← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 211

Sashe 15

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita ma Zainab dake ƙunshe a cikin ɗaki tana fama da zazzaɓi mai zafi babu wanda ya kulata, basu bi ta kanta ba, ba dare ba rana tana cikin ɗaki, bata taɓa leƙowa ko parlourn, har ɗaki Sadiq yake binta da abinci idan ya faki idanunsu Maman Haidar basa gidan, idan sun fita sai ya shigo gidan ya kawo mata abincin, sun hana shi shiga gidan ne yasa yake shiga a sace. Yanzu haka sai haukar neman Khadijan yake yi ba dare ba rana, har ma ya shigar da report, dan Zainab ta gaya mashi cewa Khadija tun ranar da maman nasu ta kashe babansu bata sake ganinta ba, tashin hankalin da Sadiq ya shiga sam ba zan iya fassara maku ba, kusan hauka ɗan tahalikin nan ya yi. Haƙiƙa ya tabka babban danasani na barinsu da ya yi ya koma Kaduna, kukan zuci yake yi yana faɗin laifinsa ne, da yana nan koma yaya zai hanata aikana wannan babban kuskuren.

Yarinyar nan Zainab duk ta fita a hayyacinta, ta dawo shiru bata magana, ko ka yi mata magana sai dai ta girgiza maka kai kawai ko ta gyaÉ—a ta, amma ba bakin magana, ta zama abar tausayi, har rama ta yi!.

Shi kam Haidar ma da alama baya garin, dan shiru kake ji, da yana nan dai zai ɗan leƙo koma yaya ne

Wannan shi ne halin da familyn Baban Zee suke ciki, bari mu leƙa wani season ɗin.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

❤️🔥RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 20/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘STEP TWO....✍️📚🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

❤️𝐓𝐇𝐄 𝐂𝐑𝐎𝐖𝐍 𝐎𝐅 𝐈𝐍𝐉𝐔𝐒𝐓𝐈𝐂𝐄💔🥺 𝐎𝐑 🖤𝐀 𝐃𝐀𝐑𝐊 𝐖𝐎𝐑𝐋𝐃🌑

RAWANIN ZALINCI ko BAKAR DUNIYA. Shi ne sunan da suke kiran wannan birni da shi, É—ayawa daga cikin mazauna wannan birnin ne suke kiranta da CROWN OF INJUSTICE, wasu kuma su kirata BLACK WORLD. Meyasa sunanta ya kasance a haka? A tarihi ya nuna cewa shekaru da dama da suka suÉ—e, babu kasa a wannan wajen ma bakiÉ—aya, daga baya aka kirkireta, Amma mu shiga cikin labarin, koma menene dalili a hankali zamu ji komai.

Dark world, birni ce mai matuƙar girma, akwai tsawo da kuma faɗin kasa gabaɗaya, sannan birni ce mai yelwar abubuwa da dama, irinsu abinci nauika daban daban, dan suna noma sosai, ruwan sha mai tsabta da masana'antunsu ke bugawa, ga ishasshen ruwan noma koda rani ne, dan suna da tapkeken teku dam mai matuƙar girma da sarkinsu ya kaddamar masu shekarun baya, suna da yelwar isassun kayan sakawa, dan suna da manyan camfanoni dake sarrafasu a birnin, wanda suke sarrafa kayan sakawa da sauran abubuwansu na amfani, suna da yelwar kasar noma, kaso sittin cikin ɗari na mazauna wannan birni da noma suka dogara, da akwai makiyaya, sai dai basu da yawa, akwai ƴan kasuwa, ma'aikata da dai sauransu.

Birni ne mai cike da kawa tare da ɗaukar hankali, suna da matuƙar tsabta ta yanda ko leda ba zaki gani a kan hanya ba idan kana tafiya, akwai masu sharan kan hanya kullum safe da yamma, sannan a kowani lungu da saƙo akwai manya manyan abubuwan zuba datti ta yadda ba zaka ga datti a kan hanya an zubar ba, idan abin zuba sharan ya cika sai a kai bayan gari a zubar, shi ma wannan akwai masu kula da wannan ɓangaren, haka zalika suna da gine gine masu matukar kyau da ɗaukar hankali, ga manya manyan tituna da suka keta har ta cikin unguwanni, wajajen wasanni haɗe da wajajen yawon buɗe idanu, manya da ƙananan jiragen ƙasa, jiragen sama, manya manyan buses, danƙara danƙaran motoci da dai sauransu.

Komai nasu abin burgewa ne, ga su da tsari wa rayuwarsu, kama da ga shigarsu mu'amalarsu, yanda suke rayuwa, cuÉ—anyarsu, tsabta da dai sauransu duk abin birgewa ne.

Ga dukkan alamu kuma basu son hayani, kuma basu son faÉ—a. Sai dai kuma babban abin birgewa da birnin nan shi ne, duk wanda ka É—aga idanu ka kallah in ma matashi ko dattijo, to sai ka gan shi da kirar mayaka, abin da abin mamaki, mafiya yawan waÉ—an da suke simtiri a tsakiyar birnin kuma mata ne, zaka iya wuce mata hamsin ba tare da ka kalli namiji É—aya ba, kasuwanninsu, gonakinsu da sauransu, dukka mata ne zaka tarar a wajen ba maza.

Yanayin dressing na kayan jikin matan wannan birni ya kasance irin dogayen sket ɗin nan ne zuwa har ƙasa, da riga zuwa ƙugu, yanayin yanda sket ɗin nasu yake sai ya baka sha'awa, dan daga ta sama ya kamasu tare da fitar musu da shapes nasu, daga zuwa dai'dai gwiwa kuma, ya buɗe sosai kamar umbrella har zuwa ƙasa, sannan suna da wata shiga da suke yinta a duk ranar jumma'a da kuma ranar lahadi, ita ma ta kasance shiga ce mai matuƙar burgewa da ɗaukar hankali, riga ce dogowa zuwa ƙasan gwiwarsu, rigar tana da maɗauri a tsakiyar cikinsu, sai kuma ƴar karamar hannun ke gareta, shi ma rigar like A shape take, shi ga ce ta zuwa wajen bautarsu. Ko wacce mace ka kallah zaka tarar da irin ɗinkisu kenan, kuma yana da matukar kyau tsantsa a jikkunansu, duba da yanayinsu na rashin kiba, ga bala'in shape mai tsananin kyan gaske da suke da shi, shape nasu akwai matuƙar ɗaukar hankali, daga manyansu har yara, tamkar su suka yi wa kansu.

Kuma abin mamaki da burgewa kusan kamanninsu iri É—aya, fararene kal, zaka iya wuce mata hamsin farare ba tare da ka haÉ—u da baka or chocolate color ba, gasu da bakin gashi tamkar su suka bawa kansu.

Sai dai ga dukkan alamu gabaɗayansu mutanen birnin suna da addini na daban, akwai abin da suke bautawa dukkansu, ba musulmai ba ne, kuma da yuwuwar addini ɗaya suke bi, abu ɗaya suke bautawa, suna da yelwar tsawon gashi wanda mafiya yawansu ya kai musu har tsakiyan bayansu wasu kuma har ƙugunsu, basu ɗaura ɗankwali sam sam a kawunansu, suna yin abubuwansu bisa bin doja da oder.

Sai harkokin gabansu suke yi, ba su wani damuwa da komai da kowa ba, da alama akwai halin ko in kula a tattare da su sosai.

Daga gefe tsallaken titi wajen wani makeken rumfa taron wasu gungun matasa ne wanda za su iya kai su 20 a wajen suke zaune, wani kayatatcen rumfa mai matukar kyau wanda yake tamkar da zinari aka yi shi saboda tsantsar kyau. Dukka mazan dake wajen shigarsu iri É—aya, sannan dukkansu kirar warriors ne a tattare da su, wandon jikinsu ya kasance brown color mai É—an faÉ—i, sai riga mai maÉ—auri a dai'dai ciki, while faffaÉ—ar kirazansu a buÉ—e, dan gaban rigar a buÉ—e take, shi kalar rigar ta kasance milk color, gabaÉ—aya mazan suna da yalwar tsawon gashi sosai, da alama irin kiristocin nan ne masu tsananin tsauri a kan addininsu, waÉ—an da suke koyi da annabi isa, su ne masu barin gashinsu ya yi tsawo sosai irin na Annabi Isa, haka suka kasance. Suna koyi da shi amma basu yarda su musulunta ba, da ni da ku dai duk mun san annbi Isanmu musulmi ne, su dai ina sun dai yarda shi ne Allansu ba Ubangijinmu ba.

Ga wasu kananan yara da suke ta wasanninsu a wajen, mata suna ta kai kawo cikin wannan shigar tasu mai ɗaukar hankali da matuƙar kyau. One thing about DARK WORLD shi ne, kewayayyen birni ne yana da kofifin shiga da fita, tampatsa tampatsetsan gates ne kamar dai masarautun zamanin da suka suɗe.

Lokacin guda gabakiÉ—aya gungun mazan dake zaunen suka mike tsaye gabaÉ—ayansu. GabaÉ—aya harta mata dake bakin hanya suna kasuwancinsu da harkokinsu, da mata masu wuce duk sai da suka wani ja birki suka tsaya tare da kamewa kam, komai dake arean wajen sai da ya dakata cak, harta kananan yara da suke wasa a wajen sai da suka shiga taitayinsu. Nan take wani tsananin tsoro ya bayyana a saman fuskokinsu, fargaba da tashin hankali ya ziyarci zukatansu, kallo É—aya zaka yi musu kasan suna cikin tsananin tashin hankali. Abin da É—aure mun kai!.

A wani irin mahaukacin gudu wasu danƙara danƙarar motoci bakake kirin suka shararo ta saman wannan tabkeken titi da waɗan nan jama'a suka kame kam ɗin. Sosai motocin suke zabga uban gudu tamkar zasu tashi sama. A yawa ba zaka iya ganin karshensu ba, dan a kalla zasu kai 50 haka, dukkansu kala ɗaya suke except 1, sannan kuma dukkansu motoci ne da suka amsa sunansu motoci

motocine masu numfashi wanda tamkar da gold aka yi su tsabar kyau da ɗaukar idanu, sun haɗu iya haɗuwa, gabakiɗayansu bakake ne kirar *BUGATI* tayun motocin ma kawai abin kallo ne, tamkar ba'a kan ƙasa suke tafiya ba, saboda tsananin kyau, ga wani kuka da suke yi mai fita a hankali hankali tamkar ba kuka suke yi ba.
Chapter 15 · 0% Book details