Sashe 155
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan ka faɗo a wannan waje kuwa idan baka mutuba to ba zaka sake moruwa ba, shirmen banza da wofi, haka ya rinƙa faɗa a ransa. Bai san cewa su wannan al'adar ta iyaye da kakannin ganinsa suke yi kamar bauta ba, bama su taɓa yarda ayi biki ba'ayi shi ba, ai wannan aure bai cika ba.
Ko kallon in da su bappan suke bai yi ba a lokacin da ya sauko, su kuwa sun kasa yarda da cewa shi ne, saboda gani suke yi lokacin da kowa yake saukowa idan ya hau bai yi ba, ya aka yi shi ya yi sauri, sun É—an tsorata sun kuma yi mamakin ganinsa.
Baiwar Allah Mahreen ta kasa yin barci, tunaninsu kawai take yi ta kwanta a jikin bappa shiru. Tana ganinsu da gudu ta bar jikinsa ta nufesu. Yana ƙoƙarin riƙota saboda ruwan sama, amma ina tuni ta nufesu while shi kuma Jaish ɗin bai dakata a wajen ba, hanyar gida kawai ya nufa, dan wani irin haushinsu na musamman ma yake ji na wannan abin. (Ni kuwa nace anya Jaish ba haushi yake ji dan ruwa ya jiƙa mashi mata ba kuwa? Ɗan ƙaniya meyasa tun farko bai ji haushin al'adun ba sai da ruwa ya sauƙo? Ni fa ban yarda da kai ba Jaish, ato!)
Da gudu ta bi bayansu tana yi masu sannu da saukowa. Bisa al'ada fa idan ya sauko daga saman dutsen a wajen zasu zauna a cigaba da gudanar da bikin, amma shi ya wani wuce da ita, a nan ma sai da ya sake yi masu tsarinsa.
Ganin sun wuce gida ne yasa bappa ya fita a cikin ruwan shi ma ya bi bayansu, dan hankalinsa a tashe na ganin halin da suke ciki, ruwa ya yi masu duka.
Kusan a tare suka shiga gida, a tsakiyar gidan ya sauƙeta yana sauke numfashi a hankali hankali, fuskar nan a ɗaure tamau. Da gudu Mahreen ta zo ta faɗa jikinsa tana yi mashi sannu da dawowa.
Ƙasa ƙasa kamar mai ciwon baki ta furta. "Meyasa kika fito a cikin ruwan nan?".
A fujaje ta É—ago kanta daga saman jikin nasa ta kalli face É—insa. "Hamma yaushe ka iya yin magana?". A ruÉ—e ta yi tambayar.
Dai'dai lokacin bappa ya ƙariso wajen, shi ma ya ji maganar, da yake yana sa ran hakan sai ya fara zabga godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya nuna mashi wannan rana da ya ji sautin muryar bakon nasa a kunnensa. A ransa yake faɗin lokacin ya yi da zasu san wanenen bakon nasu, Allah sarki basu san bai gama samun sauki ba, dan baya a hayyacinsa har yanzu.
Ganin ta dunkule jikinta waje guda tana aikin rawan sanyi ne yasa Jaish ya nuna mata hanyar É—akinsu da hannu a in da ya ce ta tafi É—aki.
Bappa ne ya tari numfashinsa da cewa. "Ga naku É—akin ai ta je can kayanta suna ciki sai ta canza, kai ma yakamata ka je ka canza kaya kada mura ta kamaku, kaga sanyin asba tana gabatowa".
Tun da bappan ya fara magana ya tsare shi da ido bai ce komai ba, sai dai ba ido cikin ido yake kallonsa ba, ji yake kamar ma ya dallah wa bappan mari, dan dik waye ya ja masu wannan wahalar idan ba shi ba, da wani zancensa na banza wai tun iyaye da kakanni al'adar take, kayan takaicin..... Jaish fa ya fara samun sauki, hali ta fara dawowa, akwai aiki kenan.
Ganin bai motsa ba sai kallon in da yake yake yi ne yasa bappan ya gane haushin bikin nasu yake ji, dan ya iya karantar yanayinsa a yanzu, kuma dai kun san dole su iya karantarsa tsab, saboda iya maganar kurame da mutun ba ƙaramin abu bane, dole su iya gane ma'anar shirun da kowace motsinsa.
Hakan yasa bappan ya fara rarrashinsa a kan ya yi hakuri komai ya wuce, kuma ya yi mashi alkawarin ba za'a ƙarisa sauran waɗan nan al'adu ba, ya yi babban ai.
Wani irin kallon da ya wurga mashi mai cike da takaici ne yasa bappan juyawa ya nufi nasa room É—in, dan yasan halin mutumin nasa, wannan kallo ba komai bace face na bakinciki, so gara ma ya kama kansa, dan yasan Jaish baya jin rarrashi, tun baya magana abin da ya yi niya kawai yake yi, bare yanzu ya fara yin magana, ai sai a slow.
Wucewa da sauri Mahnoor ta yi ta shige cikin É—akin da bappan ya ce ta shiga, dan wani irin bala'in sanyi take ji na daban.
Ɗan rage tsawonsa ya yi tare da raba jikinsa da Mahreen da ta ƙanƙame shi. "Jeki ki canza kaya kada sanyi ya kamaki ko?". Yana magana yana kara rage tsawonsa har yazamana ya sunkuyo sosai suna fuskantar juna.
"Hamma yanzu ka iya yin magana?". Kamar zata yi kuka ta yi maganar, tana jin wani irin tsantsar farincikin na musamman.
Kai ya gyaÉ—a mata kafin ya ce. "E ina magana, yanzu jeki ki canza kaya ki É—an kwanta kaÉ—an zuwa asuba". Ya yi maganar suna kallon juna har cikin ido.
"Hamma muryarka tana da daÉ—i sosai, idan kana magana kamar ba mutun ne yake yi ba".
"Da gaske?". Ya yi tambayar ba tare da yasan ya É—aga mata gera É—aya ba, da yake hakan kusan É—abiarsa ce a da, sai ya yi ta bai san ya yi ba. A hankali dai wasu É—abi'un nasa suna dawowa jikinsa.
Mamaki ne ya kamata na ganin ya ɗaga gera guda, miƙewa tsaye ya yi tare da karɓar torch light dake hannunta, ya riƙe hannunta har izuwa cikin ɗakin nasu, a lokacin Mahnoor ta canza kaya, sai kuma ta zauna a ƙasa bata hau saman mattress ɗin nasu ba, ta takure jikinta waje guda, hakan zai tabbatar maka da sanyi take ji sosai.
Mamaki ne ya kamashi lokacin da ya shigo cikin É—akin, kayansa gabaÉ—aya bappa ya dawo mashi da su nan, ita ma gabaÉ—aya kayanta ya dawo da su, lallai ma bappa akwai kokari sosai.
Wucewa da ita ya yi, cikin sanyin murya ya ce da Mahnoor ina kayan Mahreen suke?.
"Kayan ta baya nan, ina ga yana É—akinmu ko É—akin bappa". Da kyar ta iya bashi amsar, saboda yadda jikinta ke kerma haka hakwaranta suke garuwa da na juna.
"Jeki ki É—auko kayan naki kizo ki canza kin ji?". Ya faÉ—a yana sakin hannun nata.
Da gudu ta juya ta fita. Shi kuma ya nufi wajen kayansa. Kayan da yake da buƙata ya ɗauka ya fice daga ɗakin.
After 30 mins ya dawo bakinsa a ɗauke da sallama. Shiru bata amsa mashi ba, ciki ya shigo. Saman mattress ɗin ya nufa, dan ya ɗan kwanta ko da na 20 mins ne sai ya tashi ya yi raƙatainil fajir sannan su tafi masallaci.
Har ya karkata zai kwanta sai kuma idanunsa suka sauƙa a kanta, Allah sarki ta yi barci a yadda take zaune, ga wani irin rawar sanyi da take yi.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya kariso in da take ɗin, ɗan rage tsawonsa ya yi ya ɗauketa cak, barcin nata mai nauyi ne sosai, saboda gajiya ga dukan ruwan saman da ta sha, hakan yasa bata farka ba da ya ɗauketa.
A saman mattress É—in ya kwantar da ita, sannan ya janyo bargon da Inna Rabi ta shinfiÉ—a masu a karshen mattress É—in irin kwalliyar nan, ya janyo ya rufeta har zuwa saman kirjinta, ya juya mata baya ya kwanta, shiru ya É—an yi kaman mai wani tunani.
Sai kuma ya juyo da jikinsa ta in da take, ya zamana suna fuskantar juna, zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda take sauke numfashin barci a hankali hankali irin na gajiya.
Ji ya yi tsikar jikinsa tana tashi tamkar wanda rayuwarsa ta baya take ƙoƙarin dawo mashi, ɗan kawar da kallonsa daga face ɗin nata ya yi izuwa gangan jikinta. Kamar wanda aka tsikara ya wani miƙe zaune tare da kawar da kallonsa daga kanta.
A hankali ya sauko da kafafunsa ƙasa, sannan ya miƙe ya nufi waje. Ita kuwa sai ta ƙara kudundunewa a cikin bargon da bata san da shi ba, baiwar Allah ta ji ɗumi mai ni'ima yana ratsa har cikin ƙashin jikinta ne, hakan yasa ta kara shigewa bargo sosai.
Yana fita bappa na fitowa, sam yaki kallon in da yake, sai yanzu yake kara jin wani sabon kunyan bappan tana ratsa shi, alwalarsa kawai ya ɗauro ya wuce ya dawo cikin ɗakin, bappan ma alwalarsa ya yi ya koma ciki, Mahreen tana kwnace a saman gadonsa, shi ya hanata komawa wajen su Jaish ɗin, da ta canza kaya sai ya ce ta hau gadonsa ta kwanta, kuma daga yau kada ta rinƙa shiga masu ɗaki idan har basu suka kirata ko suka aiketa ciki ba.
Ai kuwa nan ta yi tsalle ta dire ta ce bata yarda ba, ya za'ayi É—akin addarta da Hammanta kuma ace ba zata shiga ba? Ai ita ma É—akin zata koma kwana.
Da kyar ya samu ya yi mata dabara ya shawo kanta ta yarda da hakan, shi ne ta kwanta ta yi barci.
Akwai komai da zasu buƙata a cikin ɗakin, harta dadduma an kai masu, yana shinfiɗe a ta gabas.
Raƙatainil fajir suka gabatar kusan a tare shi da bappan da yake ɗakinsa, sannan suka fito suka nufi masallaci, a tare suka tafi, Jaish kansa a ƙasa, kamar ma ba zai jera da bappan ba, amma ba yadda zai yi, bappan ya rigada ya fito, ga shi an fara tada sallah ba halin ya ce bappa ya je yana zuwa dan ya je shi kaɗai daga baya, hakan zai sa sallah ta wucesa, dole kawai su jera kaman wani yaya da ƙani, sai dai Jaish ya fisa tsawo gaskiya, amma shi ma dogon mutun ne.
Bayan sun idar da sallah, suka yi askar kafin su dawo gida, sai dai bappa ya rigasa dawowa, da gangan ya ki tashi su dawo a tare, dan baya son su jera, kunya sosai yake ji, sai ya ƙaƙalo askar ɗin karya har bappa ya wuce gida.