← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 211

Sashe 75

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowani jami'i aikin dake gabansa kawai yake yi, sai ku rantse da Allah basu san juna ba, babu irin hiran nan na sanayya bare raha, tamkar ma basu san da junansu a wajen ba, kowa ka gani fuska a turɓune tamkar waɗan da aka cewa wutar jahannama zasu shiga, kunga kuwa ai karshen ɗaure fuska kenan zasu yi.

Ya ɗauki almost 1h a cikin na'urorin nan, yana tsaye a kan kafafunsa ko ɗar na gajiya baiyi ba, tamkar wani saƙagon da aka sassaƙa. Yawan ringing da wayarsa ta yi ta yi ne yasa ya ciccire duk wasu na'ura dake jikinsa ya fita daga wajen, sai kaga tamkar ma'aikatan nasa basu ganin komai face aikin dake gabansu, amma da zarar ya dososu zai wuce sai kuga sun ɗaga hannu sun sara mashi kamar wasu masu idanu a bayan wuya.

Wani hanya mai É—an tsawo ya bi, duk a cikin wajen ne, wani katafaren luxurious parlour ya shiga, yadda kuka san ba'a underground suke ba, ga wani irin daddaÉ—ar kamshin da sanyi dake tashi a wajen, ba abin da ya fi bani mamaki ma irin furnitures dake cikin parlourn, sun haÉ—u kam, luntsuma luntsuma da su.

Jami'ai biyu ne ke gadin room door ɗin, yana dososu suka kame waje guda tare da sara mashi, bai tankasu ba, tamkar ma bai gansu ba ya sa kai zai shiga ciki. A hanzarce ɗaya daga cikinsu ya tsugunna ya riƙe ƙasan takalmarsa hakan yasa takalmar suka fita daga kafafunsa, ɗaukarsu ya yi ya sanyasu a cikin shoe dryer dake ta bakin door ɗin ta ciki.

ÆŠayan jami'in kuma ya yi saurin sanya hannu ya zame mashi rigar dake jikinsa da jami'an farko suka sanya mashi a yayin shigowarsa wajen, yana cire mashi ya fice da rigar daga wajen...... Kai kaga wani isa da iko!! Takalma da rigar ma sai an cire mashi?!! Wannan guy daga gani akwai girman kai!!.

Shi kuwa Smart É—in toilet É—insa dake cikin parlourn ya nufa, akwai socks a kafafunsa, a haka ya zura toilet shoe É—insa ya shige ciki. Kai tsaye wash hand base ya nufa, wash hand sanitizer mai kyau da tsada ya É—auko, wanke hannunsa tas ya yi da shi, yana da tsabta sosai, komai nasa very clean gwanin ban sha'awa.

Waje ya fito bayan ya kammala, a saman sofa ya zauna, kafin ya fito wannan jami'in nasa da ya cire mashi takalma yasata a dryer ya É—auko mashi ruwa mai sanyi and glass cup ya kawo mashi saman table kusa da sofar da ya zauna, su dai waÉ—an nan jami'ai guda biyun nan aikinsu kenan su hidimta mashi!.

Yana zama ya ciro wayar tasa, gayyar miss calls dayawa ya samu, mum É—insa kawai ta yi mashi 10 miss calls kamar ba É—azun ba jimawa suka rabu ba. Miss calls na dad É—insa ya kai 20, É—an girgiza kai ya yi tare da furzar da iska mai É—an zafi daga bakinsa. A hankali ya jingina bayansa a jikin sofar tare da fara kiran number mum É—in nasa, da alama yafi sonta sosai sama da dad.

Bugu ɗaya ta ɗauka, tana daga zaune a office nata ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ga sanyin Ac na bugata, sannan ga kamshi mai kwantar da hankali a gauraye a cikin office ɗin ta ko'ina, securitys biyu suna gadin kofar shigowa, hannunsu ɗauke da manya manyan guns masu lafiya ba saɓa saiti.

Cike da tsananin so da kaunarsa ta ce. "Hello my baby".

Wani daddaÉ—ar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Mum.........." Katse shi ta yi da cewa. "I hope you get to the office safely?".

Ɗaga kai ya yi yana kallon cikin parlourn nasa, wato ita mum duk a tunaninta wajen aikinsa ya tafi, har da tambayar ya isa lafiya? Bata san yana nan yana aiki daddynsa da suka ɓoye mata ba, lallai akwai kura ran da ta gane gaskiya kuwa.

"My baby". Ta sake kiran sunansa jin bai amsa mata ba, bata san ya aka duniyar tunaninta a kan idan ta ganosu daddynsa yana ruwa tsundum bane, dan kuwa zai sha hukunci a hannunta ba kaɗan ba. (Ni kam na ce idan ma bata ce ta saki daddyn ba🤣🤣 e mana su ai kunsan mata tana saki a wajensu🤣 ba wani cikakken hankali ne ya ishi wasun su ba, amma ba ruwana na yi nan kada Smart ya ji abin da nace.)

"Mum everything is going well like the way you think". Ya faÉ—a a sanyaye, yana magana yana bin parlourn da kallo kamar bai san komai da yake ciki ba.

"How's your work? Hope you're enjoying the day?". Ta sake jefa mashi tambaya. "My mum". "My baby". "My mum". "My baby". Shiru ya yi tare da É—aura hannunsa a saman forehead

Mum da dad É—insa suna yi mashi son ransu, sai ya kira sunansu suma su kira nasa, sun saba mashi da wannan abin tun yana É—an shekara bakwai, sai ya ce mum ta ce baby, idan ya ce dad ya ce son, abin gwanin ban dariya.

Call É—in dad ne ya shigo wayarsa, dukka fa a kan abu É—aya suke son tambayarsa, shi ne kuma ya isa office lafiya sannan ya aiki, a kan wannan tambayar fa suka tara mashi miss calls har haka, kullum haka suke yi mashi, sai sun ji ya isa lafiya kuma yana cikin aminci sannan suke kama nasu aikin, wannan É—an nasu mugun ji da shi suke yi, suna kaunarsa fiye da kansu,....... Ni kam nace ai dole su so shi, dan kuwa shi kaÉ—ai kamar rai ne ke garesu, ga shi sun tsufa, dan shi kansa Smart É—in ya kai 30 years a duniya, kunga kuwa ai sun fara tsufa, basu ma sanya rai a kan samun wani yaron ba, dan a tunaninsu ba samu zasu yi ba, shiyasa suke bashi kulawa fiye da kansu, one in billions yake a garesu.

"Mum dad is call me let me pick his call". Ya faÉ—a a kasale.

Da okey ta amsa mashi kafin ta jero mashi jawaban da ta saba a kan lallai ya yi breakfast mai kyau tun da yaki ya yi a gida, sannan lallai idan ya yi aiki na awa ɗaya ya kwanta ya yi barci na awa biyu dan ya huta, kada ya yi wani tunani idan ba nata ita da dad ɗinsa ba, ya kula masu da kansa sosai, haka dai ta rinƙa jeramasa su kamar yadda ta saba, kullum haka take yi mashi. Wani irin haɗaɗɗen sumbata ta mannawa wayar tata a zuwan shi ta sumbata.

Okey kawai ya ce tare da katse kiran, dan in ya biyewa mum sai su kai yamma basu yi sallama ba, jawabinta baya karewa, idan ya ce mata shi fa yanzu ba yaro bane, sai ta ce mashi har gobe shi babynta ne, a baby take kallonsa, hakan bata yi mashi daɗi sam sam, mum ta ki yarda ya girma.........😅

Yana ɗaukar call ɗin daddyn ma abin da mum ta faɗa shi ya sake nanata mashi, okey nan dai ita ta raba shi da su. Yana katse kiran ya ajiye wayar, sam bai bi sauran miss calls ɗin ya kira ba, dan dama shi idan ba mum and dad ba baya bin miss calls na kowa ya kira, duk mai buƙatarsa sai dai ya Kiransa.

Shiru ya É—an kwantar da kansa yana kallon sama kamar mai nazarin wani abin, Allah ya gani yana kaunar iyayen nan nasa, yana jinsu a ransa tamkar ya yi masu numfashi.

Wayar tasa ce ta fara ringing again, ɗaukota ya yi ya kawota dai'dai saitin face ɗinsa. Ganin sunan dake yawo a saman screen ɗin ne ya sanya shi yin hanzarin picking tare da miƙewa ya nufi waje, dukkan nutsuwarsa ya tattara waje guda dan yin magana da wanda ya kirasa ɗin, da alama mutum ne mai muhimmanci a garesa.

Kai tsaye wajen ya nufa, yana waya yana tafiya har ya je ya shige cikin motarsa. Da gudun gaske motar ta tashi ya bar wajen. Office É—insa ya nufa wato ma'aikatansu na jami'an Secret Intelligence Service.
______________________🔥🌼❤️

DARK WORLD🔥

Idanun Ronnie cika suka yi tab da kwallah a lokacin da Sweetie ta kammala bashi labarinta, sosai ya ji tausayinta ya kamashi, bai taɓa jin tausayin wani ba a rayuwarsa sai yau, ajiyar zuciya ya sauke tare da sanya hannu ya ciro handkerchief daga aljihunsa, goge kwallan da suka cika mashi idanu ya yi, sannan ya matso kusa da ita sosai, sai kuka take yi hawaye duk sun wanke mata fuska, da alama labarinta ba mai daɗin saurara bane, handkerchief ɗin ya sanya ya fara goge mata hawayen nata da shi........ Abin da mamaki, ashe Sweetie ta san labarinsu kenan? Ta san su waye su?! Tabɗijam!. Amma yarinyar nan akwai basira da nutsuwa.

Rarrashinta ya fara yi a kan ta yi shiru. Da kyar ya samu ta dai'na kukan, ruwa ya ɗauko mata ta karɓa ta sha. Shiru ya zuba mata idanu yana kallonta, ita kuma ta duƙar da kanta ƙasa tana ɗan shesshekar kuka...... Abin da mamaki sosai gaskiya, Ronnie da yake irin wannan masarauta mai cike da zalinci kala kala, azaba kala kala mai taɓa zuciya bai taɓa zubar da kwallah wai dan an zalintar wani ko kuma yaga zalincin da ta ɗaga mashi hankali ba sai a kan labarin Sweetie, wannan wani irin labari ne to? Kada ku manta ɗazun fa aka datsewa wani wuya a gabansa amma rawa ma ya rinƙa tiƙa shi da master Devil ko a jikinsu, yanzu sai ga shi kwatsam yana yi wa labarin Sweetie kwallah, kai da mamaki sosai abin, shi fa bai taɓa zubar da kwallah a kan wani abin ba, tabɗijam lallai da matsala in kuwa hakan ne, ko me ta gaya mashi?.

Zuciyarsa ta karaya matuƙa yau a karon farko a rayuwarsa, bai taɓa jin karaya ko wani rauni na sai yau, duk sai ya jikinsa ya yi sanyi, har wani guntun ciwon kai ya ji.

Hannu ya kai ya riƙo nata hannayen, hakan yasa ta ɗago kanta tare da sauke idanunta a cikin nasa. "Where's your mum now?". A hankali ya faɗi maganar. "I don't know where is she". Ta bashi amsa.
Chapter 75 · 0% Book details