← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 211

Sashe 127

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komai da kuka sani na cikin wannan haÉ—aÉ—É—en luxurious bedroom É—in nasa sai da wannan iska ta kifar da shi saboda karfinta, yadda kuka san wani walkiya haka iskan ta shigo.

Wani irin haske na ban mamaki ne ya bayyana a cikin wannan iska mai kama da guguwar, gabaɗaya glasses na cikin ɗakin sai da suka tarwatse, show glass dake kusa da bed ɗin mai shake da Bibles kala kala ma haka ta jijjigo ta faɗi ƙasa, gabaɗaya glass ɗin ya tarwatse ya Bibles suka fara watse ƙasa.

Dressing mirrorsa ma ya tarwatse watsa watsa, chandelier ɗakin ma jijjigowa ya yi da karfi ya yo ƙasa zai faɗi, in kuma ya faɗo to fa a tsakiyar cikin Ronnien ɗin zai faɗi, in kuma ya faɗi a kansa to fa da wuya ya rayu, dan chandelier tana da girma sosai.

Aikuwa yana kwance yana fuskantar sama, dan haka yana ganin yadda chandelier nan ta jijjigo ta yo kansa, amma ina ko motsawa bai yi ba, tamkar babu shi a É—akin.

My people's wani irin iska ce wannan? Su ba'a cikin daji suke na! Sannan ba lokacin iska ba! Anya lafiya kuwa? .

Amin afuwa yau bana jin daɗi ne, zazzaɓi da ciwon kai, amma duk da haka nace bari na ƙokarta kada na barku a cikin kewa, shiyasa kuka ga short page, da babu gara ba daɗi, sai mun haɗu on Monday In Sha Allah, idan kun ban hot comments na yi maku weekend.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 4/11/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘ZANGO NA BIYU....✍️📚🔥

34

Aikuwa yana kwance yana fuskantar sama, dan haka yana ganin yadda chandelier nan ta jijjigo ta yo kansa a dubu, amma ina ko motsawa bai yi ba, tamkar babu shi a cikin É—akin.

A fujaje chandelier tayo kansa, ko datse idanu irin tsoron nan bai yi ba, idanunsa kar a kanta, yadda kuka san wanda ya yi suman kwance.

Dai'dai saitin daf zata sauka a cikin nasa ne sai kuma ta tsaya cak tamkar wadda aka riƙe, babu kuma wanda ya riƙeta.

Ɗan Lumshe idanu ya yi tare da sake warosu, a hankali ya miƙe zaune yana fuskantar wannan haske da yake ƙoƙarin riƙiɗewa alamar halittar ɗan adam yana bayyana a cikinsa.

Abin gwanin ban mamaki da ban tsoro, haka ya zuba idanu yana kallo daga wannan haske har ya riƙiɗe ya zama complete halittar ɗan Adam. Babban mutum ne sosai ya bayyana, sai dai yana da karfi da kwarin jiki sosai, baka iya ganin face ɗinsa bare ka iya tantance wanenen?.

Ya fito cikin wata iriyar dressing wanda kai daga gani kasan dukiya tana cin ƙaniyarta a wannan Daula. Hannunsa na riƙe da irin sandar nan na sarauta mai tambarin kan bakar damusa ta wage baki, ga garma garman hakwara tamkar zata cinye ni.

Takalmar dake kafafunsa sun kasance covers ne masu bala'in kyalli kashe ganin idanu, na zallar madarar gold ce, doguwar alkyabbar jikinsa ta sauka har tana ja a ƙasa ta rufe takalmar tasa, kansa na sanye da hular alkyabbar tasa, from up to down ɗinsa komai na jikinsa fararene ƙal except takalmarsa da suka kasance gold, ya rufe komai na jikinsa, ko kalar fatarsa ba zaka iya ganewa ba.

Baka iya ganin face É—insa sakamakon wannan haske da ta fara bayyana a farko ta tattaru ta koma saitin face É—in nasa ta rufeta, hakan ya hana damar ganinsa.

Abin dai ba'a magana.

Wace iriyar haske ce mai karfin kashe idanun gani ta bayyana a bayansa, idanun bawa ba zai iya kurawa wannan haske idanu ba, sai kashe mashi karfin gani da kwarin idanun.

A hankali hasken ya fara riƙiɗewa yana komawa golden color. Babu ko alamar mamaki da al'ajabin abin a face ɗin Ronnien, da alama ya saba da ganin fin hakan ma, hankalinsa a kwance, shi sai yunwar dake damunsa ne ma take murɗa mashi ciki.

A hankali wannan farin haske ta riƙiɗe ta koma wani irin dandatsetsen katafaren the most powerful seat of king in the world da ba'a taɓa yin irinsa a duniya ba, kujerace wadda aka ƙawata ta musamman, gabaɗayanta da zallar madarar gold aka yita, sannan gabaɗaya jikinta an yi mata kwalliya ne da wasu irin wuƙaƙe masu bala'in kaifi ta bayanta kenan ba ta wajen zama ba, ta jikinta kenan, wuƙaƙen ma na zallar madarar gold ne, kujerar tana da tsawon kai sosai, koda an zauna a kanta, duk tsawon mutum kansa ba zata yi dai'dai da kanta ba, sai dai ya lume a cikinta, daga can karshen kayinta kuwa an yi shi ne design of black tiger, shegen damisa mai haɗarin gaske kenan, yafi jar damisa haɗari, shi yana iya kashe zaki har lahira idan ya fusata.

Design ɗin damisan ya fita sosai, a takaice dai kujerar nan ya wuce tunaninku a ƙawatuwa, ga wasu duwasun zinari masu haske tas dake manne a jikinsa ta ko'ina, abin dai sai wanda ya gani, bana jin a duniya ma akwai kuɗin da zai iya sayan wannan gold kujerar. Tana da girmar two seater wajen zama, kyallinta sai ɗaukar idanu yake yi.

Cikin wata iriyar ƙasaita ya zauna a samanta, duk tsawon kan da kujerar take da shi sai da kansa ya kusa kai tsawonta da ya zauna, saboda tsawonsa dogo ne sosai, duk da yake babban mutum yana da wani irin jiki tamkar wani tsohon ɗan Wrestling ɗin da ya shafe tsawon shekaru ana gwabzawa da shi a fili, a murɗe yake sosai.

Yana zama ya É—aga wannan scepter king É—in nasa ya fara nunnuna dukkan wasu kayan da suke cikin room É—in.

Abin al'ajabi baya ƙarewa a duniya matuƙar kana raye, gabaɗaya kayan da suka fashe a ɗakin ne suka fara komawa da kansu yadda suke. Duk abin da ya nuna da wannan scepter king ɗin nasa sai ta koma yadda take kamar bata taɓa tarwatsewa ba, gabaɗaya glasses ɗin sun koma, Bibles da suka zube a ƙasa duk sun koma cikin glass ɗin da kansu, a hankali chandelier ma ta bar saitin kan Ronnien ta koma sama mazauninta.

Wani irin fitinannen kamshi mai kwantar da hankalin mai shaƙa da ban taɓa jin daɗin kamshi irinsa bane ya gauraye gabaɗaya ɗakin, sai wani irin iska from nowhere mai daɗin gaske ne ya fara kaɗawa a hankali hankali, kofofi da winduna fa a rufe, sai Allah kaɗai yasan daga ina Black Tiger ya ƙaƙalo wannan daddaɗar iska dake ƙaɗawa gwanin birgewa da sanya zuƙata nishaɗi musamman ga masoya, sai dai kash su dai yaya ne da kaninsa ba masoya ba!.

Har lokacin idanun Ronnie yana a kansa babu ko kyaftawa, duk kaifin ganin wani idanu ba zai iya ganin cikin wannan haske ba, amma shi Ronnie ya sanya kwayar nasa a ciki ba tare da ya ji komai ba, da alama dai kaifin ganinsa daban yake da sauran mutane, ga shi babu alamar tsoro a cikinsu ko É—igo.

Aka ce kowa a duniyar nan in ma mutun ko aljani yana da weakness ɗinsa, dole akwai in da ake gazawa, babu wanda yake dai'dai sai Allah, to hakance, shi ma Black Tiger dai Ronnie ne weakness ɗinsa a duniya, ya ƙasa jurar halin da Ronnie ɗin ya shiga ne yasa ya taso da kansa ya zo in da yake. Tun da yake a rayuwarsa a empeir ɗin nan bai taɓa fitowa daga wannan room ɗin nasa ba sai yau, kuma duk a dalilin Ronnie ya fito, to why Ronnien ya samu wannan matsayi haka? Kome alaƙarsu? Meyasa duk wannan zafin nasa, zalincinsa! Muguntarsa! Karfin ikonsa! Ronnie ya zama shi ne rauninsa? Me dalili? Komai dai dole yana da dalili! Dan haka suma dai akwai dalili.

Kuma shi Black Tiger tabbas bashi da ƴan uwa kamar yadda yan cikin birnin suke faɗa, hakance, Ronnie ba ɗan uwansa bane, shi shiƙaɗai yake tun bayan ɓacewar mahaifinsa a doron duniya, a idanun mutane mahaifinsa ɓacewa ya yi, a idanunsa kuma mutuwa baban nasa ya yi, abin da yasa mutane suke cewa ɓacewa babansa ya yi ba mutuwa ba shi ne, ranar da baban ya mutu, insect of a sanya shi a akwati a kaisa kabarinsa sai suka ga gawar ta ɓace ɓat daga saman gado mulki da yake kwance. Ranar Black World sunga tashin hankalin da basu taɓa zatan zasu gani ba!!. Sai dai kuma tun ranar da ya bar duniya ya bar cikin kwakwalen mutanen birnin, tamkar an shafe masu saninsa, shiyasa suke cewa basu taɓa ganin wani ɗan uwan Black Tiger ɗin ba a duniya!.

A lokacin da baban nasa yake raye shi ne yake zaune a kujerar da Black Tiger ɗin ya zauna a yau, shi baya ɓoye kansa, kowa ya san shi a birnin, sai dai kuma shi yake ɓoye Black Tiger tun yana ƙarami hakan yasa ya taso a mai ɓoye kansa, shi kaɗai yasan dalilinsa na yin haka.

My people's izuwa yanzu me kuka fara tunani a kan wannan Daula ta Black Tiger? Alamu dai sun nuna mutanen birnin suna da gaskiya na cewa Black Tiger ba mutum bane kenan?.
Chapter 127 · 0% Book details