Sashe 46
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bashi da mafita dai a yanzu, ita kam Chuchu ko a jikinta, sai ma tsiya da take son yi mashi idan Akka ta ƙariso wajen. Ɗan raba jikinsa da nata ya yi tare da zuwa hannun a aljihun wandonsa. Handkerchief fara tas mai shegen kamshi ya ciro, sannan ya matso bakin hanyar.
Haba wa Akka na isowa wajen saboda tsiya irin nasa sai ya ware handkerchief É—in nasa ya rufe mata fuska da shi tare da toshe mata baki dan kada ta yi mashi ihu. Da ido ya nunawa Chuchun hanyar part É—in momma a kan ta tafi.
Ita kuwa dan tsiya sai ma kara jingina da jikin bangon wajen ta yi alamar ba zata tafi ba, baya son buɗe baki kada Akka ta ji voice ɗinsa, yasan tsohuwar nan sarai ta haddace voice ɗin kowa a gidan nan except voice na twins Obaid and Omaid, ai waɗan nan twins ɗin wlh ko Jaish baya rabe voice nasu, ko King baya rabesu, mommarsu ce kawai take rabesu, ita kaɗai ce ko a duhu ta laluɓasu zata rabe Obaid ta cire Omaid.
Yanzu yana yin magana zata gane voice ɗinsa. Dan haka sai ya sake nunawa Chuchun hanya a kan ta gudu, ai kuwa make mashi kafaɗa ta yi a kan ita gaskiya ba zata tafi ba. Kamar zai yi kuka, ga Akka kuwa tana ta ƙoƙarin kwace kanta ya toshe mata baki ga rufe mata ido da ya yi, sai ƙoƙarin taɓa jikinsa take yi dan ta tantance jikin waye ne ya yi mata wannan ɗanyar aiki, tab wlh idan ya kuskure Akka ta kwaci kanta ya shiga ɗari biyar ba uku ba.
Chuchu da tsiya taki tafiya, kamar zai yi kuka ya marai rai ce mata fuska yana bata hakuri ta hanyar motsa lips É—insa, kin yarda ta yi ta make kafaÉ—a tana toshe baki da hannunta saboda dariyar mugunta da ke son cubce mata.
Sai da ya wahala, Akka ta kusa kwatar kanta sannan Chuchu ta fara tafiyar yanga dan iya shege, har da wani murguɗa bashi good bye ɗinta tana tafiya cikin saiɓi kamar hawainiya, ji yake kamar ya jawota ya kifa mata mari, amma ba hali, zaman lafiya yake so da ita, haka ya hakura ya toshewa Akka baki yana kallonta har ta wuce ta hanyar part ɗin momma ta kurewa ganinsa.
Sai da ya tabbatar ta yi nisa sosai, sannan ya ja Akka har parlourn King, yana zuwa ya turata saman sofar King ya juya da gudun gaske ya bar parlourn.
Ai kuwa a ɗari Akka ta miƙe ta fara surfa bala'i wai tasan wlh ɗaya daga cikin jikokinta ne suka yi mata hakan, ko Jaish ko Jawad, dan sun fi kowa rainata a gidan nan, wlh ɗaya daga cikinsu ne ya yi mata hakan, dan haka ba zata kyalesu ba, dole King Zuhair da uncle Abbas su zo su ɗauka mata fansa, wlh ba zata yafe ba, har da cewa ita dai bata yi sa'an jikoki ba, har da karawa da cewa jikokin nata kamar masu karɓar huɗubar shaiɗan..........😂
King dake É—akinsa yana shirin fita fada ne ya jiyota sai surfa masifa take yi. Hakan yasa ya fito da sauri. A zaune saman sofa ya sameta. A hanzarce ya kariso wajenta yana tambayarta lafiya?.
Ai ina a fusace ta ce ya kira mata Abbas da Jahiz a waya duk su bar abin da suke yi su bi jirgin safe su zo, sai sun zo sun haɗu zata faɗi abin da aka yi mata.......... Kai wannan mata akwai rikici, rikitacciyar tsohuwa ce, uncle Jahiz dake ƙasar Brazil, shi kuma uncle Abbas ya tafi ƙasar China baya nan, amma dan balai saboda ta nunawa su Jawad ita take da su shi ne sai an haɗo mata kan iyayen nasu dukka, kai Akka duniya ce, kar ka sake ɓatacciya ta haɗoku, ba zata kyaleka ba, iyayenka zata sa a gaba, kana ji kana gani ranka na kuna ta zagesu tsab shi ne ta ɗauki fansa.........😂
King dai bashi da zaɓin da ya wuce ya bi umarninta, dan sai surfa masifa take yi, ɗaki ya koma ya ɗauki wayarsa, yau Yah Jawad ya ɓallo ruwa, kingdom of power yau ba zaman lafiya.
Number uncle Jahiz king ya fara kira. A lokacin da kiran ta shigo wayarsa yana zaune a saman wata iriyar luxury sofa wadda babu irinta ma a yankin Africa, kuɗi ta zauna mashi, tsayawa zayyana maku Daular guy ɗin nan ma ba zai yiwu ba, domin kuwa babu irin wannan ginin a Africa ma gabaɗaya, dollars ta yi kuka ta kuma yi mubaya'a, kun fa san manyan ƴan kwallon nan ba ƙaramin dukiya ne da su ba, bare shi Jahiz da yake shararren ɗan kwallo da kowacce team ke son sayansa ya buga mata kwallo, dan kuwa in ya shiga filli fa jama'a har wani irin ihu da fito na musamman suke yi, idan ya riƙi kwallo ba mai iya kwata ta daɗi a hannunsa. Sai dai fa shi ɗin jinin mulki ne ke gudana a jininsa, akwai shi da izza ga shegen iya shariya, baya kula masoyansa ko kaɗan, ko ɗaga idanu baya yi ya gansu, amma a haka kuma suke haukar kaunarsa, idan ba wasan team nasu ba ma dayawan jama'a basu son zuwa. A baya Manchester united yake bugawa kwallo daga baya real Madrid suka saye shi da, billions suka sayesa, dan yana da tsada sosai, ɗan kwallo ne mafi hazaƙa.
A gaskiya ma shi ya fi King Zuhair ma kuÉ—i ba uncle Abbas ba tukun nan, ya samu duniya kam iya duniya saura lahira.
Zaune yake a saman sofa daga shi sai short jessy trouser zuwa gwiwa, ta sama kuma single ce fara tas, jessyn jikinsa ma ba ƙaramin dukiya aka narka wajen sayansa ba, ga su da shegen kyau.
Guy ne iya guy, da ka gansa ka ga King Zuhair, babu banbanci kamar shi yake binsa wajen haihuwa, amma bashi bane, uncle Abbas ne, arab guy, fari tas da shi, ga hanci har baka, dollars ta zauna sosai, jikinsa har wani kyalli yake yi, cikakken namiji ne sosai, da ka gansa ka san ɗan kwallo ne na gasken gasken. Kafafunsa na sanye da sillpers na cikin gida masu bala'in laushi, ya yi crossing leg ɗinsa, hannunsa na riƙe da tsadaddiyar cup na cappuccino haɗaɗɗiya yana sha cike da class. Tsadaddun wayoyinsa ne a saman luxury glass table dake gabansa, ga wata tsadaddiyar laptop a gefe guda saman table ɗin, wannan parlourn nasa kamar ba'a duniya kake ba zaka ji idan ka shiga, su kansu sofas ɗin nasa kamar wasu jirage luntsuma luntsuma da su.
Wani irin daddaÉ—ar kamshin mai kwantar da hankali ne yake yashi a ko'ina cikin parlourn, ga sanyi Ac mai ratsa zuciya. Sai dai kash dukka wannan alatun nasa bashi da mata, katan gwauro ne bai cika cikakken namiji ba.
Picking call É—in ya yi cikin nutsuwa, da alama yana da nutsuwa sosai da sosai, komai cike da class yake yi.
"Good morning bro!". Ya faÉ—a kamar baya son motsa baki, voice É—insa sak na King Zuhair, sun yi kama sosai gaskiya, jini ba wasa ba.
Daga can King ya ce. "Akka ta ce ku bar duk abin da kuke yi tana son ganinku yau".
Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "Bro I have something very important to do, but me yake faruwa take son ganin mu? Ina da wasa champions league gobe fa".
Nisawa King ya yi. "Kai da ita ne wannan, ni dai na isar da saƙo, ka kira Abbas ka sanar da shi". Daga haka King ya katse kiran.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mayar da wayar ya ajiye.
Shi kuwa King komowa parlourn ya yi ya hau rarrashin Akka a kan tazo su je ciki ta gaya mashi me aka yi mata?. Shi kam Yah Jawad bin bayan Chuchun ya yi izuwa part na Momma abinsa, bai san Akka ta tada balli ba.
A parlourn ya iskota tana tsaye, ai tana ganinsa ta watsa a guje ta nufin ɗakin Momma, sai dai kafin ta shiga shi ma ya tako da gudu ya riƙota, ashe tasan ta yi mashi laifi, tasa shi ya kusa yin kuka.
Riƙo west ɗinta ya yi, wage baki ta yi zata yi mashi ihu ya yi saurin rufe mata baki.
"Yau sai kin gaya mun idan ni sa'an wasan ki ne? Nace ki tafi sai kika tsaya kina ganina ko? Wlh saura ki gayawa Akka ni na rufe mata ido zaki ga yadda zamu ƙare". Ya faɗa yana ɗaure fuska kamar ba shi ne ɗazun ya marairace mata fuska kamar zai yi kuka ba, yanzu kuma da ya samu ya kuɓuta daga haɗuwa da Akka shi ne zai nuna mata jan ido.
Fitowar Momma daga room nata zuwa parlourn ne yasa ya saketa tare da juyawa zai bar part É—in.
"Zo nan Jawad". Momma ta faɗa tana nufar saman sofa. Da gudu Chuchun kuwa ta nufi cikin room ɗin abinta, ta samu Momma ta kwaceta. Tana shiga ta faɗa saman sofa dake cikin room ɗin ta hau tiƙar dariya kamar zararriya, sai ta yi dariya sosai sai ta ɗan tsaya shiru, idan ta tuna yadda ya marairace mata fuska kamar zai yi kuka ɗazun sai ta sake watsewa da dariya kamar ba lafiya ba.
Shi kuwa Momma ta zaunar da shi ta shiga gaya mashi ya kula sosai, dan yana da tarin makiya a tarayyarsa da chuchu, dan haka ya ɓuye soyayyarsa, kada ya bari ma a rinƙa ganinsu a tare, ya yi kamar ya mance da ita ko sun rabu, dan wanda ya yi ƙoƙarin rabasu ɗin ya ji daɗi ya kuma ciresu a ransa kada ya kara haɗa masu wani tuggun, idan ta samu lokaci ta zauna da king zata gaya mashi batunsu, sai a sanya masu rana ayi bikin kowa ya huta, amma yanzu ya kula ya kuma ɓoye batun, sannan ya tsananta addu'a sosai, dan abu ne da ya haɗu da mushirikai, so ya kula sosai.