← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 211

Sashe 3

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma Yah Jawad ka É—an ci abincin mana". Ta faÉ—a kamar zata yi kuka, sam bata ji daÉ—in yadda yaki cin abincin bane.

"Kina son in ci ne?". Ya faɗa tare da ƙaƙalo murmushin dole dan ya kwantar mata da hankali, amma zancen gaskiya hankalinsa a tashe sosai yake, kawai Rizwan ya gaya mashi kada ya bari kowa yasan me yake faruwa ne yasa ya danne, amma ga dukkan alamu maganar da suka yi da Rizwan ta yi mugu mugun ɗaga mashi hankali.

A hanzarce cikin farinciki ta furta. "E Yah Jawad ina son ka ci".

"Zaki bani a baki?". Ya faɗa yana kura mata ido, kuma ya yi maganar yana ƙara ƙaƙalo murmushin.

Kai ta gyaÉ—a mashi. "E zan baka a baki Allah in dai zaka ci".

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da alama maganar ta yi mashi daÉ—i sosai. Gaya mata abin da zai ci ya yi, da sauri ta zuba mashi tare da É—aukar spoon na fara É—ebo mashi.

Saitin ɗan bakinsa ta kai mashi tana sunkuyar da kanta ƙasa. A fili ya furta. "A matsayin wa zaki bani abincin a baki?".

"Yayana da na fi kauna". Ta bashi amsa. "Da gaske kin fi kaunata sama da kowa?". Ya yi tambayar da alamar mamaki a saman fuskarsa. Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e.

"Meyasa kika fi kaunata?".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara jero mashi bayani. "Saboda kafi sake mun fuska sama da su Yah Bilal, sannan ka fi su kaunata, kana mun duk abin da nace nake so, kana wasa da dariya da mu saɓaninsu Yah Bilal da ko murmushinsu ma ban taɓa gani ba, sannan kan......."

Katseta ya yi da cewa. "Meyasa kika ce nafi kaunarki Jannat?".

Girgiza kai ta É—an yi. "Yah Jawad ni ma ban sani ba, kawai dai nasan kafi kaunata shiyasa na fi kaunarka sama da kowa, daga kai kuma sai Yah Rizwan, sai Yah Raj, ku kaÉ—ai nake so".

Ajiyar zuciya ya sauke tare da kai hannunsa ya riƙo hannun nata, bakinsa ya kai spoon ɗin, a tare da shi da ita suka juye mashi abincin a cikin baki yana kallon face ɗinta.

Sake mayar da spoon ɗin ta yi zata ɗebi abincin bayan ya saki hannun nata. Hannun nata ya sake riƙewa yana faɗin. "Ajiye spoon ɗin ki ciyar da ni da hannunki".

Ba musu ta ajiye ta fara É—iba da hannunta tana bashi a bakin. Sosai ya ci abincin, bai yi zaton zai ci mai yawa har haka ba, amma da yake suna hira tana bashi sai ya ci mai É—an yawa.

Bayan sun kammala ya ce su je ya kaita school akwai in da zai je. Miƙewa ta yi tare da ɗaukar jakarta suka nufi waje.

Dai'dai zai fita part É—insu mai gabaÉ—aya, family part na King kenan, a dai'dai katafaren gate É—in suka ci karo da Mammie tana shigowa, da alama ta biyo bayan Aliyah ce.

Shi kuwa Jawad yana riƙe da hannunta, sai hira take zuba mashi suna tafiya, dama zai je amsa kiran mammie ɗin ce kafin ya wuce ya kaita school, shiyasa suka nufo kofar fita ba tare da mota ba, shi fa Jawad gabaɗaya ya mance da cewa Mammie ta ce kada ta kara ganinsa a tare da Chuchun.

Dakatawa daga tafiyar da yake yi ya yi. Da kallo ya bi Mammien, bata ce mashi ko kala ba saboda jiga jigan zakunan matasan mayakan dake tsaron gate ɗin, saboda su yasa Mammien bata tanka masu ba ta wuce kawai. Ganin ta wuce bata ce masu ko sannu bane yasa shi ma ya juya ya bi bayanta, kuma har lokacin yana riƙe da hannun Chuchun.

Parking space suka nufa, bai bi Mammaien cikin gida ba, ya shiga motarsa kawai dan ya kai beb É—insa school, lokaci ya tafi sosai, ta kusa yin latti, su Fanan har sun tafi sun barta, sun nemeta dan su tafi tare, da suka san tana tare da shi sai suka tafi abinsu.

Wucewa da ita school ya yi, ita kuwa Mammie tana shigowa part ɗin kai tsaye wajen Momma ta nufa. My people's duk yadda kuke tunnin makircin Mammie ya wuce tunaninku, lumbu lumbuce ita ɗin, nunawa take yi babu wanda ya kaita son zaman lafiya, nunawa take yi tana kaunar Momma kamar ranta, ta manne da Momma kamar me, suna shiri, Allah sarki Momma bata san true colonta ba, bata san cewa ita ɗin musa ce a zahiri fir'auna a baɗini. Haka take nunawa Mummyn Gimbiya Chuchu ma kauna over, Maman Gimbiya Aneesa ce kawai basu shiri, basu haɗa inuwa da Mama, kamar wuta da audiga haka suke, kar ta san kar ne, dukkansu sarakan makirci ne, kun san idan fa kana aikata abu sai kaga kamar kowama aikatawa yake, hakan yasa basu zama inuwa ɗaya, in dai suka haɗu sai aikawa juna baƙaƙen maganganu da habaici game da harare harare suke yi, sukam sun fitar da kishin balbalin nasu a fili.

Kuma yadda kuka ga Mammie da iya makircin nan haka Gimbiya Sarina take, Fanan dai babu ruwanta, nutsatsiya ce, ba ruwanta da makirci da kirsa, amma Sarina kam ita ta sha nonan Mammaie É—in haikam, Mammaien na cire kafa ita kuma zata sanya nata kafan a munafurci da kirsa da kisisina haÉ—e da makirci, Æ´ar karama da ita amma idan ta haÉ—a maka wani makircin sai ka yi zaton macece yar shakaru 50 wadda ta ga jiya ta ga yau, ba'a banza ta zama master team É—in su Obaid and Omaid ba ai, iyashegensu ne kusan É—aya, sai dai su sunfita, amma akwai kamanceceniyar halayya da wasu dabi'u a tsakaninsu.

A parlourn ta isko Momma, kusa da ita ta zauna tare da sakar mata fuska kamar wata ta Allah, sannan ta É—aga mata gaisuwa.

Mommar ma duk da murmushi bai wani dameta ba, ba zaka taɓa ganin tana murmushi da waɗansu ba sai da yaranta, su ne kawai suke ganin murmushinta sai King namu, amma ganin Mammie ɗin ta sakar mata murmushi yasa ita ma ta ɗan saki ɗan siriri murmushi kafin ta amsa gaisuwar tata.

Cike da kwarewa a iya kirsa da makirci ta fara janta da hira, ba komai yasa take son jan Momma da hira kuma take yawan zuwa wajenta sannan ta nuna tana kaunarta over ba face dan san sanin wani sirrin Momman, gabaɗaya matan gidan banda Mummyn Gimbiya Chuchu duk suna zargin Momma tana ɓoye masu wani sirri tsawon shekaru, sun buga sun buga suna son sanin gaskiya, amma da yake ita bata ma san suna yi ba, kuma da zuciya ɗaya take zaune da su, shiyasa Allah bai basu ikon sanin komai a kan hakan ba. Wannan dalilin yasa ita Mommar da Mama basu shiri ko kaɗan, dan mama tana zargin tabbas akwai abin da Momma ta ɓoye masu a tsakaninta da King.

Sosai Mammie ta zage tana ta janta da hira, Momma fa bata da yawan magana wlh, amma nacin Mammie take sawa ta rinƙa ɗan tayata hirar jefi jefi. Ba komai yasa bata da yawan magana ba face faɗar da mahaifiyarta take yawan yi mata a kan kada ta bari kowa ya san sirrinta, kishiya fa ba'a bar bawa yarda gabaɗaya bace, shi ne yasa bata sakewa ta saki baki tana magana, in kunji tana hira sosai to da yaranta ne ko kuma da masoyinta King.

Mommar izuwa yanzu ta fara mamaki a kan yanayin hiran Mammie a duk lokacin da ta zo in da take, a duk lokacin da ta zo bata da hira da ya wuce na shekarun baya, ba zata taɓa yi mata hira kan abubuwan yanzu ba, sai dai ta yi ta kaƙale kaƙalen abubuwan da suka suɗe. A gaskiya da can baya an yi wani irin zama a cikin family part ɗin nan, ba ƙaramin faɗa aka yi ba, Momma ta sha bakar wahala a gidan fiye da tunaninku, bata shiri da kowa, kusan haukatata aka yi a cikin gidan, akwai lokacin da har ya zamana tana zaune ita kaɗai tana magana, wani lokaci sai ta yi ta buga kanta a bango har sai ya fashe ya yi ta jini, wani lokaci kuma ta yi ta faman kuka babu gaira babu dalili, abubuwa dai kala kala, to babban abin da yake damun Mammie har ita da Mama suke zargin akwai abin da Mommar ta ɓoye masu shi ne lafiya da ta samu sosai, yadda take gudanar da rayuwarta yanzu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, abin ya basu mamaki, suna son sanin ya aka yi hakan ta faru?.

Haka dai Mommar ta cigaba da biye mata suna hira sama sama, ita kuma Aliyah tana wajen Mummyn Gimbiya Chuchu, sai hira suke yi kamar kawaye, Allah sarki Mummy fa bata san mijinsu Aliyah take hari ba. Mama kuwa sai yanzu jikinta ya fara É—an rage raÉ—aÉ—in da take ji na azabtarwan su Omaid da suka yi mata.

After some hours.

Da misalin karfe ɗaya na dare, shirye take cikin wasu irin baƙaƙen kaya, doguwar riga ce tana ja a ƙasa, sai ta ɗaura bakar alkyabbarta a saman kayan, shi ma alkyabbar yana jan ƙasa, cikin wani irin tafiya wadda takun sahu baya bayyana ta fito daga cikin ɗakinta. Ta kofar baya ta fita daga part ɗin nasu.

Tafiya ta fara yi cikin taku kamar na marasa gaskiya ta miƙi wata hanya mai tsawo. Ta ɗan yi tafiya mai ɗan nisa kaɗan, duk in da ta zo giftawa idan ta kalli warriors a wajen sai ta laɓe, da yake warriors ɗin suna kai komone a cikin masarautar sai ya zamana idan sun wuce sai ta fito ta cigaba da tafiya.

Wani irin canza kala idanunta ya yi izuwa red color sosai lokacin da ta kusa isa bakin babban gate na farko na masarautar. Bakin gate ɗin shake yake da manya manyan zakunan warriors a wajen, jiga jigai masu ji da karfi ranon commander Zafar, a tsaye suke kamar waɗan da aka sassaƙa. Ta gabansu ta zo ta wuce amma basu sami damar iya ganinta ba, canza taku ta yi izuwa takun ƙasaita lokacin da ta zo giftawa ta gabansu. Wucewa ta yi kai tsaye ta nufi waje. Tana fita wajen gate ɗin kuma ta ɓace ɓat, babu ko alamarta...............
Chapter 3 · 0% Book details