← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 211

Sashe 180

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai bata san lokacin da ta kurma ihu tare da dirowa kasa daga saman gadon ba, da gudu ta nufi waje. Allah sarki tun lokacin da uncle Abbas ya gaya mashi cewa jumma'ar nan za'a ɗaura auren Jannat da Rizwan shikenan ya dawo ɗaki ya kwanta, ya ƙasa iya furtawa uncle Abbas ɗin ma ko uppan, tin daga lokacin bai iya furta ko uppan ba, tun da ya kwanta a kan gadon nan nasa kuma bai tashi ba, ko sallar asuba bai yi ba, haka zalika bai ci abincin daren jiya ba, babu wanda yasan halin da yake a ciki.

Part ɗin momma Chuchu ta koma, tana zuwa ta gaya masu halin da ta gansa a ciki, ai ba wanda ya riga guyson da ya ce lallai a kirasa riga kowa miƙewa a cikin waɗan da suke zaune.
Ramish dake tsaye shi da Bilal a tsakiyar parlourn su suka riga kowa nufar hanyar fita, da sauri Dr Raj ya bi bayansu, momma ta riga Mummy bin bayansu.

Chuchu da hawaye ya gama wankewa fuska ne ta bi bayan momma da gudu, yau dai an ɓatawa guyson murnar Birthday ɗinsa, tuni ya watsar da batun ya bi bayan brothers ɗin nasa.

Suna shiga cikin ɗakin Ramish ya yi kansa a ɗari, Dr Raj ya riga Bilal ƙarisawa wajen, dan yadda suka ji numfashinsa yake fita tamkar wanda zuciyarsa take son bugawa, hankulansu ya yi mugun tashi, tuni momma ta ce guyson ya je ya kira masu King, ai kasa tafiya ya yi a in da ya tsaya ya fara yi masu ruwan hawaye, da yake shi hawaye sun mashi yawa, abu na faruwa kaɗan zai fara ruwan hawaye.

A tare su mummy suka ƙariso ɗakin ita da Yah Rizwan da Auta, sun je part ɗin nata tana ƙoƙarin fitowa ne ta ce masu su zo su je part ɗin Jawad bashi da lafiya.

Ai suna shigowa a miliyan ɗari Rizwan ya yi kansa yana ambatar sunansa, har bai san lokacin da ya kai hannu zai karɓesa daga hannun Ramish ba, da alama ya fita daga cikin hayyacinsa, ya manta su ɗin dik abu guda ne, tuni ya manta da hakan yana ƙoƙarin kwacesa daga hannunsu.

Dr Raj ne ya ce. "Rizwan calm down please, zan duba shi yanzu, In Sha Allah babu abin da zai faru".

Ramish ne ya ce da Bilal. "Kama shi Bilal".

A hanzarce Bilal ya kai hannu ya riƙoshi da nufin ya ja shi su fita waje, amma ina tirgewa ya yi yana cigaba da kiran sunan ɗan uwan nasa, ga dai numfashinsa na fita da karfi karfi amma kuma baya motsi kamar wanda ya mutu.

Momma ce ta ce Auta ta je ta kira King tun da Guyson ya kasa zuwa, ya ƙanƙame mummy yana ruwan hawaye, sai faɗi yake yi dan Allah a ce Yah Jawad ɗinsa ya tashi kada ya mutu.

Ita ma Autar dai kuka ta fara yi, amma ta fi guyson kwarin jiki, dan haka tana hawaye ta nufi fada wajen King.

King yana tare da uncle Abbas, dan wajensa uncle Abbas ya nufa dan ya tambayesa batun da gaske ne su Ramish sun zo?. Sai dai ko da ya tamnayesa sai ya ce a'a basu zo ba, dan shi ma bai san da zuwan nasu ba, dan haka sai uncle Abbas É—in ya yi zamansa kawai a zuwan ai Sarina bata sansu bane, watakila wasu baki ta gani ta ce su ne, so sai ya shashantar da maganar.

Chuchu kuwa hauka ta kusa yi masu, ta manta da family dik suna waje, ta manta ma cewa tana jin tsoron brothers É—in nata, tuni ta haye saman gadon tana kuka tana ambatar sunansa.

Kowa ya É—auka saboda shakuwar dake tsakaninsu yasa take wannan kuka, momma ce kawai tasan dalili, dan haka ita ce ta zo da nufin ta kamata su fita. Ina ai kin yarda Chuchu ta yi, ihu kawai take yi tana faÉ—in. "Dan Allah Yah Jawad É—ina ka tashi, Momma ki ce ya tashi, wayyo na shiga ukuna!!".

Harta mummynta bata san da batun soyayyarsu ba, ita dai tasan King ya sameta da batun jibi Jummaa kenan zai É—aura auren Jannat da Rizwan, a matsayinta na uwa tana da abin faÉ—e, sai ta ce Allah ya bada zaman lafiya kawai tun da Jannat É—in tana son shi, bata da wani abin faÉ—e illah ta tayasu da addu'ar zaman lafiya.

Mammien su Sarina kuwa, dik abin da yake faruwa a cikin family tana tsaye a gaban wannan mirror nata ga wani kwarya mai É—auke da ruwan tsafi a gabanta tana kallon dik abin da yake faruwa, tsabar mugunta sai ta yi amfani da tsafin nata ta rufe bakin Jawad É—in dan ma kada ya farka ya fara kiran sunan Jannat har a fahimci da wani abin a tsakaninsu, ta kuma rufewa ita ma Chuchun baki ta hanata kiransa da sunayen soyayya da take kiransa, sai dai ta yi ta ihun Yah Jawad ka tashi kawai. Yau ranta fes, sai daÉ—i take ji burinta ya kusa cika, wani irin daÉ—i na musamman take ji, musamman ma da ta ga Rizwan ya kusa zarewa, sai kiran sunan É—an uwan nasa yake yi, dama tasan Rizwan ba zai iya jure rashin Jawad ba, shiyasa bata damuba ta barshi zancen soyayarsa da Jannat ya isa gaban iyaye, saboda a cewarta shi mutuwarsa mai sauki ne a kan Jawad, amfani ta yi da raunin kowannesun.

Tasan Jawad zai yi wuya ya rayu idan ya rasa Chuchu, tasan idan Jawad ɗin ya mutu shi ma Rizwan da wuya ya sha, shiyasa ta yi masu haka, har wani irin shu'umin murmushi take saki a lokacin da idanunta suke kallon ƴan uwan a cikin tashin hankali, tsabar mugunta ta kara iza wutar soyayyar Chuchun a cikin zuƙatarsu dikkansu biyu da tsafinta.

A tare uncle Abbas, uncle Jahiz, and King suka shigo cikin room ɗin. A lokacin kuma Rizwan yana ƙoƙarin yi masu karamar hauka, dan gani yake kamar Jawad baya raye, saboda anyi kiran duniyar nan dik yaki motsawa, sun zuba mashi ruwa ma amma shiru bai motsa ba, kuma dai ga numfashi fa yanayi, abin akwai mamaki da ɗaure kai matuƙa.

Karfi Bilal ya sanya ya cicciɓi Rizwan sama suka nufi waje, dan ba zai barsu su yi abin da ya dace ba, ita ma Chuchun sai da momma tasa karfi ta jata suka nufi waje, mummy ma waje ta yi yunkurin fita da guyson dake aikin kuka, amma sai ya tirje yaki yarda, ya kankame King da hannunsa ɗaya, rabin jikinsa yana jikinta yana ƙoƙarin gudu ya bar jikin nata ya koma wajen King da suka shigo yanzu.

Ramish ne ya ce da mummy ta fita da shi ko ta karfi ne, idan ta je kuma ta tabbatar ta rarrashe shi ya yi shiru, kada ya yi kuka sosai ciwonsa ta tashi. Haka kuwa aka yi, sai dai uncle Abbas ne ya fita da shi, mummy ta kasa jansa, saboda ya tirje yana boƙarewa shi ba zai fita ba sai yaga Yah Jawad ɗinsa ya farka.

Uncle Abbas ya sa karfi ya É—aukesa suka fita, sai ihu yake yi yana wiwwintsila kafafu shi ba zai fita ba. Auta ma bin bayan Mommarta ta yi dan ta je ta lallashi Chuchu.

Ɗakin ya rage daga Ramish dake tallafe da Jawad ɗin, sai Dr Raj da yake ƙoƙarin cire rigan jikin Jawad ɗin, sai King Zuhair, dama ita Sarina bata dawo cikin part ɗin ba, Aneesa da Fanan ma bin bayan momma suka yi dan su je su rarrashi Chuchu, sai uncle Jahiz da ya kara cewa uppan.

Ai King ya manta ma da cewa su Ramish ya gani unexpect, tuni ya nufi Jawad, sai bai yi mashi kaman bakin da bai san da zuwansu ya gani ba, ciwon Jawad ya É—aga hankalinsa yasa ya mance da ya gansu a wajen.

Bilal ne ya dawo cikin É—akin hannunsa É—auke da boxes na magunguna da allurai, ya je ne ya rufe Rizwan a cikin É—akinsa, sannan ya kwaso kayan magunguna dan su ceto rayuwar Jawad É—in.

To quickly recovery our Yah Jawad, Allah ya baka Jannat idan alkhari ce a gareka, Allah ya kuɓutar daku daga makircin mammie, Allah kuma ya bawa dik wanda ya rasa Jannat hakurin rashi da iya juriya. Bari mu leƙa wani wajen, watakila kafin mudawo zaƙwaƙwurin doctornmu wato Dr Raj zai iya shawo kan matsalar.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

JIMETA.

Sanyin safiya ne ya ratsa shi yasa ya farka da daddaÉ—ar barcin da ya É—aukesa, a hankali ya waro idanunsa da suke jajir.

Gefensa ya fara juyawa domin ganinta, sai dai kash bata nan, cikin nutsuwa ya juyar da kallonsa ya fara bin ɗakin da kallo, mamaki ne ya yi matuƙar kamasa na ganin gari ya yi haske kamar asuba ta ɗan gota.

A hanzarce ya miƙe zaune, aikuwa da gaske ne asuba ta gota, lallai yau yaron Mommarsa ya yi barci mai daɗin da har ya makara ba tare da ya sani ba. Ɗan dafe kansa ya yi yana mamakin hakan, jikinsa dik a mace haka ya miƙe ya nufo waje.

A tunaninsa zai ganta a tsakar gida, sai dai wayam bata nan. Abin dariya baya karewa a kauyen su Mahnoor, sai da ya tsaya ta cikin ɗakin ya leƙa waje ya gani bappa na nan a tsakar gida ne ko baya nan, abin kunya su haɗa idanu da bappa bai je masallaci ba, to me ya hanasa zuwa zai ce wa bappan kenan? Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsarta, dan haka ya yi godiya ga Allah na ganin bappa baya nan a tsakar gidan.

Da sauri ya fito ya É—auki buta, ruwa yasa ya shiga toilet dan yin tsarki.

A gaggauce ya fito ya yi alwala ya komo cikin É—akin, zuciyarsa cike tab da tunanin ina ta tafi da sassafiyar nan, ko wayewa gari bai gama yi ba.

Sallarsa ya gabatar cikin nutsuwa tare da zama saman daddumar ya fara gabatar da addu'oi. Ya ɗauki a kallah 1h a saman daddumar kafin ya miƙe ya koma saman mattress ɗin nasu.
Chapter 180 · 0% Book details