← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 211

Sashe 2

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa Hajiyarsu baban Zainab É—in da take ta faman kuka tun da ta zo, Æ´an'sanda sun ce ta koma gida, kin yarda ta koma ta yi, faÉ—i take sai maman Zainab ta biyata ran É—anta, azzaluma ta kashe masu bangonsu, da shi kaÉ—ai suka dogara, shi ne mai yi masu komai, dan haka wlh sai ta biyata É—anta, maman Zainab dake sume bata san wainar da ake toyawa bama baiwar Allah, sai banka mata ashariya kala kala suke yi tana sume. Maman Haidar kam ma har da wani cewa wlh ba zasu yarda ba dole ita ma a kasheta kamar yadda ta kashe shi azzaluma kawai.

Da kyar dai aka samu ƴar'sanda mace ta ja Hajiyar suka tafi zata mayar da ita gida, haka su Maman Haidar suka bisu, Maman Hanif kam ta ƙasa iya furta ko kala bayan ruwan hawaye da take yi, banda ruwan hawaye babu abin da take yi, ita dai tasan maman Zainab ba zata taɓa kashe baban Zainab haka kawai da gangan ba, dan ita ta san soyayyar da yake a tsakaninsu, ta san irin yadda baban Zainab ya rinƙa jigila a tsakanin Kano da Kaduna saboda ita, sannan ta san yadda maman Zainab ɗin ma take son shi, so ita bata ma yarda cewa maman Zainab ɗin ce ta kashe shi ba, zargin Hauwa ce ta yi hakan take yi a ranta, dan ita fa kwata kwata bata kaunar Hauwa, amma Hajiyarsu da Maman Haidar fa suna kaunar Hauwar duk da balai'n da take surfa masu, da alama ta kai sunansu wajen bokanta ne, sai dai aikin bai kama maman Hanif ba, dan dai ita kam babu son Hauwar ko ɗigo a ranta, sai ma zallar tsana da take yi mata.

Ko da aka mayar da su gidan baban Zainab É—in, a bakin kofar gidan suka isko Zainab a zaune tana tikar kuka kamar ranta zai fita, ta rasa ina zata sanya rayuwarta, babu uba yau, sannan Æ´an'sanda sun tafi da mamansu, ga kuma Khadija shiru bata dawo ba.

Ƴar'sanda da ta rakosu ta dawo da su gidan tana juyawa suka fara halin nasu, tana barin gidan maman Haidar ta fara surfe da nikar bala'in a kan wlh ba zasu taɓa hakura su yafewa maman Zainab ba, dole a kasheta kamar yadda ta kashe masu bangonsu ma jingina.

(Ni kam na ce sai yanzu kenan suka san cewa shi ɗin bango ne a gare su?🤔)

Kasancewar har da Hauwa Æ´an'sanda suka saki da nufin idan wani abin ya taso zasu nemeta, hakan yasa ita ma ta fara rera nata kukan munafurcin tana faÉ—in wlh haka ne ba zasu yafe jinin baban Zainab ba.

Dama fa ita Hauwa idan baku manta ba dukiyar baban Zainab ɗin kawai take so ba shi ba, so ita mutuwar tasa ma rage mata hanya ya yi, ya zame mata tsanin da zata taƙa ta cinma burinta ne, dama ko maman Zainab bata kashe shi ba ita Hauwar ta shirya yadda zata sanya a ɓatar mata da shi bayan ta gama kwasan abin da zata kwasa, so ita wannan kasheshi da maman Zee ta yi hanya ta rage mata, wani dama ne ta samu, yanzu tunanin da yake a cikin ranta kawai shi ne ta yadda zata yi ta rufe bakin kowa ta kwashe komai na marayun Allahn nan Khadija da Zainab ta gudu abinta, shiyasa ma kuka ga ta yi saurin zuwa ta kira ƴan'sanda domin su tafi da maman Zainab, tasan idan maman Zainab ɗin tana cikin cell abubuwa zasu tafi mata yadda take so saɓanin idan tana gidan, bokanta ya gaya mata asirinta ba zai ci maman Zainab ɗin ba, ba zata iya rufe mata baki ba, domin a yanzu maman Zainab ta tsaya tsayin daka a kan ibada, ta koma ga Allah sosai, hakan yasa babu wani aiki da zai iya kamata.

Sanin hakan yasa Hauwar ta yi azaman jefata a cell, dan in tana gidan zata katse mata duk wani abin da ta shirya, kuma bata isa ta É—auki ko tsinke a gidan ba, amma yanzu kunga maman Zainab tana cell, iyayen baban zee É—in kuma ta sanya an yi masu aikin cusa masu kaunarta, saura mata aiki É—aya shi ne ta rufe bakunansu ta yadda zata gudanar da komai babu wanda zai iya ce da ita uppan........ E lallai akwai kura, ina Khadija? Sai Allah kaÉ—ai yasan su waye suka É—auketa, ina kuma zasu kaita baiwar Allah.

Wani irin tsananin tsana Hajiyarsu baban Zee ta ji take yi wa maman Zee da Æ´aÆ´anta gabaÉ—aya...... Ni kuwa nace to me laifin Æ´aÆ´an nata? Su suka yi laifin ne? Ko a wajen Allah laifin wani baya shafar wani, amma jahilci yasa Hajiyarsu ta haÉ—e da su dukka ta tsana kamar ta kashesu, sai faÉ—i take maman Zainab ta gama da su ta tona masu asirin da Allah ya rufa masu, shikenan sun shiga uku sun lalace.

Maman Hanif kam har izuwa yanzu ta kasa iya furta ko uppan. Banda zagi babu abin da maman Haidar take surfawa Zainab dake zaune a bakin kofa tana tikar kuka, yarinyar nan kamar ranta zai fita, kuka take yi ba ji ba gani, idanunta har ƙanƙancewa suka yi, sun kumbura sun yi jajir, idan ka ganta sai ta baka tausayi, sai kuma ka tsorata da ganin idanun nata, saboda yadda suke jazur da su.

Ko sannu bata ce da su ba, duk zagin da maman Haidar take yi mata bata ko É—ago idanu ta kallesu ba, hasalima hankalinta baya a tattare da ita ne, bata jin me ma suke faÉ—e.

Maman Haidar na zagi Hauwa na ƙara ingizata, har da kara cewa ai dama maman Zainab ta kai sati tana cewa sai ta kashe baban Zainab, dan haka wlh har su Zainab ɗin ma kada su bari, ai suma mugun iri ne, dan halin uwarsu suka ɗauko.

Ita fa Hauwa fama take yi taga yadda zata yi ta kawar da su Zainab ɗin, sannan ta rufewa kowa baki ta kwashi dukiya ta yi pacakanta da su son ranta, ta haɗa kayanta ta koma Kaduna....... Gaskiya ba karamar mayyar son abin duniya bace Hauwar nan, ba kuma ƙaramar azzaluma bace ba.

Da dai suka ishe Zainab da zagi kamar zasu cinyeta ɗanya, sai ta miƙe ta nufi cikin ɗakinsu, ji take kamar zuciyarta na ƙonewa da wuta, su barta ta ji da abin da take ji mana, amma suna kara mata wani.

Ko da ta shiga ɗakinma ba su barta ba, maman Haidar ta ce ta fito daga ɗakin nan munafuka, yadda kuka san ba jininsu ba ce, kamar ba jinin baban Zainab ɗin ne yake gudu a jinin Zainab ɗin ba, suka murje idanu, suka sanya yarinya a gaba da zagi da baƙaƙen maganganu kamar ita ta aikata laifin ba mamanta ba.

Da maman Hanif ta yi ƙoƙarin basu hakuri su rabu da ita, ai kuwa ita ma maman Haidar ta hau zaginta babu kakkautawa, wai bata kishin jinin ɗan uwanta, kamar ba yau bawan Allahn nan ya rasu ba, sun zauna sai kace nace suke yi, tun ruhinsa bai gama sauka a masaukinsa ba sun fara walaƙanta bayansa, sun fara cin zarafin ƴaƴansa kamar ba nasu ba.

A takaice dai Zainab da ta ga ba raga mata zasu yi ba, sun isheta da magana, sai ta kama hanyarta ta nufi barin gidan. Maman Haidar ce ta ce ina zata je munafukar banza.

Ko sannu bata ce masu ba, bata ma sake É—aga idanu ta kallesu ba, abin da take ji a cikin zuciyarta ma ya isheta, haka ta yi banza da su ta nufi waje, sai magana suke ta yi mata, ina ko waigowa bata yi ba, sai kiranta suke yi.

Tana fita ta fara neman ina Khadija take, tana tafiya tana hawaye bibbiyu, wani na bin wani gwanin ban tausayi.

Ni kai'na na tausayawa maman Zainab da ƴaƴanta wlh, kowa da kalar tasa ƙaddara a rayuwa, ba ta yadda Allah baya jarabtar bawa, amma kuma my people's ina son ku san wani abu, duk wanda kuka ga yana shiga cikin kaddarori to wlh Allah ya fi sonsa, Allah yana jarabta imanin bawa ne kawai idan yana kaunarsa, kada ki ga kina shiga cikin wasu matsaloli ki yi tunanin ko Allah baya tare da ke har ki fara tunanin kauce hanya, wlh wlh wlh Allah yana jarabtar wanda yake so ne kawai, to fata na dai a nan shi ne Ubangiji Allah ya bamu ikon cin rabawarmu a rayuwa koma wace iriya ce, sannan ƙarin wata haske shi ne duk abin da kike so kike kauna a rayuwar nan ki saki a nan kaddararki da jarabawarki take, hadisi ne in gantaciya, domin na baku misali a aikace yasa na zaje na yi rubutu a kan part ɗin su maman Zainab, duk abin da ya faru da maman Zainab mu kaddarine da ga Allah, kuma ku sani kaddara da jarabawar ta faru da ita ne a kan abin da ta fi so ta fi kauna wato baban Zainab, a dalilinsa komai ya faru, saboda son da take yi mashi yasa har ta kauce hanya, dalilin son da take yi mashi yasa abubuwan duk suka faru da ita, da bata son shi da hakan ba zai faru ba, so misali na baku a aikace ba a labarce ko a kwatance ba. Ƴar uwa ki kasance mai yawan rokon Allah a kan abin da kika fi kauna, hakan zai sa idan kaddara da jarabawa zasu afka maki bisa wannan abin ya zo maki da sauki, saboda yawan addu'a, fatan kun gane? To rayuwar maman Zainab tarin karatu na tara maku a wajen dan ku ilmantu, Allah ya bamu dacewa ya kuma yafe mana kura kuranmu.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

KINGDOM OF POWER💪🔥💘

A karo na almost 8 Yah Jawad ya sake gwada kiran number Jaish, sai ya ji number a kashe. Guntun tsaki ya ja kafin ya ce. "Aikin me ka yi jiya da har yanzu baka tashi daga barci ba? Wato na dameka da kira shi ne har da kashe wayar ko? Zamu haÉ—u ne".

Ya kai karshen zancen zucin nasa tare da kai kallonsa kan Chuchu dake goge É—an bakinta da tissue. "Kin gama mu je ko?". GyaÉ—a mashi kai ta yi alamar e.
Chapter 2 · 0% Book details