalli idanun aljani".

Sai ƙoƙarin nutsar da ita suke, amma ina yadda kuka san iska haka take yawo a sama dan sun rirriketa, sai ta ɗage kafa sama tana wuwwuntsiyasu tana ihun ina Nenne.

Nennen nasu dake tsaka da barci ne ta tsinkayo muryar Æ´ar tata a cikin kunnenta, a hanzarce ta zabura ta taso ta fito, kusan a tare suka fito da ainahin Kakansu Mahreen É—in.

Matan Arɗo uku ne, so biyun da suka tari Mahreen ɗin suna ƙoƙarin rarrashinta kishiyoyin kakar tasu ce, ita kuma ainahin wadda ta haifi Nennen tana banɗaki lokacin da Mahreen ɗin ta afko masu, so yanzu fitowarta kuma a tare da Nennen kenan.

Kanta suka yi a tare da gudu kakar tata ta ainahi tana faÉ—in. "Cikinku wace shegiya ce ta dakar mun jika?".

Sake Mahreen ɗin suka yi, ai kuwa a guje ta yi wajen Nenne tana ihu. Arɗo na ƙoƙarin yin magana ɗayar matar wadda ake kira da Diddi ce ta rigasa da cewa. "Ai babu shegiya a cikin gidan nan ko kin manta ne? Ko wacce da ubanta".

"To rasa kunya ɓerar tanka, wacece ta dakar mun jika na ce?". Cewar kakan Mahreen da suke kira da gwaggo.

Sa kai É—ayar matar da suke kira da Inna ta yi ta wuce izuwa nata É—akin abinta, bata tofa ko uppan ba, da alama bata son hayaniya.

Su kuwa suka tsaya kace nace, gwaggo ta zage sai ta ji uban waye ya dakar mata jika.

Inna na shiga ɗakinta ta ci karo da Mahnoor a zaune tana ta kuka, dan ba karya ta tsorata. A hanzarce ta ƙariso wajenta. "Mahnoor lafiya me ya faru?".

Tana ganinta ta yi maza ta miƙe ta faɗa jikinta tare da kara sautin kukanta. "Mahnoor ki gaya mun me ya faru mana? Meyasameki?".

Ƙasa yin magana ta yi tana cigaba da yin kukanta. Nasan zaku yi mamakin ganin Mahreen ta nufi wajen gwaggo ita kuma Mahnoor ta nufi ɗakin Inna ko? To barin baku kaɗan daga labarinsu dan ku fahimci ina muka dosa. Mahnoor Inna ce kakarta a gidan, ita ta haifi mahaifiyarta, ita kuma Mahreen gwaggo ce kakarta ita ta haifi Nennenta.

Mahaifiyar Mahnoor bata gidan Bappa kwairaga, Inna ƴaƴanta biyu rak a duniya, daga mahaifiyar Mahnoor mai suna Halima, sai kuma kaninta Ibrahim. Bappa kwairaga mahaifiyar Mahnoor ya fara aura, ita ce matarsa ta farko, Nenne kawarta ce da aka maye mashi gurbin mahaifiyar Mahnoor da ita bayan ya rasata, ƴaƴan kishiyoyi suke da Mahaifiyar Mahnoor da Nenne, kuma kunga gidan Arɗon ba zaman lafiya suke yi ba, akwai kishi a tsakaninsu, lokacin da Bappa ya rasa mahaifiyar Mahnoor Mahnoor ɗin tana yarinya bata wuci 2 years ba, shiyasa Arɗo ya bashi auren Nenne dan ta riƙe Mahnoor ɗin tunda ƴar ƴar uwarta ce, suna ganin zata kula da ita sosai.

Hakan kuma aka yi, da farko Nenne ta riƙe ta sosai da sosai, tamkar ƴar cikinta, har ta haifi Mahreen, ta haɗasu ta riƙe da amana, sai dai kash mahaifiyarta ta canza mata tunani daga baya, a in da suka fara sakawa ɗinbin uban tulin dabbobin bappa ido, daga nan ta fara sanyata ta fara juya riƙon amanar da take yi wa Mahnoor izuwa nanzalinci, duk lokacin da Inna ta yi wa gwaggo ba daidai ba, sai gwaggo ta ce da Nenne ta azabtar da Mahnoor, ta hakan suke cusawa Inna bakinciki, dan Mahnoor ita ce kaɗai jikarta, ita take kallah ta tuna ƴarta, bappa kwairaga kuma yaki bata Mahnoor ɗin ta riƙe, wai shi ma yana tuna mahaifiyarta a duk lokacin da ya ɗaga idanu ya kalleta, so ba zai iya rabuwa da it ba.

Sannan su gwaggo suna bakincikin irin kauna da bappa yake nunawa Mahnoor ɗin dan maraicin rashin uwa, sai ya zamana yana kula da ita sosai fiye da kansa, kuma yana ƙoƙari dannewa fa baya nuna banbanci a tsakaninsu da Mahreen, amma saboda shegen makirci irin na gwaggo ta zuga Nenne wai Bappa ya fi kaunar Mahnoor a kan Mahreen, hakan yasa ta kara tsananta wahalar da Mahnoor ɗin.

Duk kuma wannan abin da yake faruwa Bappa ko Arɗo ba wanda ya sani a cikinsu, bappa bai san ana wahalar mashi da ɗiya ba, kuma bata taɓa gaya mashi ba baiwar Allah, idan ya yi tafiya har talla Nenne take ɗaura mata, amma da ya dawo zata dai'na ta nuna tana kaunarta ma a gaban idanunsa.
Chapter 25 · 0% Book details