← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 211

Sashe 184

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita ya bar gidan mai gabaÉ—aya, dan baya son su haÉ—a ido a yanzu. Yana fita kuma suka haÉ—u da Ibrahim kanin maman Mahnoor É—in.

Jerawa a tare suka yi suka nufi hanyar gona. Ita kuma ta jima a kwance a saman mattress ɗin kafin daga bisani ta miƙe, kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta lallaɓo ta fito waje, yau ta jita a sabuwar duniya ta musamman, har wani ɗan munafikin jiri jiri take gani.

Waje ta nufo, dik da tana cikin hijabi ya taɓa mata tula tulan nata har yanzu ji take yi kamar hannunsa yana a kansu, sai ta ji kamar yana matsa mata su, abin ku da bata saba ba.

Tana fitowa waje Nenne na shigowa cikin gidan, katari suka yi a in da ta tsaya a tsakar gidan tare da yin ƙasa da kai, dik sai ta ji kamar tsirara take, kunya kamar ta shige cikin ƙasa, sai take ganin kamar Nennen tasan me ya faru, kamar ta ga kiss da Jaish ya yi mata.

Ita kuwa Nenne wani irin ɗan iskan matsiyacin kallo ta fara binta da shi, so take ta fahimci wani abin, sai take ganin kamar Jaish ya cika aiki shiyasa take wani rakuɓe rakuɓe.

Ƙasa ta yi da murya kamar kishiyoyin da suka haɗa kai suna gulmar uwar mijinsu. "Ke mijinki yana ciki?". Ta faɗa cike da fargabar amsar da zata bata, tana tsoron ace tana nan.

Kai ta fara girgiza mata alamar a'a baya nan, kanta a ƙasa taki ɗagowa.

Haba jin baya nan yasa ta É—aga murya. "Dan ubanki meyahanaki fitowa ki yi mun aikin da kika saba yi".

Ƙasa iya bata amsa ta yi, dan ba zata iya yin magana ba, Jaish ya kwance mata notikan ƙwaƙwalwa, abin da bata taɓa saninsa ba, bata yi tsammani ko tunanin makamancinsa ba da rana tsaka suna ganin juna ya wani kama ya sha mata ɗan bakinta dan tabbatar rashin kunya irin nasa.

"Ina magana ba zaki bani amsa ba sai na taka ruwan cikinki a wajen har sai kin mutu ne?".

Jikinta ne ya fara kerma, sai ta fara ruwan hawaye, domin kuwa bakinta yaki iya buÉ—uwa ta bata amsa, sai kawai ta fara kuka.

Nufota gadan gadan ta yi da nufin ta daketa, sai da ta isota gab da ita kome ta tuna sai kuma ta fasa, a cikin ranta ta ce kenan ya tabbata mijin nata ya cika aiki, tun da ga shi ko magana ma ta kasa iya yi.

"Wuce ki zo ki gyara mun É—akina, dama ban sharesa ba". Ta faÉ—a a gadarance, irin ta isa da ita É—in nan. Ba komai yasa ta fasa dukanta ba kuma face tana tunanin a kowani lokaci Jaish zai iya shigowa cikin gidan, kada ya shigo ya sameta tana ruwan hawaye ya zamar mata matsala, shi ne yasa ta dakata bata kai mata jibgar da ta yi niya ba.

Da kyar ta iya buÉ—e baki ta ce. "Kiyi hakuri amma ni hamma ya hanani yin aikin komai sai na tambayesa".

Eyeee zaro idanu waje sosai ta yi, bata taɓa expect ɗin irin wannan amsa daga gareta ba, ba ƙaramin fusata ta yi ba, cikin fushi ta ɗaga hannu da nufin ta yi mata duka har sai ta kasa miƙewa, a wannan gaɓar ɓacin rai yasa ta manta da cewa Jaish ne mijinta fa, sai ta yi yunkurin jibgarta.

Ina ai bata tsaya ba, gudu ta yi ta bar mata gida, dan kuwa zancen mijinta yana a ranta na kada ta tsaya wani ya daketa, sai ta watsa a guje ta barwa Nennen gidan.

Baki galala Nenne ta buÉ—e tana bin bayanta da kallo har ta fice ta bar gidan, dama ita Mahreen tun da ta gama cin abincinta ta wuce wajen bappanta.

Tana fita gidan ta dakata da yin gudun ta fara tafiya cikin nutsuwa, yunwa take ji baiwar Allah, ta fito da nufin ta nemi abincin da zata sa a bakin salatinta amma Nenne ta hanata yin hakan ma.

Kai tsaye wajen bappa ta nufa. Tana tafiya tana waige waige, dan a tunaninta Nenne zata biyo bayanta.

Tana tsaka da waige waige bata ankara ba sai ji ta yi ta bugu mutun. Baya baya ta yi kamar zata faÉ—i, a É—ari ta É—ago kanta domin ta ga wanene.

Ba ƙaramin razana ta yi ba na ganin yadda ya ɗaure fuska yake binta da wani irin mugun fusatatcen kallo.

Murya na kerma ta ce. "Hamma....... Hamma Faisal ina......... Ina kwana". Tana magana maganar yana rarrabewa.

Ko uppan bai furta ba, sai ma wani irin harara na musamman da ya bita da shi, dan a cewarsa ita ce nan ta ci amanarsa, dan da ta ce fir bata son Jaish bappa ba zai yi mata dole ba, dan haka yanzu ya tsaneta kuma har da cin alwashin ba zai rabu da ita ba sai ya É—auki fansa.

Takowa ya fara yi tana tinkarota da nufin ya aikata mata dik abin da ya zo cikin ransa.

Baya baya ta farayi tana zaro idanunta. Ganin da gaske yake kara tinkarota yasa ta juya ta watsa a guje. Sai dai bata yi nisa a gudun ba ta ci karo da su Salisun Inna Rabi dake nemanta dan É—aukar fansa su ma. Ga kuma Faisal É—in ma ya biyo bayanta, kai jahilci dai bata yi ba a rayuwa wlh.

Ihu su Salisu suka saka suna murnar yau sun kamata, ga shi kuma a cikin gonaki ne su yi mata duka su gudu babu wanda zai san su suka yi, amma fa a cewarsu.

Salis shi ne a gaba ya nufota yana faÉ—in. "Yau ai gudun naki ya kare ko akwai saur.............".

Bai ƙarisar da maganar ba ya dakata, ya zaro idanun nan waje kamar zasu faɗin ƙasa yana kallon Faisal dake bayanta wanda ya iso wajen ba jimawa.

Ita ma zaro idanu ta yi tana kallonsa tana mamaki me ya gani yake zaro idanun.

A miliyan ya juya kamar kafarsa zata tsinke saboda gudu ya bar wajen.

A hanzarce ta juya domin ta ga wenenen a bayan nata. Tana juyowa sai taga Faisal ya ɗaga sandar hannunsa zai buga mata Jaish dake bayansa ya riƙe sandar, wannan dalilin yasa Salis suka bar wajen a guje, su ƴan uwansa ma sun rigasa barin wajen, dan su tun Jaish bai iso wajen ba suka hangosa, hakan yasa suka gudu.

A tunanin Faisal bappa ne ya riƙe mashi sandarsa hakan yasa ya juyo da karfi dan ya gaggaya mashi maganganu son ransa. Sai dai kuma yana juyowa suka yi ido biyu da namijin gaske, ai bai san time ɗin da ya saki sandar ba, ya koma gefe yadda zai ji daɗin ganin Jaish ɗin da kyau.

Jefar da sandar a gefe ya yi tare da miƙa mata hannu a kan ta zo. Ba musu ta nufesa dan a tsorace take da Faisal. Kamar zai yi wa Faisal ɗin magana sai kuma ya fasa, saboda yasan in ya ce zai yi magana ransa ne zata kara ɓaci yaja ya karya Faisal a banza, shiyasa ya wuce, amma ba wai dan ya barsu bane, so yake ya haɗasu da su Salis ɗin dikka ya ɗauki kwakkwaran kataki a kansu wanda gobe ko da kuɗi aka basu ba zasu nufeta ba, ko ganinta ma bazasu so su sake yi ba.

Cikin gonar bappa ya nufa hannunsa riƙe da nata, suka bar Faisal tsaye yana binsu da kallon takaici kamar zai haɗiyi zuciya ya mutu.

Suna shiga cikin gonar akwai wani faffaÉ—ar bishiyar gwaiva mai wani irin faÉ—i ta tsakiya kamar kujerar zama, a kasan bishiyar suka tsaya, sannan ya sanya hannunsa dukka biyu a saman waist É—inta ya É—aga ta sama, ya É—aurata a saman bishiyar ta zauna kamar kujera, sai ya zama tana daga zaunen tsawonsu ya yi daidai.

Ai bata san lokacin da murmushi ya subce mata ba, ta manta da tana jin yunwa, bappa yana can wajen kiwo sun zo gonarsa zasu kashe juna da love su shuka flowers É—in kaunarsu bai sani ba.

"Meya fito dake daga gida?". Muryarsa ce ta katse mata murmushin da take yi.

"Nenne ce zata dakeni shiyasa na gudu". Ta bashi amsa tana sunkuyar da kai ƙasa.

Jinjina kai ya yi har cikin ransa ya ji daɗin hakan, kuma ya kudurta dole yau ba sai gobe ba ya yi mata tsakani da Nennen nan in ba haka ba ta kuskura ta sake taɓa mashi lafiyar jikinta to fa zasu ga abin da basu taɓa zato ba, shi yanzu ya ji daɗin duniya a tattare da ita, dan haka jikinta nasa ne ba nata ba, jiya ya yi barci cikin nishaɗi har da makara saboda daɗin kasakcewarta a jikinsa, dan haka babu wanda zai sake taɓa mashi jikinta ya zauna lafiya..... (To fa. Maman Sultan kina ina? Jaish dai ya ɗanɗani daɗin duniya za'a fara ɗaukar fansar dik wanda ya taɓa mashi jikinta😅🤭 eyee su Malam Jaish, aa ban ga laifinka ba, ai jikinka ne ma daman, oh ni Bintu ɗiyar babana, ina ganin al'amura a wajen Jaish namu na gargajiya 🤭)

Ganin ya luluƙa duniyar tunani ne yasa ta sanya hannunta a saman shoulder ɗinsa dan ji take yi kamar zata faɗi ƙasa shi kuma bai ankara ba ya afka tunani ya barta.

Ajiyar zuciya ya sauke ya jin hannunta a jikinsa, É—ago kai ya yi ya kalleta da kyau, ga yanayin wajen akwai É—an sanyi madaidaici, dan a bayan wannan bishiyar gwaiva fadamar nomar shinkafa ce a wajen, a nan bappa yake nomar shinkafa, kun san kuma dik in da fadama take to fa akwai yalwar sanyi a arear.

Yanayin wajen akwai daÉ—i ga masoya, ga iska mai daÉ—i ta ganyen bishiyoyi suna kaÉ—awa, sosai ya ji wani irin tsumin soyayya na tsuma shi, ga tsumin sha'awa dake addaba mashi.

Ɗago kai da ya yi ya kalleta babu abin da ya zo ransa face kiss da ya yi mata ɗazun, ba ƙaramin daɗin abin ya ji bafa, bai ki ya yi ta shanye mata baki daga nan har dare ba, abin akwai sugar amma fa in ji shi tom.

Zubawa laɓɓan nata idanu ya yi yana wani kallonsu cike da kwaɗayin ya sake sha.
Chapter 184 · 0% Book details