← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 211

Sashe 108

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kallon ƙasƙanci da walaƙanci ta bita da shi ba tare da ta amsa gaisuwar ba.

"Yah Jawad ina ne office É—inka? Dan ni wucewa can zan yi".

Yadda ta yi maganar sai ta baka dariya, kishi kiri kiri, ko waye ya ce mata ita ce budurwar tasa? Kai Chuchu ikon Allah. Ita kanta P.A ta lura da balai'n kishin da yake kwance a cikin idanunta, hakan yasa ta fahimci duk yadda aka yi Chuchu matar ogansu ce ko kuma wadda zai aura, É—aya cikin biyu, dan haka sai ta kama kanta kada ta ci duka, a cikin ranta faÉ—i take.
"Shiyasa master baya ɗaga idanu ya kalli mutane kenan? Allah mai iko, dama kana da wannan haɗaɗɗiyar beauty flower yaushe zaka kalli wasu matan? Yanzu kenan master a maza fa yake kallonmu, dan idan irin waɗan nan mata suna a gabanka a maza zaka rinƙa kallon sauran mata, ni kam yau ina Rashidah take ne? Ita sarkin ji da kyau har tana ikirarin zata iya sace zuciyar oga da wannan ɗan guntun kyan nata, to yau ta zo ta ga kyau a nan, ai tana zuwa kusa da wannan zata zama kamar namiji, Allah ya yi halitta a nan, ga iya ɗaukar gayu, ji yadda kayan jikin nan nata ya zauna mata da kyau kamar dan ita aka yi su, master ban ga laifinka ba na kin ɗaga idanu ka kallemu, dole ka ruɗe a nan gaskiya, ashe a maza muke a gabaka, yau ina Rashidah ne". Sai sambatu take yi a cikin zuciyarta, da alama wannan P.A ƴar iska ce, dan har da fa wani lashe baki take yi tana karewa Chuchunmu kallo.

Ta kai karshen zancen zucin nata bata san lokacin da dariyar mugunta ya kubce mata ba, ba dariyar komai kuma ba ne ya kubce mata face dariyar Rashidah da take jiji da kai ita kyakkyawace, to ashe dai a namiji ma Jawad yake kallonta, shi ne abin da ya bawa P.A dariya.

Ganin Chuchu ta dalla mata harara ne yasa ta yi cak ta tsayar da dariyar. Shi kuwa ko kallon in da table É—in P.An yake bai yi ba, kamar bai ji ta yi dariya ba

"Fuck dirty girl!". Chuchun ta faÉ—a a bayyane.......... Ni kuwa nace ashe dai Chuchun mu ta iya faÉ—a, ashe ba'a iya gayu aka tsaya ba har da tsiwa, kunji ta kama zagin mata ba gaira babu dalili, sai kace ance mata ita ce budurwar yayan nata.

"Jannat lafiya?". Ya faÉ—a a sanyaye yana kallon face É—inta dake É—aure kamar hadari.

"Ni dai ka nuna mun office É—inka kawai". Kamar zata sa kuka yi maganar.

Cigaba da tafiya ya yi suka shiga cikin nasa office É—in. Suna shiga a maimakon ya wuce saman kujerarsa, sai ya zauna a saman É—aya daga cikin sofars set dake cikin office É—in, a saman three seater ya zauna.

Yana zama sai ga wani matashi da ba zai wuci 20 years ba, a gabansa ya zo ya tsugunna ya hau cire mashi takalma izuwa sock.

Bayan ya kammala ya miƙe ya kaisu ma'ajiyarsu, sannan ya fice, shi ma miƙewa ya yi izuwa saman nasa kujerar ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.

"My Queen zan iya samun ruwan sha?". Ya faɗa yana kallonta, ta zauna saman sofa tana ta aikin turɓune fuska.

Shi fa duk abin da take yi yau kara sanyayya mashi zuciya take yi, dan kishin da take nunawa a kan nasa ma ya ja sonta ya ƙara ninninkuwa sosai a ransa.

Miƙewa ta yi ta isa gaban freezers dake cikin office ɗin. Buɗe ɗaya ta yi ta ciro ruwan, ta dawo wajen kyakkyawan show glass da ta gani a ta kusa da shi, a shake yake da cups and small plates kala kala for snacks. Guda ɗaya ta ɗauko mai kyau, a gabansa saman table ta ajiye mashi da nufin ta juya.

Hannunta ya riƙo, da sauri ta juyo, saman laps ɗinsa ya nuna mata a kan ta zauna. Babu musu ta zauna tana mai kallon face ɗinsa.

"To zuba mun ruwan". Yana magana yana É—aga kansa izuwa kallon pop.

Ɗaukar robar ruwan ta yi tare da fara ƙoƙarin buɗewa, kasawa ta yi hakan yasa ta ajiye tana faɗin. "Yah Jawad ya yi tauri sosai ba zan iya buɗewa ba, amma ka kira budurwar nan taka ta zo ta buɗe mana, dan naga ita lukuta ce kirar adawa ko sumudawa zata iya".

A ɗari ya sauƙo da kansa haɗe da kallonsu izuwa kan ɗan bakin nata, wato dai a fakaice ita a dole ta zagi P.A da take yi wa kallon budurwarsa ce, ba shakka Chuchu ita ma akwai faɗa kam.

ÆŠaukar ruwan kawai ya yi tare da buÉ—ewa ya zuba a cup É—in bai ce ko uppan ba. Sosai ya sha sannan ya cireta daga bakinsa.

Kawo mata saitin bakinta ya yi, dama ita ma tana buƙatar shan ruwan, dan haka sai ta buɗe baki ya sanya mata. Ɗan dai'dai tasa ta cire baki.

Tunani ya fara yi ta yadda zai bayyana mata soyayyarsa a gareta, can dabara ya faɗo mashi ya ce ta rufe idanu sai ya kaita gaban mirror dake cikin office ɗin, sannan ya ce ta buɗe idanu taga budurwarsa, tana buɗewa sai taga kanta a cikin mirror hakan zai ƙayatar.

Na'am ya yi da wannan shawara da zuciyarsa ta basa, yana ƙoƙarin yi mata magana aka yi knocking na kofar.

Shiru ya É—an yi na na Æ´an sakani kafin ya ce wanene?.

Daga waje P.A ta e ita ce. Izinin shigowa ya bata, a ɗari Chuchu taso barin jikinsa ya yi saurin riƙeta yana kallon face ɗinta.

A gaban table ɗinsa ta ƙariso, cikin girmamawa ta ce. "Sir daman waɗan nan bakin namu ne suke jiranka a meeting office". Tana magana tana aikin satar kallonsu, sun yi mugun dacewa sun kuma tafi da imaninta sosai.

Kai kawai ya jinjina mata alamar ya ji ba tare da ya yi magana ba. Juyawa ta yi ta tafi tana mai É—an waigowa ta saci kallonsu. Muguwa tunanin Rashidah ce kawai a ranta, tana ta faman dariyar mijinta ta ciki, su Rashidah masu kyan sace zuciyar oga.

"Jannat ban aran minti biyar ina zuwa ko?". Ya yi magana yana kallonta.

Okey ta amsa tare da barin jikin nasa.

Miƙewa ya yi a hanzarce ya fice. Yana fita ta koma saman chair ɗin ta zauna.

Shiru ta yi tana tunanin Yah Rizwan É—inta, a haka har ya dawo ya sameta, ya je ya sanya hannun.

Yana zuwa ta miƙe ta bashi waje, zama ya yi tare da mayar da ita saman laps ɗin nasa.

"Yah Jawad wai ina budurwar taka ne?". Ta faÉ—a kamar zata yi kuka.

Tausayinta ne ya ji ta kamashi, wato har yanzu abin yana cinta a rai, hakan yasa ya ji gara ya gaya mata abin da yake ran nasa kawai, dan ya saukaka mata abin da take ji na zafin kishi.

Juyowa ya yi tare da matso da face ɗinsa daf da tata har suna iya jiyo sautin numfashin juna, wani irin ƙurawa juna idanu suka yi, jiran amsarsa kawai take yi, shi kuwa ya zubawa kwayar idanunta ido yana kallon tsantsar soyayyarsa dake kwance a cikinsu.

Saƙo na musamman zuciyoyi suka shiga aikawa juna, a hankali ya haɗe face ɗinsu waje guda, wani irin duniya na daban ya tsinci kansa a ciki.

Ƙasa ƙasa cikin salo mai matuƙar jan hankali ya furta. "My Jannat".

Sarƙewa muryarta ya yi a in da ta kasa amsawa da na'am ɗin, saboda yadda ya haɗe fuskokinsu ya jefata a cikin ruɗani da fargabar me zai biyo baya.

"My Jannat bani da kalaman da zan iya bayyana maki abin da nake ji a yanzu, baki bai isa ya faÉ—i abin da suke tare cunkushe a cikin zuciyata ba, ba abin da zan iya cewa face in ce maki..............".

Knocking na kofar da aka yi ne ya sanya ya dakata da maganar bai iya kai karshenta ba.

Cikin wani irin kasala ya É—an yi baya kaÉ—an ya raba fuskokinsu ya koma ya jingina bayansa da jikin chair É—in.

Kasa jurewa ta yi da sauri ta kwnatar da kanta a saman kirjinsa tana sauke numfashi a hankali hankali, ɗazun ta rasa ina hankalinta ya shiga da har ta iya tsayuwa tana kallon cikin idanunsa ya kuma haɗe fuskokinsu waje guda, har yana ƙoƙarin kamar zai yi kissing ɗinta kuma duk tana kallon cikin kwayar idanunsa, abin ya bata mamaki, soyayya yasa tama mance a wace duniya take.

Da kyar ya iya motsa lips É—insa wajen furta. "Come in". Dan yasan P.A ce.

Turo kofar ta yi ta shigo, a karo na biyu ta same Chuchun kwance a saman kirjinsa, abin dai ya yi matuƙar ƙayatar da ita, sai ta ji ina ma ace ita ce, sai dai matsalar ita ɗin hajiya one seater ce a ƙiba, ai kunji ma Chuchun ta faɗa da bakinta ɗazun, tana da kiɓa sosai.

Idanunsa a lumshe ya ce. "Lafiya?". "Sir dama sir Rizwan ne yake neman iso".

Ai da jin sunan Rizwan bai san time É—in da ya waro idanunsa waje na. A É—ari ita kuma ta É—ago kanta daga saman kirjin nasa, kai tsaye face É—insa ta kai kallonta, while shi ma juyo da kallonsa a kanta ya yi.

P.A dai mamaki suka bata, daga jin sunan Rizwan duk sun ruÉ—e kamar marasa gaskiya, shi Jawad tunani yake yi ya za'ayi ya bari yayan nasa ya kamashi da ita a nan? Ai sai ya ce dama ya saba. Ita kuma tunani take yi shikenan ya zo sai su yi hira.

"Zan iya tafiya sir?". P.A ta katse masu kallon juna da suke yi, dan ta lura kamar sun manta da ita.

Kai kawai ya gyaɗa mata, a hanzarce ya ce wa Chuchun ta shiga ƙasar table ɗinsa ta ɓuya, tun da in ta shiga babu mai iya ganinta sai shi da yake ta wajen, waɗan da zasu shigo daga baya ba zasu ganta ba.

A hanzarce ta sauƙa daga jikin nasa ta shige ƙasan table ɗin, dan ta lura ba da wasa yake yi ba, so kada ta ja ransa ya ɓaci a banza.

Tana shigewa shi kuma Rizwan ya shigo, ƙananan kaya ne a jikinsa, ya yi kyau fresh da shi.
Chapter 108 · 0% Book details