← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 211

Sashe 44

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yake su basu É—auki dollars da mahimmanci ba, kai bama su san banbancinsa da kuÉ—in Nigeria ba, ita dai da taga dubu É—aya a rubuce a jiki sai ta yi tunanin ko irin dubu É—ayan Nigeria ne, bata san wajen miliyan É—aya da rabi ake magana a kan dollar dubu É—aya ba. Dan haka rashin sani yasa ta sake zarar dubu É—aya ta nufi waje abinta bayan ta É—auki hijabi Zee É—in ta sanya a jikinta.

Har lokacin su maman Haidar suna parlourn. Maman Haidar ce ta ce. "Khadija ina zaki je a daren nan?". Cikin halin ko in kula ta ce. "Abu zan saya a waje gwaggo".

"To amma kada ki jima kuma ki kula kin ga dare ya yi"...... Kash wato a duniya idan ba ka nunawa wasu kai ma É—an iska bane fa bazaku zauna lafita ba, yanzu dai ga shi maman Haidar ta fara yin biyayyar dole gasu Khadija, ta fara tausaya masu dan dole ba dan tana so ba sai dan gudun kada Khadija ta daketa, wannan shi ne maganin shege sai É—an iska, maganin biri karen maguzawa.

"A daren nan ne zaki fita?". Cewar Hauwa da bata gajiya da shegen shisshigin tsiya.

Ko sannu Khadija É—in bata ce mata ba, bama ta kalli in da take ba, dan wani irin haushin Hauwa da take ji kamar ta shake shegiya ta kashe, idan ta ce zata kulata to wlh za'a sake tabka irin kuskuren da aka yi sati bakwai da suka wuce, dan wlh yadda Zainab ta bata labarin abin da ya farun nan ji take ta kashe Hauwar kawai ta huta.

"Khadija ba dake nake magana bane? Nace kada ki fita da daddaren nan ko?". Hauwa ta sake faÉ—a kamar wata uwarsu, hegiya bata gajiya da shisshigi a lamuran mutane.

Yadda kuka san da mutun mutumi take magana ba Khadija ba, ko juyowa bata yi ba bare ta ganta, ta sanya kai ta yi waje abinta, dan wlh in ta juyo zata iya sumar da Hauwa da duk abin da ta gani a gabanta É—auka zata yi ta bugawa hegiya, amma gudun kada shaiÉ—an ya yi galaba a kanta ne yasa taki juyowa, addu'a take yi Allah yasa tafi karfin zuciyarta, da haka ta nufi waje.

Kai tsaye shagon mai sayar da provision ta nufa. Kayan tea masu inganci ta sayawa Zainab É—in, bayan mai shagon ya haÉ—a mata komai sai ta bashi wannan dalar da ta É—auko.

Zaro idanu ya yi yana kallon kuɗin, ya kasa iya gaya mata cewa a shagon nan nasu basu da kuɗin da zasu iya bata canjin wannan kuɗin nata. Ya saki baki yana ta kallon kuɗin har ta kwashi abubuwan da ta saya ta ƙara gaba abinta, bata tsaya neman canji ba, bama ta san tana da canji ba, dan abubuwan dubu ɗaya dai'dai a kuɗin Nigeria ta karɓa, na gaya maku ganin kuɗin take yi kamar dai'dai yake da kuɗin Nigeria, ita dama ba shiga media take yi ba bare ta iya sanin farashin dollar, ba waya ne da ita ba, idan kunga ta riƙe wayar mamarta ma to game take bugawa da wayar, so bata san komai dan gane da fashin kuɗin ba.

Hanyar gida ta nufa sai sauri take yi, kamar daga sama daga bayanta ta ji ance. Khadija................. A hankali ta juyo domin taga wanenen da ƙoƙari ya iya ganeta a daren nan, hanyar ba wani haske ne sosai da shi ba, bugu da ƙari sabuwar unguwa suke, bata san kowa a unguwar ba to waye ya ambaci sunanta?

Tana juyowa sai taga......................✍️🔥🦋

___________________________🔥🌹

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

Gimbiya Zunaira🌹

Ihu sosai take kurmawa da iya karfinta na karshe, wani ƙosasshen doki da ya yi kanta a guje ne yasa ta sanƙare waje guda tare da kurma ihu mai sautin gaske, ga shi dai dokin da babanta yake yawan hawa ne, amma saboda rashin mutunci irin na dokin nan bai ji tausayinta ba ya yi kanta da nufin ya murkusheta, ko tsayawa bai yi ya ga kamanninta da King Zuhair ba bare ya tausaya mata...........😅 (Wai doki bai san kamanni bane?😫 Meyasa ba zai tsaya ya fahimci tana kama da King Zuhair kuma jininsa bace?😫)

Kanta kawai ya yi da nufin ya tattaketa, haba tsabar tsorata har sai da numfashinta ya ɗauke cak, tana ƙoƙarin zubewa ƙasa Hoorain ya tareta da hannu ɗaya ta faɗa saman faffaɗar chest ɗinsa, hannunsa ɗayan kuma da yake riƙe da yellow da jan kyallen ne ya fara ƙaɗawa dokin a face ɗinsa. Ai da gudu dokin ya juya ya bar wajen a in da ya bazama cikin sauran dabbobin, dukkan sauran dawakan sun watse sun bazama cikin gonar.

Jefar da kyallen ya yi tare da riƙota da kyau yana kallon face ɗinta, kamar dai kullum kayan warriors ne a jikinsa. Dama kun san tsakaninsa da Auta akwai amana sosai, to tun fitowarta daga family part ya hangota, yana tsaye da abokansa suna hira suna nishaɗi ya hangota, tun daga kan yadda yaga tana tafiya ƴar tsanɗo ya fahimci bata da gaskiya, ya fahimci akwai abin da take son aikatawa na rashin gaskiya, hakan yasa ya ce da abokan nasa yana zuwa.

Bai jira amsarsu ba ya bar wajen cikin takun jarumta, a hankali ya bi bayanta ba tare da ya bari ta sani ba, duk in taga mayaƙa sai ta ɓuya, shi ma sai ya dakata da binta, idan ta cigaba da tafiya sai ya bi bayanta, idan yaga zata juyo sai ya ɓuya, haka suka rinƙa tafiya har izuwa bakin gonar. Lokacin da ya ga ta yi wa mayaƙan bakin gate ɗin wayo ta saki tattabarun nan sun tashi sama sai da ta kusa sanya shi murmushi, ƴar karama da ita wai ita ma ta yi wayo, ta yi wa manyan warriors wayo, bata san cewa ba wayo ta yi masu ba, kawai dai a matsayinta na Gimbiya ne basu isa su ki bin umarninta ba shiyasa suka bi tattabaru, bugu da ƙari ta kasance Auta a cikin family, sannan ita ɗin sanyin idaniyar kowa na cikin family ne, wannan dalilan yasa suka yi hakuri suka bi tattabaru.

Hoorain dai saura kaɗan ta sanya shi murmushi, haka ya laɓe ya zuba mata idanu yana ganinta har ta yi dabara ta buɗe kofar gate ɗin ta shiga. Cikin tafasar jini ya rufa mata baya, sai dai yana zuwa ya tarar da ta kulle gate ɗin ta ciki.

Ganin haka yasa bai yi ƙasa a gwiwa ba ya yi zafin naman haurawa ta dogon kakkarfan katangar wajen, dan gudun kada wani abin ya sameta, shi yasan me a cikin gonar, sannan idan wani abin ya sameta ya shiga tara ba uku ba, dan shi King Zuhair zai hukunta, saboda alhakin kula da ita a wuyarsa yake, shi aka damƙawa kula da duk wata motsinta, so ko ciwo ta ji shi za'a hukunta, hakan yasa ya haura ta gini ya bi bayanta dan gudun kada babansa commander ya jibgesa, kunsan commander shi ne mai hukunta duk wani mai laifi, kuma gara mashi ace wani ya hukuntasa a kan Abbu ɗinsa, dan in ya kama shi mantawa yake yi da shi ɗansa ne, sai ya lallasashi idan sun je part nasu ya yi jinyarsa.........😅

Commander namu baya wasa kuma baya son kai, aiki yake gudanarwa dai'dai tsakani da Allah.

Sosai ya ƙurawa face ɗinta ido yana kallo, ta tafi da tunaninsa, ga kuma tumatunta luwai luwai irin na Jaish in ji Mahreen kamar bread........😅

Ya shagaltu da kallon kyanta ya fara jin ihun wasu daga cikin dabbobin wajen, gonar yana ƙoƙarin ruɗewa da kukan dabbobi daban daban, ba komai bane ya ja hakan kuma face ɓallewan da dawakan nan suka yi, sun bazama cikin gonar, so sun watsa wasu daga cikin dabbobin ma. Kafin ya yi wani yunkuri sai ganin wasu daga cikin dabbobin ya yi suna ta watsewa, Auta ta ja komai na ƙoƙarin rikicewa.

Ɗago kai ya yi yana tunanin yadda zai yi da ita ya samu ya kaɗa dawakan nan ya mayar da su wajensu, tunani yake yi a ina zai kwantar da ita, ga shi ta suma. Yana tsaka da tunani wani ƙosasshen doki ya yo kansu a haukace.

Ai kuwa bai san lokacin da ya kwantar da Autar a ƙasa a wajen ya miƙe ya tinkari dokin gadan gadan ba. Cikin jarumta ya yi nasarar kama linzamin dokin tare da daka wani uban tsalle ya haye bayanta. Haba wani irin haniniya dokin ya yi tare da ɗaga kafafunsa biyu na gaban nan sama yana cigaba da yin haniniya, jan linzaminsa ya yi da karfi nan take ya kaɗashi suka nufi wajen da suke dama. Da gudun gaske dokin ya nufi wajen. Ciki ya mayar da dokin kafin ya dawo ya saɓi Autar a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye ya nufi wajen da King yake zama idan ya kawowa gonar ziyara, akwai waje na musamman da aka tanada, ya sha kayan alatu da luntsuma luntsumar kujeru, an ƙawata wajen matuƙa da kayayyaki masu ɗaukar hankali, sannan ga shinfiɗu na alfarma irin na gidan sarauta masu kwalliyar gashin jimmina. Ga throw pillows da aka zuba a saman shinfiɗun.

A saman doguwar sofa ya kwantar da ita ya juya, yadda yake tafiya a buÉ—e zaka gane yana da jarumta sosai, babu tsoro ko kaÉ—an a tattare da shi, ko da yake assistant commander ne shi É—in, dole ya yi namijin jarumta sosai.

Wannan kyalle yellow and red É—in ya É—auko ya nufi dawakan dake ta gudu a cikin gonar, haÉ—a kansu ya fara yi yana kaÉ—asu dan ya mayar da su in da suka fito.

A lokacin kuma warriors dake gadin gate É—in suka fara knocking na gate É—in ta waje cikin tashin hankali, dan kuwa sun san King ya hana kowa shiga wajen ba tare da izininsa ba, so idan suka yi wasa yau sai sun shiga hannun commander!....... Tab lallai kuna tsaka mai wuya, shiga hannun commander ai ba alkhari bane, kowa baya kaunar hakan!!.

Hoorain yana jinsu amma bai tanka masu ba, sai da ya mayar da dabbobin dukka, sannan ya nufi in da take kwance. Ruwa ya ɗauko a cikin freezer dake wajen ya ƙariso wajen nata.
Chapter 44 · 0% Book details